BAKAR INUWA 60
Episode. 60_*
………TAURA HOUSE
Tunda suka baro government house a sirrance da Raudha kai tsaye Taura house suka nufo. sai dai anan ɗin ma dai babu wanda yasan da dawowar tasu
kamar yanda kowa bai san da fitarsu ba. Sake dukufa Dr Hauwa tai akan Raudha har sai da ta tabbatar komai ya daidaita. Abin tausayi har ɗinki akai mata
saboda bidirin da Ramadhan yay a jikinta. Hakan ya sake kona zuciyar Bappi da Anne sai dai babu wanda ya iya cewa komai har Dr Hauwa ta kammala aikinta ta
wuce.
Barci Raudha take saboda allurar barcin da Dr Hauwa tai mata. Dan haka Bilkisu ta zauna ta zayyanema Anne komai data sani har wanda Raudha ma bata san
ta sani ɗin ba. Anne harda hawaye tausayin Raudha mai tsanani na cin zuciyarta. Koba komai sune suka jefata a wannan masifar. Maybe dasun barta ta aura
dai-dai da ita da duk hakan bai faruba. Sai dai kuma ƙaddara ta riga fata inji masu iya magana. Sannan kuma babu mai sawa ko hanawa daga abinda yazo a
littafin ƙaddarar wani bawa koda yana kalon kansa matsayin SILA.
WASHE GARI
Raudha ta jima bata farka ba har kusan tara, koda ta farka ɗin kuma Anne fidda kunya tai ta taimaka mata sosai kodan ɗinkin da akai mata. Ga Dr
Hauwa ta tabbatar musu kar ai wasa da wani motsin Raudha mai karfi saboda cikinta a ɗofane yake. Hasalima bed rest shi tafi bukata fiye da komai a yanzun.
Tabbas abu biyu da Raudha tayi ya matukar birge Anne da Bappi. Na farko tambayar duniya sun mata akan abinda ke tsakaninta da Ramadhan ta keƙashe
ƙasa ta dage akan babu komai. Tushen abinda ya faru tsakaninta da shi a jiya harya doke ta (dan duka suka danganta abun saboda alkunya da kawaici irin nasu)
amma sai Raudha tace wai faɗuwa tai a toilet. Batasan su da idonsu sukaje sukaga halin da take a ciki ba. (Saboda sun ɓoye mata cewar Bilkisu ce ta kaita
asibiti suma acan suka amso ta). Na uku tunda ta tashi babu wanda yaga ko ɗigon hawayenta alamar ta dake, wannan ya sakama Anne ƙwarin gwiwar cewar lokaci
yayi da zatai training ɗin Raudha a bigiren da sai Gimbiya Su’adah da shaiɗanunta sunyi dana sani. Ramadhan kuwa zai matuƙar gane kuskurensa, ba ita zata
hukuntashi ba Raudha ce da kanta zata hukunta shi.
Hhhhh ashe akwai sabon show????????????.
★★★★_
Tsahon kwanaki uku Raudha na a Taura house babu wanda ya sani sai Bilkisu da Pa da su Anne. Koda Gimbiya Su’adah taga Bilkisu bataji komai ba
tunda tasan dama tana shirin dawowa gida ai. Zuwa yau baƙi sun fara isowa daga masarautar su gimbiya Su’adah. Hakama a bangaren sauran matan gidan tunda
kowa zai aurar da ɗa. Daga Taura ma dai wasu sun iso sai dai maza ne.
Babu wanda ya sake jin labarin Ramadhan babu kuma wanda ya bibiyesa, a kwanaki ukun nan ma ko a labarai sai dai kaji ance Shugaban kasa Ramadhan ya
kaddamar da kaza da yawun wane. Amma shi ko sau ɗaya ba’a nunasa ba sai a yau da kowa yasan za’a tafi hutu na ƙarshen shekara da Christmas. Kuma kakakin
shugaban ƙasa ya sanar a Taura house shugaban ƙasa zaiyi hutun nasa baki daya.
Hankalin Adda Asmah ya tashi matuka, musamman data kira bokanta yace sam karta yarda. Ita da suka gama cin burin kai Aynah government house kai
tsaya ya Ramadhan ɗin zai musu haka, ya tabbatar mata ajiye Aynah a Taura house bazai taɓa haifar musu ɗa mai ido ba. Garama tayi duk yanda za’ai ta gyara
barnar. Zuwa dare kuma tazo tare da Aynah zai mata wankan magani na ƙarshe da shine sirrin mallakar Ramadhan da duk ma wanda zai raɓesa, zai koma baijin
magana ko umarnin kowa sai nata ita kaɗai Aina’u.
