BAKAR INUWA 60

an ɗaura aure…….
*_Tofa dole na dara kafin na cigaba????????????????, wannan fa shine ana dara ga dare yayi????. Ga boka yace kar…..????????bara dai kawai na tsuke bakina muga yaya wasan zai
kaya to._*
★Wani irin ihu Adda Asmah da Ayna’u suka fasa a tare cikin tsantsar tashin hankali. Dan kuwa sallamar Aynah dake gaban Addah Asmah tayi dai-dai da
ɗagowar Ramadhan saboda ƙofar falon da aka buɗe batare da yayi tunanin wani zai shigo musu ba.
Ita kanta Gimbiya Su’adah dake ƙoƙarin kunna buner ta saka turaren hayakin magani da boka yace ta dinga sakawa a duk sanda Ramadhan yazo gareta ta
saki tare da yin wani uban tsalle tana dafe ƙirji.
“Innalillahi wa-inna’ilaihirraji’un. Allahumma ajirni fi musibati…..” Ramadhan ya ambato a jere saboda suna haɗa ido da Aynah gabansa yay wani
irin mummunar faɗuwar da har sai da kansa ya sara. Hannu ya kai ya dafe kan saboda yanda ihunsu ke shiga masa har tsakkiyar kwakwkwararsa. Duk da kunne sa
daya toshe ihun bai fasa shiga ba. Kai bama shi ba, hatta duk wanda yake kusa da sashen gimbiya Su’adah dole ne yaji tagwayen ihun nan.
Pa ne ya fara shigowa a kiɗime. dan kamar yanda ya saba duk dare kafin ya kwanta sai ya zagaye gidan ya tabbatar da komai normal jininsa kuma ya motsa
yauma hakance ta kasance. Yana ta wajen babban gate ɗin gidan baki ɗaya yaga shigowar Ramadhan. Duk da ya rufe fuskarsa da hular jacket ɗin jikinsa da
facemask hakan bai hanashi shaidashi ba. Dan babu wata ɓadda kama da Ramadhan zaiyi bai gane abinsa ba. Shiru yay ransa fal al’ajab, bai gama dawowa
hayyacinsa ba kuma sai ga motar su Adda Asmah ta danno kai. hakan ya sashi kiran Anne da Bappi da Yafendo a waya yace suzo dan ALLAH. Shi kuma ya biyo bayan
su Addah Asmah ɗin.
Takan kowa Pa bebiba tsakanin Aynah da Adda Asmah data zube ƙasa kamar wadda ma ta suma. Yakai ga ɗansa dake jujjuya kansa cikin tafukan hannunsa
alamar akwai abunda ke faruwa da shi. A dai-dai nan su Anne ma suka iso, suma duk kan Ramadhan ɗin sukayi hankalinsu tashe. Sai kawai sukaji ya fasa wata
gigitacciyar ƙara da duk wanda ke a gidan nan ƙarya yake yace bai jita ba.
Innalillahi kawai suke ta ambato, Pa ya riko Ramadhan dake shirin kaiwa ƙasa ya ringumesa a jikinsa. Rawa sosai jikinsa keyi kamar mazari. Hakan yasa
Bappi ma tallafawa suka riƙosa.
“Basheer kafin attention ɗin kowa ya dawo nan ɗin mu fita da shi”.
Shawarar Bappi Pa yabi, suka kama Ramadhan da har yanzu yake faman jujjuya kai sukai waje da shi, fitarsu kamar ƙyaftawar ido jama’ar gidan suka fara
tururuwar shigowa falon a gurguje. Su kum ganin Adda Asmah kwance duk sai sukai kanta. Da wannan damar Anne da su Yafendo suka zame jikinsu suka bar falon.
★★
“Ya ALLAHU miya faru? Suma yay?”.
Cewar Anne dake shigowa falon Bappi idonta akan Ramadhan da suka shimfiɗar a ƙasan carpet Pa na kokarin shafa masa ruwa. Kai kawai Bappi dake zaune kan
Ramadhan ɗin a cinyarsa ya ɗaga mata. Wani nannauyan numfashi Ramadhan ya ja a fisge sai kuma ya sake riƙe kansa zai fasa ƙara Bappi ya rufe masa bakki.
“Tabbas akwai matsala, inaga akwai lamarin azzaluman aljanun sihiri tare da shi”. Cewar Yafendo tana kuka. Da sauri Anne ta fita a ɗakin tana faɗin
bara ta ɗakko alkur’ani. Bappi na kiranta tazo ta ɗakko na ɗakinsa bama taji ba harta fice. Zaune ta iske Raudha na karatun alkur’ani da alama sallar
shafa’i da wutiri ta idar. Ai tama manta da batun bedrest da Raudha keyi ta kamo hanuntan.
“Ameenatu taso ga inda ake buƙatar karatun nan naki can.”
Hankali tashe Raudha ta dakata, ganin Anne a firgice yasa batabi ba’asi ba ta mike kawi ta bita. Sanye take cikin dogon hijjab fari har ƙasa. Dan haka
baka iya ganin komai nata sai fuska da tafukan hannu………✍