BAKAR INUWA 78

Duk ɗan siyasar da aka samu ya bama yara makamai ko kayan maye domin masa campaign ko makamancin hakan to takararsa ta ruguje bazaiyiba. Wannan al’amari shine ya saka ƴan siyasar shiga hankalinsu, matasan kuma dama mafiya yawansu sunda aikinyi wasu sabo dayine da kuma shegen kwaɗayi ke ingiza zukatansu.
Alhmdllhi campaign ya wanzu cikin nutsuwa da burgewa, inda har akai aka gama babu wanda yaga matar shugaban ƙasa ko da a poster. Sai dai Ramadhan yasha fita da Abdull da Alhaji ƙarami da shima yake neman cika shekara guda da haihuwa. Zuwa yanzu mutane da yawa sun fahimci shugaban ƙasa Ramadhan baya ra’ayin matarsa a harkokin siyasa ne kawai, yana kishinta yana killace abarsa matsayin tashi shi kaɗai. Hakan ya matuƙar birege mutane, harma a wannan campaign ɗin wasu ƴan siyasar sukai koyi da hakan musamman ƴan takarkaru.
Dan hatta abubuwan alkairi da Raudha ke shimfidawa a bayan fage bazaka taɓajinsa a bayyane wa duniya ba, acewarta tayine domin ALLAH badan wani ya sani koya yaba mata ba. Mijinta kuma ya bata goyon baya ɗari bisa ɗari.
Alhmdllhi an gama campaign lafiya ankumayi zaɓe shima. Yayinda sakamakon zaɓe ya tabbatar da sake zaman Ramadhan B. Hameed Taura matsayin shugaban ƙasa a karo na biyu a ƙasar NAYA. Duk wani masoyinsa ya tayasu murna da fatan sauke nauyin al’umma a kansu.
Inda a wannan karon ya shigo sabon tsarin da sabon tsare-tsare da ƙudirirrika na musamman. Yayi sauye-sauyen wasu a cikin ministers da suka kasance zabin su Alhaji Yaro glass a wancan karon. Hakama vice president an sake sabo tunda su Alhaji Yaro ana can ana cin gabza a prison????.
Rantsar da shugaban ƙasa baifi da sati uku ba su Raudha sukai GRADUATION a makaranta. A kuma lokacin ta bayyanama school mate nata ko ita ɗin wacece. Ansha mamaki, ansha al’ajab da kace nace ga ƙasar NAYA ma ba makarantar kawai ba. Gaba ɗaya hidimar bikin fitar tasu ita ta ɗauki nauyin komai.
Ansha hotuna na tarihi kowa burinsa firt lady karta manta da shi duk da bata yarda ta buɗe fuskarta ba ko a wajen bikin kamar yanda Ramadhan ya bada doka. Yadai yarje mata ta sanar dasu ko ita wacece kawai..
A randa suka kamma bikin gama karatu a ranar ta sake fahimtar tana da ciki, taci kukanta tai gum da bakinta, sai dai batasan mai gayya mai aiki shi ya san da abunsaba tunkan ta sani. Sai ranar kawai yake bayyana mata ta gama boye-boyenta shi ya jima da sanin ya samo ribar farautarsa ai.
Galala tai tana kallonsa, shiko yay mata gwalo ya fice. Jitai kamar ta zauna taita kuka kawai. Ita wannan wane irin abune bata yaye yara sai sabon ciki. To babu yanda aka iya da hukuncin ALLAH, wasuma nema suke basu samu ba da kuɗi.
Tun tana zumbure-zumɓurenta harta ware suka cigaba da rainon ciki Mama Ladi ta yaye Alhaji Ƙarami. A randa Raudha ta haihu a ranar ALLAH yayma Addah Asmah dake fama da jiyya har yanzu rasuwa. Ba kowa yaji mutuwarba. Dan dama masu jiyyar tata sun matuƙar gajiya. Yanda bata nema yafiyar kowaba babu wanda yace ya yafe matan har gimbiya Su’adah da yanzu akai sanyi.
Bata sakema Raudha dai bakuma ta takura mata. Babbar damuwarta ma yanzu zaman Lubnah a gida da Muneera da a yanzu ta koma sai wheelchair saboda ƙafarta ta samu matsala a wancan haɗarin. Har kuɗi da gida da mota aka saka ga wanda zai auri Muneera amma duk wanda yazo ya ganta saboda raunikan da tayi a fuska sun canja mata kamani sai ya gudu. Bilkisu kuwa tuni harta haihu abinta ita da su Fatisa. Yanzu hakama shirye-shiryen bikin su Basma akeyi.
A wannan karon dai Ramadhan ya dage baza’ai bikin suna ba, ya dai ɗauke matarsa bayan arba’in sukai tafitarsu America domin hutawa na sati biyu tare da yaransu uku vice president ya cigaba da riƙe ƙasar NAYA kafin ya dawo. Dan jinjirin shima yaci sunan Mal. Dauda. amma suna kiransa Dawood. Raudha da Ramadhan na cemasa Abbati.
Satinsu biyu suka dawo NAYA harkokin mulki suka cigaba da tafiya yanda akai fata………..✍