A rikice tai kiran Number Gimbuya Su’adah. Ita kanta gimbiya Su’adah ranta ya baci dan yau bata maida hankali akan television ba balle tasan da
labarin. Tana can suna tafka rigima da Pa akan kofa dinner sai sunyi har guda uku idan ance sauran an hanasu. Shi kuma yace isar da bataiba kenan.
Ramadhan ta shiga nema, dan rabonta da shi yau kwana uku kenan tun randa ta kunna zuciyarsa akan kiran daya sanar mata su Bappi sun masa. Maimakon
hankalinta ya tashi matsayinta na uwa ta nemesa sai ta share da cewar yana lafiya shiyyasa ko kuma aikin office ne ya rikesa.
A lokacin kwance yake yana barci, dan tunda aka baro Raudha daga gidan ya tsinta kansa a wani irin yanayi mai matukar wahalar fassara a garesa. Ya
rasa mike masa daɗi mi kuma zai kama. Ransane a ɓace? Ko damuwa da halin daya jefa ƴar mutane? Kokuwa halin da ke shirin riskarsa na auren wadda shi kansa
har yanzu baisan dalilin da yasa yake mata wannan mahaikacin son ba. Bisa lallabawar cos yake fita office. Sai dai baya wani jimawa yake dawowa gida. Kuma
kullum ya shigo sai yaje ɗakin Raudha da mama ladi bata gajiya da gyarawa. Hatta jinin da Raudha ta zubar a wancan ranar idan bama faɗa maka akaiba bazaka
sani ba. Yakanje ya kwanta a saman gadonta. Sai dai baya haɗa mintuna biyu kansa zai shiga sarawa da karfi har sai ya fito ya koma nasa.
Kunnawar da Ginbiya Su’adah tai masa yau ma ya sakashi tashi cike da fusata. Yay azamar dafe kansa dake juya masa da karfi. Sai kuma ya mike yana
kallon agogo. Ƙarfe kusan sha ɗaya na dare. Amma tsabar yanda yake jin zuciyarsa tuni ya fice cikin ɓadda kama dan bazai iya jira sai gobe da zai huce Taura
house ɗin ba ma, yanda yake komai saika ɗauka ana controling nashi da remote ne, dukya birkice, baya gane komai sai abinda su gimbiya Su’adah sukace yayi.
Maimakon ma ko a motane yay fitar sirrin kamar yanda yakeyi, sai kawai ya fice da ƙafa ta karamin gate da taimakon odilan ɗinsa da baida ikon hanashi yin
hakan saboda akwana biyun nan sam baya gane kan shugaban ƙasa, baya son yace wani abu kuma ga wani game da hakan saboda gargaɗi da Ramadhan yaja masa mai
ƙarfi akan yanda yake fitar sirri inhar ya bari wani ya sani bayan shi duk hukuncin daya zartar a kansa yay kuka da kansa kawai. Cab ya tare sai taura
house.
A dai-dai lokacin da Ramadhan ke nufar Taura house Adda Asmah ce da Aynah sun dawo daga gidan bokanta anyo mata wankan maganin mallaka. Sam batai
tunanin haɗuwa da Ramadhan ba, shiyyasa ta yanke shawarar biyawa ta Taura House takai maganin da bokan ya bata akan gimbiya Su’ada tai turare da shi
matsayin na rufa idon su Bappi akan events ɗin da suke sonyi. Sai dai a zahirin gaskiya ba hakan bane. Na rabata da Ramadhan ne baki ɗaya yanda zai koma
karƙashin ikon ita Addah Asmah ɗin.
Kusan a tare Ramadhan da su Addah Asmah suka iso Taura house. Sai dai shi ya rigasu shigowa saboda an tsaya buɗe musu gate shiko yay wuff ya shige
yanda ko mai-gadi ma bai lura da shi ba. Kai tsaye falon hutawa na gimbiya Su’adah ya nufa ta baya kamar yanda ta sanar masa ya sameta a can. Ko zama
baiyiba Addah Asmah da Aynah suma suka shigo kamar yanda Gimbiya Su’adah ta sanarma Adda Asmah itama ta sameta anan. Adda Asmah bata san Ramadhan zaizo
taura house ba. Haka zalika gimbiya Su’adah batasan Adda Asmah na tare da Aynah ba tunda tasan dokar dake tsakanin kar Ramadhan da Aynah su haɗu sai bayan