BAKAR INUWA 47

kwashe ya siyar kona wacece a gidan babu ubanda ya isa yace wani abu kuma. Bata da tarkacen ƙawaye, idan ma kika kasance mai rawar kai a aji bata shiga
harkarki, sannan bata zaman fira in group daga boko har islamiyya, hasalima faɗa takema su Safara’u idan taga sunayi. Tasan dole ne ta shiga ruɗani da sabon
yanayin da Ramadhan ke son jefasu a tsakanin nan. A wani bangaren kuma tanada gaskiyarta akan shiga ruɗani. Tun farko ta sakama ranta Ramadhan yafi
ƙarfinta. Shima kansa ya tabbatar mata yafi ƙarfin nata. Mahaifiyarsa da danginsa harma da mutanen duniya sun tabbatar. A baya babu abinda take gani a cikin
idanunsa sai saɓanin abinda take gani a yanzun, duk da dai harga ALLAH tasan bai taɓa muzantata da baki ba, bai taɓa hantararta ko wulaƙantata ba, kawai dai
baya shiga sabgarta. Dolene canjawarsa a ƙanƙanin lokaci ta zama abu mai rikitarwa a gareta. Amma tayi alƙawarin hakan bazaisa ta taɓa saɓama umarni ko hani
daga garesaba, zatai masa biyayya matsayinsa na miji inhar bai hau turbar sabama ALLAH ba. Zata yi biyayya ga umarnin UBANGIJI akan binyayya ga miji da
dokokin aure kodan tabbatar da martabar tarbiyyarta data gidansu a idanunsa saɓanin wadda aka sanar masa da wadda duniya take kallon ahalinta dana iyayenta
da shi……
Ƙarar landline ɗin ɗakin ta katse mata tunaninta, gabanta ya faɗi. Sai dai tunanin ko Mama Ladi ne ya sata buɗe kanta a bargon ta ɗaga.
“Ustazah! Haka aka koya muki kula da mijinne wai a islamiyyar?”.
Batama san bakinta ya suɓuceba wajen faɗin, “Wlhy Yaya Ramadhan zaka kasheni da raina!”.
Murmushi yay daga can, “Idan na kasheki Ustazah dawa zanyi angwancin?”.
“Na shiga uku”.
Dariyar da batasan ya iyaba ya ƙyalƙyale da ita daga can. Tasa hannu ta rufe fuska tamkar tana gabansa. A zuciyarta ɗunbin mamaki da al’ajab ne danƙare.
(Dama haka yake kokuwa yanzune ya canja…..?)
“Ina jiranki kizo ki bani abinci kar yunwa ta hallakani ga ciwo”. Ya faɗa cikin katse mata tunani yana yanke wayar.
Baki buɗe Ramadhan dake zaune cikin kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya lap-top a cinyarsa alamar aiki yake ya saki yana kallon Raudha data shigo bayan tayi
knocking ya bata izinin shigowa. (Lallai yarinyar nan kanta da motsi) ya ambata a ransa yana ɗauke idonsa gareta. Sanye yake cikin kaya masu taushi baƙaƙe.
Duk da badan kwalliya ya saka ba sun masa ƙyau da sake fiddo hasken fatarsa. Idanunsa dake cike da abubuwa kashi-kashi ya janye yana maidawa ga aikin
gabansa.
Gabansa Raudha ta ƙaraso bayan ta ɗakko basket abincin data shirya masa tun ɗazun, komai a cooler yake dan haka bata tunanin sun huce. Table ɗin ta
kalla inda ƙafarsace fara tas a miƙe, ganinta da abincin kuma baisa ya sauke ba. Kallonsa taɗan sata a ranta tana gulmarsa ganin yanda ya tsuke fuska tamkar
bashi ya gama mata abun kunya ɗazun ba (Humm da gaske mutumin nan dai yanada aljanu). A fili kam sai cewa tai “Ga abincin”.
Banza yay mata kamar baiji ba. Ta sake maimaitawa cikin marairaice fuskarta dake cikin niƙab data sako. Ganin yaƙi nuna yasan da zamanta a wajen sai
takai durƙushe a gabansa tana dire basket ɗin a ƙasa. “Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy tsoro naji ɗazu ɗin”.
Nanma banza yay mata yana cigaba da sarrafa keyboard ɗin lap-top ɗinsa hankali kwance. Sai dai ya fahimci maganar tata nada alaƙa da tunanin gudun datai
ɗazun ne.
“Dan ALLAH!”.
