Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 56

Ko kulata baiyiba ya maida ƙofar ɗakinsa ya datse da key duk da yasan babu mai zuwa sashen. Cakulkulo ya fara mata daga kuka ta koma dariya da bashi haƙuri,

bai ƙyaleta ba sai da suka dire cikin gadonsa. Salon daya fara bi da itane ya sata shagala da farko, sai da labari yay nisa a nanfa ido ya raina fata. Ta

shiga magiya da roƙo akan abinda shi kuma anzo gaɓar da bazai iya ɗaga kafarba. Aiko taji ajikinta, dan har dana sanin shiga huruminsa tayi. Kuka kam ba’a

magana.
           Sun fito wanka yake dubanta da murmushi yanda ta lafke a gado tana sakin numfashi da ƙyar kamar wadda ke a cikin ciwo. “K kuwa yarinyanan an miki

wankan jego kina jinjira? Shikenan da’an ɗan taɓaki sai ki sharɓema mutane a haka za’a haifa ƴan huɗun?”.
       Shiru tai masa kamar tai kuka. Haka kawai yaji dariya ta taho masa. Bai iya dannetaba ya ƙyalƙyale kuwa. Haushine ya kama Raudha, a ganinta tsantsar

muguntace ya gama wajiga rayuwarta ya dawo mata dariya. Sai kawai ta sakar masa kukan karya.
     “Okay kukama kike? To bari kawai na sakaki mai dalili mana da kiyi na banza gara kiyi na lada…..”
     Kafin ya rufe baki har takai ƙofa. Baki ya buɗe zaiyi magana gabansa yay wata irin masifaffiyar faɗuwa tare da kansa daya sara masa. Da sauri ya dafe

kan yana ambaton sunan ALLAH. Raudha data zata wayau yake son mata tai tsaye kawai tana kallonsa da murmushi. “Ya Ramadhan na riga nasan wayonka ai. Shine

harda pretending?”.
      Jin shiru bai amsa mataba ga kujera ya dafe har lokacin hanunsa dafe a kansa kamar maijin hajijiya yasata daina dariyar ta tsura masa idanu. Da sauri

ta ƙarasa garesa ganin ya tafi kamar zai faɗi. Tarosa tai, sai dai yanayin jiki ba ɗayaba yafi karfinta musamman da jikin nasa ya saki sai suka zube ƙasa ya

faɗa kanta. Ƴar ƙara ta saki da ambaton sunan ALLAH saboda wani raɗaɗi daya ratsa mata hanunta da suka faɗi a kansa. Tai ƙoƙarin dannewa amma ta kasa dan

azaba. Kuka ta saki tana son turesa sai dai ina. A take jikinta ya fara rawa, ta turashi iya karfinta yay ƙasa da ƙyar, sai dai kafin ya dire a bazata taji

ya ɗauke fuskarta da mari.
      “K! Baki da hankaline ni zaki ture?”.
    Ya faɗa a matuƙar kausashe da muryar da ko sanda basa shiri bata taɓa ji daga garesa ba. Lallai ta maru, dan yay bala’in shigarta, zata iya rantsewa

kuma shine na farko a duniya daya taɓa marinta, tsabar azaba har kifewa tai akan table sai ga goshinta ya fashe. Idanu ya waro a ɗan tsorace yay kanta yana

ambaton “Ya salam Ameenat….”
       Sai dai yana kai hannunsa jikinta ya sake tureta da ƙarfi ya sake dafe kansa dake juya masa. Duk yanda yaso yin addu’a bakinsa yay masa nauyi ya kasa

furtawa. Duk da azabar dake ratsa Raudha a goshi da hannu haka ta sake nufarsa tana kiran sunansa a tsorace. Sai dai tana matsawa garesa ya sake hankaɗeta a

matuƙar tsawace yace, “Fitarmin anan!!”.
       “Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un Ya Ramadh…..”
      “Nace ki fitar min anan!!”.
Ya faɗa a wani irin yanayi na fita hayyaci da tsananin ɓacin rai. Sosai jikin Raudha ke rawa kuwa yanzu. Ta fita a ɗakin da sauri kuka na kufce mata. Ga

jini harya wanke mata fuska duk da taresa da tai da hanunta mai lafiya. Hanunta daya bugu kuwa wata azaba yake mata harya fara yawa da kumburi. Bata samu

kowa a falon ba, sai dai karar buɗe ɗakinta da bugo ƙofar ta rufe ya fargar da Bilkisu dake gaban mirror tana kallon film a lap-top. Da sauri ta fito sai

idonta yaci karo da ɗigon jini, a razane tabi jinin da kallo har ƙofar ɗakin Raudha, ai bama tasan kalar tsallen datai kawai ta ganta jikin ƙofar

ba………….✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button