Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 50

handbag. Tana duba takalmi a akwatin lefenta ya sake shigowa. Bai yi magana ba yabi duk kayan wutar ɗakin ya kashe komai. Dai-dai tana gamawa yake faɗin,

“Ko breakfast bazamu tsaya yiba mayi acan kawai”.
     Kanta ta jinjina masa, sai dai har yanzu taƙi yarda su haɗa ido. A hankali ya matsa gefenta yay musu hoto bayan ya faɗi abinda ya sakata ɗagowa ta

kallesa a ɗan tsorace. Sai hoton ya bada wani style mai ƙayatarwa kamar anyisane da shiri.

        Bayan sun sallami su Mama Ladi suka fito compound inda jerarrun motocin da zasu fitan suke. Yau ce karo na farko da zasu fita tare da shi a bayyane.

Sai gaisuwa ake miƙa musu cike da ɗunbin girmamawa wadda har Raudha takejin babu daɗi akanta. Dan kuwa da yawansu sun haifeta da girmarta. A motar da tafi

kowace mota ƙyau da ɗaukar idanu ga tutocin ƙasar naya a jikinta suka shiga. Kafin wanda zasu musu rakkiya Taura house ciki harda cos da wasu ministers uku

suma suka shiga. Ba wani tafiya mai tazara bace ba, amma ta fahimci an bama fitar muhimmanci matuƙar dan har a redion motar da driver ya kunna saiga

sanarwar yau shugaban ƙasa Ramadhan B. Hameed Taura zaije hutun ƙarshen shekara gidansu a karo na farko tun bayan hawansa mulki na watanni kenan. Anan aka

saka zantukan mutane daban-daban daketa masa addu’a shi da iyalinsa akan yasha hutu lafiya cikin farin ciki.
     Sosai ya ƙara samun nutsuwa a ransa dan kuwa zuwa yanzun ayyukan daban-daban da suka faro na talakawa sun kankama matuƙa. Abinda zai matuƙar birgeka

duk wani mai kwangilar gwamnati sunansa da aikin da zaiyi a bayyane yake ga al’umma. Hakan yasa yake ƙara samun addu’a ga talakawa dan kuwa babu wani

ƙunshe-ƙunshe balle a cucesu a ƙiyi musu aiki kuma su rasa daga ina matsalar take. Kai hatta kuɗin da aka bama masu kwangilan da wanda sukebin bashi sai sun

kammala a cika musu duk an sanar da duniya babu wani rifa-rufa. Hakan da yay ya matuƙar taimakawa da saka tsoro a zukatan masu kwangilar dan sun san kam

inma basuyiba sune a ruwa tsundum. Gashi har adadin watanni ko shekarun da aikin zai ɗauka kowa ya sani a bayyane. Bashi kaɗaiba hatta da gwamnoni da ƴan

majilusu, ciyamomi, kansiloli duk aikin da zakai ma ƴan yankinka a jihohin nan 41 dolene ka sanar da komai talakawa su sani.

        Tarba ce ta musamman tawagar shugaban ƙasa ta samu a Taura house, dan kuwa wannan shine karo na farko da yazo gidansu a bayyane kuma da shirin

kwanaki. Sosai bakin Anne da su Yafendo ke a buɗe, ganinsa ya musu wahala yanda suke buƙata tunda ya hau mulkin nan. Raudha dai gaba ɗaya a takure take.

Jitake kamar kowa zai iya gabe abinda ya faru a tsakaninsu jiya. Ga anne da su Yafendo sai nan-nan suke da ita kowa na saka mata albarka. Bayan gaishe-

gaishe da addu’oi Ramadhan da su Bappi suka fita salla dan tawagar datai masa rakkiya sun koma. Sai dai Taura house tako ina zagaye yake da securitys kai

gaba dayama anguwar. Dole ne ka shaida shugaban ƙasa na nan koda matakan tsaron dake kewayen anguwar baki ɗaya, kai kace ko ƙuda bazasu bari ya gitta ba.
           Da ƙyar Raudha ta iya tsarki da ruwan sanyi tsabar zogin da wajen ke mata zuwa yanzun. Har jin kanta take kamar wadda zazzaɓi zai saukarmawa.

