Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 49

Tab.. Da ke a hanunsa kafin shigowarta. Ganin ya basar da ita ya sata daurewa tace, “Ga abincin”.

   “Zuba”

Ya faɗa a taƙaice batare da yabar abinda yakeyi ba. So yake yay dauriyar fasa abinda yay niyyar yi a gareta amma zuciyarsa taƙi amsar lallashin sam. Bai

kalleta ba harta zuba masa gasashen naman ragon daketa ƙamshi, yaji haɗi na musamman. Sai kunun madara da Bilkisu tayisa a nutse saboda sanin yanda yake

ƙaunarsa. Zata zuba abincin yay saurin dakatar da ita. “No bar nan kawai”.

  Dakatawa tai ta maida kwanon ta rufe da tura table ɗin gabansa yanda zai samu nutsuwar ci. Sai da ya ɓata wasu sakanni ya ajiye tab.. Ɗin, dai-dai da

miƙewar Raudha dake fatan samun hanyar guduwa dan yau bazata juri zama da shi a inuwa ɗaya ba. Caraf ya riƙo hanunta ya zaunar a gefensa.

   “Na sallameki ne?”.

Jitai kamar ta fashe masa da kuka kawai, amma ta daure dan kar yaga kamar ta cika rashin wayo. Hankalinsa ya maida ga abincin zuciyarsa na tunanin ta yanda

zai ɓullo mata ta saki jikinta. Sai dai ya kai laumar nama baki yake faɗin, “Uhhmm Bestie kinji wani gashi na musamman kamar a birnin sin. K karfa ki zata

santi nake naji abunne har cikin kai”.

    Murmushi ne ya suɓucema Raudha. A hankali tace. “Uhhmm!”.

      “Ai bakiji Humm bama sai kinci”. Ya ɗago gareta da tsoka daya ciro jikin dogon tsinken da Bilkisu ta tsiro guda uku. “Buɗe bakin kiji kar ayi babu

ke”.

   A kunyace tace, “ALLAH ni na ƙoshi”.

   Fuska ya ɓata yana ɗan hararta. “Keni bansan gulma buɗe baki. Ni nasan tun kan ki kawo namannan kike addu’ar ALLAH yasa na sammiki”.

     “Ya ALLAHU”. Ta faɗa da dasashshiyar muryarta dariya na suɓuce mata. Shima murmushin yake tare da sake kai mata naman bakinta. Dole ta buɗe saboda

cewarsa. “ALLAH sai na miki ɗura. Kuma saina tauna yayi laushi na juye miki a baki dole ki haɗiye”.

   Fuska ta yamutse alamar ƙyankyami. Ya dungure mata kai da faɗin, “K yarinyarnanfa ƴar wulaƙancice wani lokacin. Wai ƙyanƙyaminama kikeji? Koda yake

hakafa kikaimin kwanaki ina mura. Har shaƙa miki murar nai amma kikaƙi ɗauka saboda ɗan banzan ƙarfin jininki”.

   Yanzu kam kasa daurewa tai ta sanya dariya. “Kai Ya Ramadhan ko tausayi babu?”.

   “K nifa kibar wani cemin Yaya niba Yayanki bane bamsan kalar dangi. Nasan dai akwai abota tsakaninmu sai kumaaaaa……”

    Ya ɗanja ƙarshe yana kashe mata ido batare daya ƙarasa ba. Ba shiri ta miƙe zaram amma yay saurin riƙeta ya maida. “Ustaza bansan fassara irin taku ta

Ustazai fa. Kijira na karasa mana kafin ki kaini inda banje ba”.

  Dole ta dawo ta zauna kamar ta ɓuya a kujerar dan kunya. Ya dungure mata kai yana kai nama bakinsa da taɓe baki. “Gulmammiyar yarinya nafasan kema kin

kamu. A yanzu nan duniya bayan Mommy da Abba babu wanda kike so Kamar Ramadhan…”

   “Ni yaushe nace!”.

Ta faɗa cikin suɓutar baki tana taɓe fuska. 

       “Yo sai kin faɗa? Yanda kika kadandaneni ram ɗazu ke daɗi mijima ai ya isa shaida.”

   “Innalillahi….”

Ta faɗa kamar zata fasa kuka dan kunya. Dariya ke cinsa yanda tai wuri-wuri da idanu na kunya. Ya danne da ƙyar. “Oh kice baki son nawa mana kiga in gobe

banje an ɗauramin aure da ƴammata uku ba galla-galla”.

     Ji Raudha tai kamar ya kwaɗa mata guduma a tsakkiyar zuciya. A take fara’ar fuskarta ta ɓace ɓat. Tai ƙasa da kai zuciyarta na mata zafi da

kalamansa…..

