BAKAR INUWA 55

harara daya sakar mata duk da a kasan ransa yaba ƙyawun da rigar jikinta tai mata yake. Rigace mai santsi sai dai sam babu nauyi tattare da ita kalar blue,
sai dai an mata kwalliya da baƙi kaɗan-kaɗan, sai ta saka hula blue a kanta kamshin khumra mai sanyin daɗi na tashi a jikinta sama-sama. Cikin sauke ajiyar
zuciya yabi bayanta ɗakinsa data nufa.
Kusan a tare suka shigo, ta ajiye kayan inda ya dace da nufar fridge dan bashi ruwa. Yayinda shi kuma ya hau zame kayan jikinsa da suka damesa
sosai. Kanta a ƙasa ta tsiyaya ruwan ta mika masa lokacin da yake zaune bakin gado yana kunce takalnan kafarsa. Bai dago ba har saida ya gama cirewa,
kafarsa dake cikin baƙar safa ta bayyana. Ruwan ya amsa nanma yana ɗan hararta, ita dai sai tayi guntun murmushi da ƙoƙarin danne zafin da takeji a ranta.
“Kayi hakuri dan ALLAH”.
Ta faɗa cikin sanyin murya lokacin da yake miko mata kofin ruwan daya shanye gaba ɗaya. Mikewa yay kamar bazai tanka ba. Sai da ya nufi hanyar toilet ya
bata amsa kausashe…
“Da kikaimin mi?”.
Ita dai babu bakin cewa komai, da zai tausaya matama daya barta da abinda takeji a ranta. Mikewa tai ta fice kafinma ya fito. Ta koma falo ta karasa haɗa
shayinta tai zaman sha a dining dan tasan dole zai fito nan abinci koya buƙaci takai masa can……..
Shayin take sha, amma tunaninta sam baya tare da duniyar mutane. Tayi matukar yin zurfi a tunani har Ramadhan daya fito ya karaso dining ɗin bata sani
ba. Yayi kyau cikin kananun kaya farare tas daga wandon har rigar. Sai baƙin Slippers daya kara fiddo hasken kafarsa. Idanu kawai ya zuba mata ransa fal
mamakin mi take tunani haka da zurfi, dan shi a ganinsa yanda take da karancin shekaru kamar bata da wata damuwa da zata iya damunta a rayuwa. Hanunta da
take zagayawa kan kofin ya rike cikin nasa ya matse da kofin. Zafi ya ratsata ta dawo hayyacinta firgigit. Sai kuma ta bata fuska da shagwabeta kamar zatai
kuka. “Ya Ramadhan da zafi fa!”.
Bakinsa ya ɗan taɓe da faɗin, “Ai dan kiji zafin nayi. mi kike tunani haka?”.
Nannauyan numfashi taja a hankali, ji take kamar ta rushe masa da kuka. Amma sai zuciyarta ke tausarta akan ta daure har sai taji daga bakinsa
tukunna. Cikin ƙoƙarin danne ainahin damuwarta tai ƙasa da kanta idanunta na tara kwalla. “Dan ALLAH kayi haƙuri ka yafemin, ALLAH inajin tsiro ne kawai
shiyyasa. kuma akwai zafi wajen jinake kamar zan iya mutuwa”.
Idanu ya ɗan tsura mata na wasu mintuna. Sai kuma ya lumshesu ya sake buɗewa a kanta yana furzar da numfashi.
Jin yaki cewa komai ta ɗago ta ɗan dubesa fuska share-share da hawaye. Kauda kansa yay da rumtse idanu yana cizar lips. Sai kuma yaɗan murza goshinsa
kafin ya zaro tissue dake a dining din ya miƙa mata.
“Bani abinci barci nakeji”.
“Baka haƙura ba dan ALLAH”.
Fuska ya sake tamkewa. “Nifa bana son nacin magana abinci nace ki bani ko”.
Da ƙyar ta haɗiye kukanta ta mike tai masa yanda ya buƙata. Sai dai abincin ma kaɗan yace ta zuba masa shima ta bashi shayi. Duk yanda ya buƙata haka
tai masa. Kafin ta koma wajen zamanta ta cigaba da shan shayinta da duk ya huce da cokali. A haka Bilkisu da yasa ta dawo gidan da zama baki ɗaya har sai
lokacin bikinsu ta fito ta samesu. Sannu da zuwa tai masa, sannan takai zaune itama dan dama bataci abincinba yau karatun alkur’ani tayi.
“Su Muneera fa?”.
Ya tambayi Bilkisun batare daya daina cin abincinsa ba.
“Yaya ai muna isowa kayansu suka kwasa driver ya juya dasu kamar yanda Pa ya basu umarni”.
Kansa kawai ya jinjina. Raudha dakema Bilkisu kallon rashin fahimta dan batasan da barin su Aynah gidanba ta nuna mata Ramadhan da ido tana ɗaga mata
gira. Kanta kawai ta maida kasa dan ta gane Bilkiaun na nufin ta tambayesa.
Haka suka kammala cin abincin kamar wasu kurame. Ramadhan ya koma falo ya ɗan zauna yana kallon labarai. Raudha kuma ta shiga tambayar Bilkiau
miyyasa Su Muneera zasu koma gida?.
Ɗan harar wasa Bilkisun ta mata. “Aunty Raudha bansan jajibe-jajibe. Kedai kawai ki godema ALLAH an rabasu da gidan kawai suje can su karata da baƙin
halinsu”.
Raudha zata sake magana ta dakatar da ita tana miƙa mata waya. “Kinga ni share waɗan can shashashun bani shawara. “Surukinkine ya turosa wai dole saina
zaɓa kalar bags ɗin da nakeso”.
Cikin murmushi Raudha ta fara bin set na akwatinan da kallo. Sun haɗu iya haɗuwa. Da gani kuma daga kasar ketare aka turosu. “Humm ni wannan ai sai nai
ruwan ido. Duk fa sun haɗu aunty Bilkisu”.
Yar dariya bilkisun tayi itama. “ALLAH nima tun ɗazun na kasa ajiye hankalina waje guda na zaɓa. Shiyyasa nace ya jira sai kin dawo kin zaɓa sai na
bashi amsa.”
Har cikin rai Raudha najin daɗin yanda Bilkiau ta ɗauketa. Sai ta tuno da Queen Billy sabuwar ƙawar datai yau a school, a massallaci suka haɗu wajen
alwala ta yarda wallet ɗinta batare data sani ba. Shine Raudha ta ɗauka ta bita massallaci da shi. Sai da suka idar da salla ta bata. Cikin jin daɗi ta
rungumeta. Sai kuma ta saketa tana bata hannu. “Yi haƙuri dadine wlhy ya rufeni, dan duk abuna mai muhimmanci na cikin wallet ɗin nan sunana Bilkiau amma
amfi sanina da queen billy kefa?”.
Daga cikin niƙab Raudha tai murmuahi, dan ta fahimci queen Billy zatai ɗan karen surutu. Itama hanunta ta mika mata. “Nice name dear ni sunana
Amenatu Dauda”.
“Sunanki mai daɗi zamu iya zama kawaye? Danni bakuwace yau kwanana biyar kenan da shigowa school ɗin nan har yanzu na kasa sabawa da kowa.”
Nanma murmushi kawai Raudha tayi, dan haka kawai queen Billy ɗin ta birgeta. Itama dai yarinyace kamarta dan bazasu wuce sa’anin juna ba. Gata
ƙyaƙyƙyawa. Taso Raudha ta buɗe nata fuskarta amma taƙi, acewarta wataran zata ganine. Sun faɗama juna department sannan sukai sallama……….✍