Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 59

iso inda take, wata irin muguwar damƙa yayma gashinta dake daure a tsakkiyar kai da hanunsa….
       “K!! Har kin isa saboda aurenki a hanani yin yanda nakeso akan auren wadda zanyi? Wacece ke? Mikika taka?!.. Wato kinje kin kai munafunci garesu

dansu hanani, to ai in gaya miki babu ubanda ya isa. Yau zan tabbatar miki ke ɗin ƙaramar mara kunyace kuwa wlhy…”
      Kuka sosai Raudha keji jikinta na tsananin rawa. Ta shiga yarfa hannayenta duka biyu kuka mai ƙarfi na ƙwace mata ganin yana kunce belt ɗin wandon

jeans ɗin jikinsa. Abu biyu ta kawo a ranta. Duka ko abinda yay mata ranar, dan haka tai yun ƙurin ceto rayuwarta sai dai hakan ya gagara. Dan tuni ya

damƙota ya jefa saman gadon har sai da bayanta ya amsa dan azaba…….

★★★

     Ihun Raudha ya matukar tada hankalin Bilkisu da ke ɗaki har barci ya fara daukarta. Ta fito a waje zuwa ɗakin sai dai ta samesa a kulle. Bugawa ta

shigayi tana kiran sunan Raudha. Sai dai wata shegiyan ashariya da batasan Yayan nasu ya iyaba sai yau ya mulmulo mata daga ciki. Ai babu shiri tabar wajen

a guje. Sai dai koda ta koma ɗaki wayar Anne ta kira. Tana dagawa ta fashe mata da kuka da fara zayyana mata abinda ta sani.

     Sosai hankalin Anne da Bappi ya tashi, dan sun san ba kamar yanda Bilkisun ke tunanin Ramadhan dukan Raudha yake ba. Su sun san illolin daya dingama

Amnah idan irin wannan ɓacin ran mai tsanani ya riskesa. sai dai suna ƙoƙarin rufe hakan ga kanensa idan ka cire Mardiyya da Safina dakan san wasu a wani

lokutan.
       Hankali a tashe tsoffi nan suka baro gida a daren nan tare da Dr Hauwa da suka taso itama ta waya suka nufo government house. Dan Dr Hauwa ce ma da

kanta taja motar.

     Lokacin da suka iso Ramadhan ya riga ya gama illata Raudha har jini ya ɓalle mata. Tunda ya fito a hargitse Bilkisu na son shiga tanajin tsoro. A

durkushe suka sameta bakin ƙofar tana kuka. Tana ganinsu ta faɗa jikin Anne ta rungumeta.
      “Anne ya kasheta, wlhy ya kasheta Anne!!”.
     A tsawace Bappi yace, “Yana ina!?”.
Cikin kuka Bilkisu ta sanar masa ya koma dakinsa. Hakan ya bama Anne da Dr Hauwa damar shiga. Bappi kuma ya tisa keyar Bilkisu ta nuna masa bedroom ɗin

Ramadhan.

       Hankalin Dr Hauwa da Anne ya tashi a yanayin da suka sami Raudha, dan haka babu wani kace nace Dr Hauwa ta fara ƙoƙarin ganin ta tsaida jinin. Tsahon

lokaci ta ɗauka da taimakon Anne dake fama da tsufanta suka samu nasarar hakan.
      “Anne bazai yuwu mu barta anan ba. Inaga muje da ita can wajenki dan tana buƙatar kulawa mai tsanani yarinyar nan a wannan gaɓar tunda Alhmdllhi cikin

dake jikin nata mun samu ya tsaya. Da dai anyi dilay kam da labarin da ake ba wannan bane”.
     Wasu hawayene masu sanyi suka sakko akan fuskar Anne. Farin ciki da cikin Raudha, da damuwar halin da jikanta yake sakamakon son zuciyar mahaifiyarsa.

     A can kuwa ɗakin Ramadhan shigar Bappi tayi dai-dai da fitowarsa wanka, ya sauke towel ɗin da yake goge fusakarsa zuwa suma kawai yaji saukar mari

haggu da dama. Gaba ɗaya wutar kansa ta ɗauke ganin wanda ya maresan. Bappi, abinda bai taɓa faruwa ba ko a tarihin ƙuruciya. Dan ko laifi yayi yana yaro

sai dai Anne ko Pa su dakesa amma ba Bappi ba. A karshe ma Bappin ke komawa lallashinsa da masa nasiha. Amma sai gashi yau da girmansa. Shekara dai-ɗai har

36 a duniya kakan nasa ya rufe ido ya yarfata masa maruka har biyu bayan wanda Pa ya masa ɗazun….
        “Ramadhan ka kiyayi haduwata da kai wlhy!!”. Bappi ya faɗa cikin gargaɗi da ke nuna tabbatarwa. Kafin yay wani yunkuri kuma ya juya yay

ficewarsa………✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button