Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 54

Rufaidah, Ai’sha da Ummita. Dukansu sunyi karatu wasunsu ma na aiki, Ummita ce kawai take kan karatun saboda manemin nata ya takurane yasa za’a haɗa da ita

amma sa’ar Muneera ce ma. Koda yake ita kanta Muneera ɗin ta isa auren ai kawai dai dan akwai yayuntane.

       Babu wata walwala Ramadhan ya koma wajen Raudha, dan yasan ma’anar shirun mahaifiyarsa. Tuni ita har tayima shirin barci. Tana zaune ne a kan gadon

tana assignment ɗin makaranta da aka basu na cikin hutu, sai dai sanye take da hijjab a saman kayan barcin nata. A kallo guda ta fahimci ransa a ɓace yake,

cikin dauriya ta masa sannu. Bai amsa ba sai dai ya kwanta a gadon tare da ɗoro kansa saman cinyarta bayan ya ture takardun gabanta gefe.
        “K dole kin zama ƴar boko ko?”.
Ɗan murmushi tayi kawai dan yanda yay maganar kamar mai son huce haushinsa akan bokon nata ne. Cikin san kauda masa damuwarta tace, “Harka tunamin Abbanmu.

Idan mukai masa laifi koya tashi baida ko sisi sai ya hana kowa zuwa makarantar boko ranar. Ya ringa faɗin, “Anma fasa bokon, daga yau bazaku sake zuwa ba,

bandama shegantaka irin ta bature yabi duk ya katantane duniya ya hana kowa zaman lafiya, komai bazaka samesa yanda kake muradi ba sai kayi wani abu shege

a.b.c.d kai nifa shiyyasa ma ana kaini ina tserowa a makaranta da ƙyar na haɗa sakandire ɗin ma”.
      A bazata dariya ta ƙwace masa. Har haƙoransa na bayyana baki ɗaya sai dai ya kai hannu yana karewa. “ALLAH na lura Abba ɗan darune?”. Ganin yanda ya

karɓi zancen ya saka Raudha dake nata ƴar dariyar itama faɗin, “Tab damma baka sanshi bane. Wlhy duk randa darun Abba ya tashi gidan nan ranar kowa sai yaji

a jikinsa. Ko ruwa ka cika kofi zakasha sai yace ka ƙara masa talauci kana baƙin cikin ya zama mai kuɗi”.
     Yanzu kam sosai yake dariya. Raudha da farin ciki ya cikata itama ta tura yatsunta duka a cikin gashinsa tana masa susa. Nan ta shiga bashi labarin M.

Dauda sai dai na hankali wanda tasan mutuncinsa bazai zube a garesa ba. Cikin amincin ALLAH sai gashi ƙaunar mahaifinta ta sauka masa a rai har yanajin

sassaucin takaicin halayyarsa tada da bincike yazo da ita.
       “Ya kamata ma muje mu gaishe da Abba Hutawa gaskiya”.
Cak Raudha ta dakata da susan da take masa a cikin gashi ta tsurama ƙyaƙyƙyawar fuskarsa ido idanunsa a lumshe suke yayin da hannayensa duka ke harɗe a

ƙirjinsa yana kwance rigingine. Yanda ya nutsu zai baka tabbacin susar da take masa cikin gashi na masa daɗi. Ya buɗe lumsassun idanunsa da suka canja launi

a hankali ya zuba mata su. Gira yaɗan ɗaga mata yana sassanyan murmushi. “Yadai naji kinyi shiru Ustazah?”.
     Hawayen da suka ɗan cika mata ido ta haɗiye, cikin ƙaƙaro murmushin itama tace, “Nagode da karamcinka”.
        “Cmon johre. An gaya miki Abban nakine ke kaɗai banson iyayi”.
   Yay maganar yana dungure mata hanci da ƙoƙarin miƙewa zaune. Toilet ya shiga, ita kuma ta sauke ajiyar zuciya da hawaye lokaci guda. Wani abu mai

muhimmanci na sukar ranta. Koda ya fito wanka cayay ta kawo masa sauran namansa. Dan bacin ran daya shigo da shi ta riga ta gusar da shi. Kawo masa tai

harda kunun, yako ci abinsa yay ƙat sannan ya koma bayin yayo brush, koda ya dawo assignment ɗin ta nuna masa inda bata gane ba.
       “Ustazah! Kibar batun Assignment ɗin nan nima inada nawa Assignment ɗin mai kawo lada ma.”
           “Please Ya Ramadhan dafa an koma hutu idan ALLAH ya kaimu zamuyi submitting”.
     Gadon ya hawo yana ɗaure igiyar rigar barcinsa. Ya zare mata hijjab ɗin jikinta sannan ya ɗauka takardar data rubuta questions ɗin da amsar data rubuta

daban na wanda ta gane. “Yarinyar nan kanki fa naja”.
Ya faɗa cikin ɗage mata gira. Murmushi kawai tayi da maida kanta ƙasa. Shima hankalinsa ya sake maidawa ga takardun yana faɗin, “Ai gyaran ma kaɗanne”.

Bayani ya shiga mata dalla-dalla harma akan abinda bata tambayesa ba, dan shima yayi course ɗin sanda yana jami’a. Sosai taji daɗin bayaninsa har tana sake

zaƙulo masa wasu tambayoyin. Sai dai taƙi sakewa da jikinta sai faman karewa take da hannu kamar mai jin sanyi. Tsaf yana lure da ita amma yay kamar bai

gani ba. Zata sake jeho masa wata tambayar ya turo kayan karatun nata ƙasa da jawota jikinsa yana faɗin, “K ni na gaji da aikin bautar bature zo kiji wata

magana”.
    Gabantane ya shiga faɗuwa. Sai dai ko saurarenta baiyiba yaja musu bargo ya matseta a jikinsa yana shinshinar wuyanta da kai mata kiss’s……….✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button