BAKAR INUWA 47

(Kan uban nan) ya faɗa a ransa dariya na kufce masa shima. cak ta tsaya da tata dariyar ta zuba masa ido batare data sani ba. Dan wani irin ƙyau dariyar
tai masa. haƙoransa duka sun bayyana ba kuma yana yinta a haukace bane…
“Sharri kika koma kuma Ustazah?”. Ya faɗa da sake kai mata ranƙwashi yana dariyar har sannan sai ta duƙe kan nata ya sauka bisa cinyarsa hularta na
zamewa ta faɗi ƙasa. Ƙoƙarin ɗagota ya shigayi amma taƙi yarda. cakulkulo ya fara mata a wuya, cusa kanta take sakeyi tana dariya da ƙoƙarin ture hanunsa.
Jinsa yake a wani irin nishaɗi daya jima baiyiba a rayuwarsa. Zai iya rantsuwa tun bayan rasuwar Haseenahr sa da Amnah bai sake farin ciki makamancin
hakan ba da yake a kwanakin nan musamman yanzu. Yanda gashinta data ɗaure ke reto ya sashi kama ribbon ɗin ya zare gashin ya tarwatse. Da sauri Raudha ta
ɗago dan batama san hulan ya zame kansa ba. Sai kuma kunya ta kamata jin ya tura yatsunsa a ciki. Tai ƙoƙarin matsawa ya riƙeta. Shiru tai tsigar jikinta na
tashi, kamar yanda shima yakejin jininsa na haurawa da gudu a kowanne jijiyar jikinsa….
“Ina son gashin nan sosai”.
Yay maganar yana matso da kansa a kafaɗarta da kamo gashin ya kai hancinsa yana shaƙar ƙamshin haɗaɗɗen turaren YERWA INCENSE AND MORE… da yakeyi. Sai
kuma ya saka maida yatsun nasa cikin gashin ya tallafo kanta ya ɗaura goshinsa akan nata suna musayar shaƙa da fesawa juna numfashi… Murya a matuƙar shaƙe
duk da akwai mura dama tattare da shi ya ce, “Ƙawata!”.
A yanda ya ambaci kalmar ba ƙaramin tada tsigar jikin Raudha yay ba. Da ƙyar ta iya faɗin. “Uhhyim”.
“ALLAH yay miki albarka”.
Sosai taji daɗin wannan addu’a tashi da batasan dalilin yinta ba. Muryarta a raunane tace “Amin nagode”.
Kansa ya ɗan jinjina mata da cigaba da motsa yatsun hanunsa cikin gashin nata. “Ni kuma fa?”.
_“Kaima ALLAH yay maka rahama da rahamarsa. Ya kareka da kariyarsa. Ya baka ikon sauke hakkin ƴan ƙasa dake bisa wuyanka, ya baka nutsuwar ayyuka da har
abada da baza’a manta da kai ba. Ya hanaka cin hakkin kowa koda bai kai girman ƙwayar gero ba”._
(Ya ALLAH yarinyar nan zata hakalani) ya faɗa a ransa yana mai rungumeta tsam a jikinsa. Wannan shine karo na uku da hakan ta faru tsakaninsu. Amma yau
an samu cigaba dan itama tayi luf duk da jikin nata naɗan tsuma kaɗan-kaɗan.
“Insha ALLAH ke ƴar aljanna ce AMEENATU!”.
Murmushi mai sanyi da yalwa ta saki domin jin furicin nasa. Itama cikin rawar murya tace, “Tare da kai da iyayenmu baki ɗaya”.
Ɗagota yay daga jikin nasa yana ɗan murmushi. “Uhhm an samu jiki mai daɗi an lafe. Ƙawa kemafa naga kina buƙatar ɗumin mijinki gsky”.
Hannu tasa ta rufe fuskarta tana murmushi.
“Gulmammiya ni bani abincina. Kinzo kinatamin kwarkwasa yana hucewa”.
“Kai Yaya Ramadhan dan ALLAH”.
“Kam kujimin yarinya da kalan dangi, yaushe na zama Yayanki nikan daga ƙawance kuma? Koda yake kije na yafe miki dai bani abinci cikina ya fara kiran
Taura”…………✍