   Wani daɗi ya baibaye Ramadhan kamar ya tashi ta taka rawa. Cikin shafa sumar dake zagaye da kumatunsa yace, “Oh su Ustazah ba kunya anga sumulmulin yaro

ɗan jikan Anne an maƙale. Irin wannan kishi haka Ƙawata? To indai baki so nayo kishiyoyi yau kam dole naje farautar triple koda yake kefa huɗu ma naji kina

faɗa saboda tsabar haɗama keda ma ko ɗan kiss ɗin nan na zamani sau ɗaya aka taɓa mik…….”

    Ai bata bari ya ƙarasa ba ta daka tsalle ta guntse masa baki da hannayenta. Wayyo dariya kamar ta kashe Ramadhan. Yasan ya riga ya gama da ƴar darunsa

yau. Sai dai wani farin ciki ke dawainiya da shi ganin kishinsa ƙuru-ƙuru tattare da ita. Koba komai yaji daɗi bashi kaɗai ke wahalar banzaba akanta ashe.

Jikinsa ya jawota ya rungume. Cikin raɗa yace, “Na nayi shiru tashi kici abinci”.

    “Kaci kayanka, ko kaje kuci da ƴammatan naka”.

   “Wayyo Ramadhana anyi kasuwa. Uhm-uhm fa Bestie ALLAH karki tsaya kallon ruwa ƙwaɗo ya miki ƙafa. BABU SO MIYA KAWO KISHI?”.

   Turesa ta shigayi da faɗin, “Wama zaice yana sonka ɗin. Abotarma an fasa”.

      Nanma dariya kawai yakeyi yana sake riƙota dan ya fahimci so take tai amfani da damar ta tsere. Ya jima da gane tanada wayo duk da ƙarancin

shekarunta. Matseta yay da ƙyau duk yanda taso ya hanata damar dole ta nutsu saboda abinda ya raɗa mata a kunne kamar ta nutse. tanaji tana gani ya tilasta

mata cin nama da kunun wanda yay mata matuƙar daɗi. Dama da ƴar sauran yunwarta ta rana. Bayan sun kammala ta tattara kwanika zata fita da su ya hanata.

Acewarsa ta tayashi salla ya bata labarin faransa tunda ita bata tambaya ba. Ganin ya zama serious doleta haƙura. Sai dai ta masa complain na rashin hijjab

yace abu mai sauƙi yana da shi ai….

     Raudha dai dauriya kawai take amma tabbas a tsorace take. Bayan sun idar da salla ya dafa kanta yay addu’a kamar yanda musulinci ya tanada ya kuma dace

ace tun randa aka kawota gidan hakan ta faru. sai dai lokacin gogan nata na bisa gajimaren hayaƙi hakan bata faru ba. Sosai Raudha tai mamakin yanda taji

yana kwararo addu’oi. Sam batai zaton yanada ilimin addini kamar haka ba. Sai taji ya sake birgeta zuciyarta ta ƙara nauyi game da shi.

   Bayan sun idar ma ta buƙaci son zillewa ta gudu ya sake hanata. Ƙarshe ma kayan barci da batasan daga ina ya samosu ba ya bata wai ta saka. A matuƙar

kunyace ta dubesa cikin marairaicewa amma ya nuna mata babu wani ɗaga ƙafa yau anan zata kwana. Shi ya gaji da raba musu makwanci da takeyi. Daga karshe ya

haɗata da kunyar data sakata bin umarninsa dole.

    “Ustazah a haka za’a samo ƴan huɗun kina gabas ina yamma. Gara dai kiba marasa ɗa kunya ki haifama Maah jikan da taketa fatan gani. Gashi ma kin ƙudiri

surprising ɗinta har ƴan huɗu kika shirya.”

    “Kai Ya Ramadhan magana wai bata wucewa a gunka”.

  “Oh ikon ALLAH na kulafa kin fara bin hanyar rainani yarinyarnan. Ni miye nawa tunda faɗa kikai naji. Ai har Anne zanma albishir gobe”.

    “Na shiga tara dan ALLAH ka taimakeni”.

   “Hhhh taimako ɗayane zaki samu sai kin saka kayan nan”.

   Wannan kandagarki nasa ya sata shiga toilet ta canja. Sai dai ta jima tana duban kanta a mirror ɗin toilet ɗin ta kasa fitowa. Sai kallon kanta take cike

da kunya da ganin ƙyawun da tayi kamar ba itaba. Sai dai gaskiya bazata iya fita da rigarba gabans….

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button