Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 73

Kwanaki biyu da yin wannan biki na cikar masu mulki shekara ɗaya akan madafun iko Malam Dauda ya koma hutawa da shatara ta arziƙi. Dan kuwa kujerar makka har uku, tare da kuɗi masu yawa da galleliyar mota da alƙawarin buɗe masa manyan shaguna a hutawa da kuɗi zasu dinga shigo masa akoda yaushe. Wannan farin ciki ya sashi danne son Asabe daya san har Abada bazai iya dainawaba.
        A randa M. Dauda yabar Bingo a ranar hoton wani video ya karaɗe yanar gizo da duk mai wayar da take iya buɗe data zai gani. Video ne daya kasance na Aynah a cikin club ana aikata masha’a da ita. Sai kuma wani shima a cikin ɗaki kusan su biyar duk mata. Abinda zai baka mamaki na club ɗin babu face mask kamar yanda Ramadhan ya sani.
      Aminu ya saki wannan video ne bayan ya saka dukan abokansa sunyi amfani da Aynah a wannan dare wasuma harta baya (Wa’iyazubillah????) yayi hakane a dalilin kawo mata ƴammatansa da yay gidan ta nuna itafa ta gaji ya sallameta hakanan kokuma ta tona masa asiri ga iyayensa da yake yaudarar nuna musu shi ɗin mutumin kirkine. Shiko ya tabbatar mata kafin tayi hakan shi zai fara tona nata a sirin wa duniya sai yaga nata da nashi wannene zaifi gawurta da kayatarwa. Tayi kuka ta roƙesa iyakar roƙo amma yay kunnen uwar shegu da ita sai da ya saki.
      A lokacin da wannan video ya riski su Addah Asmah data haukata kanta a neman asirin hallaka Ramadhan da wulƙanta rayuwarsa data Gimbiya Su’adah har ƙasar China ta yanke jiki ta faɗi. Kwannta biyu kenan da dawowarta NAYA, wata kawarta ta rakata China wajen wani gagarumin masanin tsafi. Sun dawo zuciyarta cike da jin ɗunbin nasara saboda abinda matsafin ya haɗo musu, ta tabbatar idan har tai amfani da su Gimbiya Su’adah da zuri’arta sun zama labari kenan. Sai gashi a yau da take shirin zuwa Taura house da fuskar yaudarar roƙon gafarar gimbiya Su’adah danta aiwatar da aikinta wannan mummunan labari ya  baje ƙasar NAYA dama duniya tunda abune na media ako ina zaka iya ganinsa.
     A firgice ma’aikatan gidan nasu da kanwar Aynah suka rufu a kanta sai dai babu alamar numfashi tattare da ita. Dole Zulfah tai kiran asibitin da suke ganin likita dan ta nema no na daddyn su ma bata samuba kasancewar shi bayama kasar.
     

          Hatta da gimbiya Su’adah da ayanzu babu wanda ta tsana a duniya sama da ƴar uwar tata abin ya firgitata, balle kuma Fulani da itama ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a sume dalilin tanada hawan jini.
     Raudha ma ta gani kafin Ramadhan, amma ta kasa nuna masa sai zama datai taita kuka dan abun ya ɗaga hankalinta. Musulma ɗiyar muslmai gaba da baya itace a wannan halin duniya ke gani babu ko kunyar mahaliccinmu. Kaicon wata wayewar, kaicon wata dukiyar, kaicon wata damar dan da wata BAƘAR INUWA ce da ita gara rana ma.
      Koda Ramadhan ɗin shima ya gani baiji abin saboba tunda a gabansa aka aikata, sai dai abinda ya bashi mamaki fitar videon bayan shekaru. Hakan na nufin dan kinyi barna ko kayi ka binneta da tunanin ta wuce mutane bazasu ganiba watarana UBANGIJI idan yaso sai ya tonota ta hanyar da kai bakai tunani ko tsammani ba. Sannan ya jiraka a madakata kazo ya hukuntaka dai-dai da laifinka dan shi bai kasance azzalumin sarki ba………..✍

Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹????‍♀️⛹????‍♀️????

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button