Anne na lure da yanayin nata sai dai batace komai ba dan zuciyarta bai kai ga zargin abinda ke faruwa da Raudha ɗin ba kai tsaye. Gashi tunda suka shigo

dama yanayin idanunta na wadda taci kuka ya tsayama Anne a rai. A ɗakin Anne sukai salla duk da kuwa an gyara sashen Ramadhan ɗin tsaf domin su.
      Bayan idar da salla gaba ɗaya gidan ƴaƴa da iyaye aka haɗu domin yin lunch a katafaren falon Bappi. Abincine mai rai da lafiya da gamsarwa a wajen

iri-iri. Anyi hakanne kawai domin walimar zuwan Ramadhan ɗin da Raudha. Sai yanzu Raudha taga gimbiya Su’adah da sauran matan gidan, dan kuwa bata shiga

gaishesu ba Anne tace sai zuwa yamma sun huta. Sai dai shi Ramadhan ya shiga ya gaida Gimbiya Su’adah ɗin kawai ganin bata a masu fitowa tarbarsa.

Kasancewar salla zai fita yasa bayan gaisuwa babu wani abu daya shiga tsakaninsu ya fito suka fice massallaci.
     Har ƙasa Raudha takai tana gaishe da iyayen. Kowa ya amsa mata cike da kulawa banda gimbiya Su’adah da ko kallon inda take bataiba. Ƙasan ranta wani

takaicine da baƙin ciki da kishin yanda Raudha ta kara murjewa komai na halittar jikinta ya ƙara girma sai kace ƴar 25years. Ga tsadadden material ɗin dake

jikinta wanda ta tabbatar za’a iya sayen abincin watanni na gidansu Raudhan da kuɗinsa. Ita saima taga kamar yarinyar tana wani jin kanta.
     Oho Raudha batasan tanai ba. Ita abinda ya dametama ya isheta. Komai yinsa take cike da dauriya. Abincinma tana matuƙar bukatarsa amma ta kasa ci

saboda bakinta babu daɗi. Sai juya spoon take a ciki tana ɓata fuska. Ramadhan na lure da ita. Kuma hankalinsa na kanta. Burinsa su haɗa ido amma taƙi

kallon ko inda yake. yana zaune ne tsakkiyar Bappi da Pa. Sai Anne a gefensu da Yafendo da Inna. Ita kuma tana kusa da Bilkisu da Zainab ne. Su Lubnah sai

faman jan tsaki suke ƙasa-ƙasa suma kamar su halaka Raudha sukeji musamman ganin suturar data sanya kosu da suka tashi gidan kuɗin basu saka ba. Tsadajjen

agogon hanunta da zabba da bangles kawai duniyane. Balle ita kanta data kara wani kyau na musamman da su sam basa lura da shi sai yau duk da kuwa suna tare

da ita.
          Da gangan Ramadhan yay kamar ya sarƙe yaja gyaran muryar data saka kowa maida hankalinsa a kansa ana rige-rigen jera masa sannu. Bappi dake shafa

masa baya kamar wani ƙaramin yaro ya kai masa kofin ruwa bakinsa yana masa sannu. Kaɗan yasha yana jinjina musu kai da satar kallon Ustazahr tasa. Sai dai

bata yarda ta kallesa ba tun bayan ɗagowar datai kamar yanda kowa ya ɗago lokacin daya sarƙe. Ita sanun tatama a kan laɓɓa tai masa ta tsuke bakinta. Ganin

dai ba samun yanda yakeso zaiyi ba sai ya haƙura. Takaici ya cika Aynah da duk hankalinta ke akansu. Hakama Muneera da idonsu akan yayan nasu da abinda yake

yawan kallo. Jin hawaye na neman zuboma Aina’u itace ta fara mikewa wai ta ƙoahi. Babu wanda yace mata komai, hakan sai ya ƙara baƙanta ranta. Dan a ganin

bai kamata aƙi bata kulawaba kodan mata ta biyu da take shirin shigowa ga ɗansu kuma ɗan uwanta.
        Raudha da dama ba abincin take ci na kirki ba itace ta ukun tashi a wajen. Ramadhan ya ɗan bi yanda take tafiya da kallo. Hannu ya kai ya dafe

goshinsa a zuciyarsa yana ayyana (Yarinyar nan zata tonamin asiri fa). Bayan sun kammala kowa ya tashi a wajen yaso janta sashensa dan ya fahimci mugunta

taima kanta bata shiga ruwan zafin daya haɗa mataba da asuba, bayajin kuma da safe ta sake kula da kanta. Takaicin kansa yaji dabai tsaya akanta ya taimaka

mataba duk boranta. Sai dai duk yanda yaso ya keɓe da ita ɗin hakan bata yuwuba dan su Basma na zagaye da ita a falon Anne suna hirar school duk da ba wani

saka musu baki take sosai ba. Sai dai ganin Inna da Yafendo da Anne na wajen ya sashi haƙura ya shige shi acewarsa zai ɗan huta………..✍
        

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button