Ta sake faɗa a hankali. Idanunsa da har yanzu jan yaƙi kwaranyewa a cikinsu ya ɗan rumtse, ga mura ga fitina da yaketa ƙoƙarin haɗiyewa taƙi hadiyuwa. Iska
ya ɗan furzar dakai hanunsa saman goshi ya shafa, tunda tace ALLAH kuma ta gama da shi. Amma hakan bai hanashi yin magana a daƙile ba.
“Dan kin rainani ni zakizoma da wannan abun a fuska?!”.
(Oh ALLAH, dama akan niƙaff ne?) ta faɗa a zuciyarta tana lumshe ido. A fili kam hannayenta ta matse waje guda. Cikin sanyin muryarta dake tsumashi batun
yau ba tace, “Dan ALLAH kayi haƙuri ALLAH kunyarka nakeji”.
(Kunya) ya maimaita kalmar a ransa yana ɗan bubbuga yatsansa bisa lips ɗinsa idonsa a kanta. “Okay! Naji ciresa to, inba hakaba kuma ni bashi zan cire
ba, wancan zan cire”.
Kukane kawai ya ragema Raudha ta fashe da shi. Mutumin nan so yake kawai ya zautar da ita a gidan nan, dan sarai ta fahimci abinda yake nufin zai cire.
Babu yanda ta iya dole takai hannu tana kwance niƙaff ɗin sai dai ta rumtse idanunta… Hararta yay ya ɗauke idanunsa dan ya tsani ganin hawayen nan.
Jin bai tanka ba yasata satar kallonsa sai taga hankalinsa baya gareta. Saurin saka nikab ɗin tai ta goge hawayen. Kafin ta ɗaura basket ɗin saman table
ɗin ganin ya sauke ƙafafun nasa. Abincin ta haɗa masa ranta cike da fatan ALLAH yasa ya barta ta koma ɗakinta. Sai dai addu’ar tata bata amsu ba. Dan bayan
ya gama shan ƙamshinsa lap-top ɗin ya ajiye gefe tare da nuna mata gefensa fuska a tsuke.
(Nidai tawa ta ƙare) ta ambata a ranta tana miƙewa tabi umarninsa dan har tafara jin nutsuwa ganin ɗan sake mata da yakeyi kwana biyun nan, sam bazataso
su koma ƴar gidan jiya ba. Duk da 2seater ce sai da taɗan takura sakamakon yanayin nasa zaman. Lap-top ɗinsa ya ɗauka ya maida a cinya yana faɗin “Ohya
bani, dan hukun cinki kenan yau a gidan nan ciyar dani abinci daga nan har dare”. Ya matso da fuskarsa gab da tata. Cikin raɗa ya ƙarasa faɗin, “Inba hakaba
kuma na rantse ni zan c….”
A zabure ta ɗaura hanunta saman bakinsa ta toshe, tsabar rikicewa harda tallafo ƙeyarsa da ɗayan hanunta”.
“Ni dai gaskiya-gaskiya to nama fasa abotar a kwance wlhy”.
Kaɗan ya rage dariya ta kufce masa. amma yay dauriyar dakewa yana bin fuskarta da idanun ke rumtse da bakinta dake maganar da kallo. Ga jikinta sai tsuma
yake. Sosai yake jin nishaɗi idan ya ganta a yanayi na tsorata ko kunyarsa. Hanunsa yasa ya janye nata hanun daga bakinsa harda ɗan bugesa.
“Ustazah yaushe kika koma hakane wai? To ai mai raba wannan abotar sai mutuwa mun ƙulla kenan”.
“To an taɓa dole ne?”.
Ta faɗa cikin waro idanu tana sake ƙwaɓe fuska. Hancinta ya lakata kaɗan da ɗage gira sama ya kashe mata ido ɗaya. “Abota dani dolene yarinya. Dama kika
samu na zaɓeki zakimin iyayi”. Yaƙare maganar da wani salon taɓe baki kamar wani mace. Hakan sai yay bala’in saka Raudha dariyar da batai niyya ba. Sosai
murmushin fuskarsa ya ƙara faɗi shima. Sai dai tana gama dariyar ta ɗago da faɗin, “ALLAH yanda kayi sai kace mace. Baba Laran gidanmu haka take idan tana
faɗa”.
Fuska ya tsuke da kwaɓeta yana hararta. “Waye macen?”.
Dariyar dake yalwace da fuskarta ta sake ƙyalƙyalewa da ita tana kai hannu ta danne bakin. Yayinda shi kuma ya kai hannu ya mangare mata kai ransa
cikeda nishaɗi. Ganin taƙi daina dariyar ya sake bata ranƙwashi….
“Wayyo Mommyna zai ɓararmin da karatu na”.