BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 15

FARUQ POV.

Kamin ya isa gida sai da ya kira abokinsa Nura ya fada masa yadda sukai da abun da ya samu kana yai masa godiya. Ya isa gida cikin farinciki, ba zai ce be taba rika 100k ba amman ba kasafai ba, rabon daya rika 10k tashi ta kanshi ma ya manta.
Yana isa ya zare dubu biyu ya bawa Asiya ya ta girka abinci, sannan ya shiga daki ya taba mahaifiyarsa dake zaune tana maida numfashi a hankali.

“Mama ya jikin na ki?”

“Alhamdulillah, Aisha tace ka zo dazun ina bachi”

Ta amsa tana kallon yanayinsa dake bayyana irin farinciki da yake ciki.

“Eh na zo na tararda jikin na ki ne sai a hankali…”

Ya dora mata da labarin yadda komai ya faru ciki har da abun da Malam Musa ya kira shi yana fada masa Rafi’a ta yi, kamar wanda aka cirewa ciwo sai Mama ta nemi ciwon ta rasa zuciyarta tai fal, daman ciwon nata hawan jini ne na tunanin auren Aisha da kuma yunwar da suke wuni da ita su kwana da ita, abu ga talaka bawan Allah kadan ya ishe shi.

“Amman Allah ya saka masa da alheri, Allah ya faranta rayuwarsa ya daummawar da farinciki a cikin zuciyarsa kamar yadda ya faranta ranmu”

“Ameen, ni kaina ina tafe a hanya ina ta masa addu’a, Wallahi na jidadi sosai, domin rashin lafiyar nan naki ya dame ni, yanzu ki tashi ki shirya mu tafi asibiti”

“Aa wace asibiti kuma Faruq? Ai ni yanzu na ji sauki, daman ciwon ai na rashin kudin ne”

Wata kalar dariya Faruq yai wanda ya manta rabon da yai irinta har ya manta.

“Haba Mama saboda ciwon ki fa naje karbo kudin nan, kuma har ga Allah ni asibitin nai niyar kaiki”

“Aa ai ciwo kuma ya warke, da aje a kashe kudin a banza ai kara a kara ayi hidima, Idan aka karbi kudin lefe aka rage wani abu cikin nan ai sai a dan kara, in yaso sai ka dauki rabi ka ba mai hayar ka bashi hakuri”

“Ai ba za su isa ba, 80k ne muke biya shekara”

“Eh ka bashi ko 50k ne dai ka bashi hakuri kamin Allah ya budo mana wata hanyar samu sai ka cika masa”

“To Allah ya sa ya yarda, wannan matar ta kira min ruwa, Wallahi na gaji da halin Rafi’a Mama kullum da kalar fitinar da take bullo min da ita, bata da wata magana sai ta na sake ta”

“Ka kara hakuri tana maka haka ne saboda tana ganin baka da kudin yin wani auren, da ace ta san kana da kudi da ba zata maka haka ba, koma na rayuwa dan hakuri ne wata rana zaka ga komai ya wuce kamar ba ayi ba”

“Allah ya kara min hakurin domin har ga Allah ta kai kulu, ba wai zan sake ta ba ne bana son shiga hakkinta ne”

“Yanzu dai tashi ka tafi gurin sana’arka in yaso gobe sai ka samu mai hayar na san zuwa lokacin ya huce sai ka ba shi hakuri ka bashi dubu hansin din, Allah ya warwareka yai maka albarka, zuwa da yamma zan tafi gidan Kanen mahaifinku na fada masa yayi ya aiko da kudin lefen sai a hada da dan abun da aka samu”

“Toh Allah ya taimaka ni zan tafi”

“Ka dai baro mata abinci ko?”

“Eh akwai Taliya da wake, da cefane, idan na koma anjima zan siya mana abinci ina son na cire 5k a ciki”

“To Allah ya taimaka yai maka albarka”

“Amin Mama Allah kara miki lafiya”

Ya fada yana mikewa tsaye sai ta bishi da kallo ina na uwa da da tana jin kaunarsa na karuwa a ranta, ta fi kowa sanin cewar idan Faruq yana da mafita da tuni ya share mata hawayenta.
Kudin ya ciro ya cire 50 na mai haya sannan ya cire 5k ya mika mata 43k da suka yi saura, sannan ya fito ya nufi gurin aikinsa.
A hanyarsa ta tafiya ya saye waina sannan ya karasa shagon daman yana da plate da spoon da dan copinsa a shagon bayan ya bude ya wanke plate din sannan ya zuba wainar ya ci, ya siyo ruwa ya sha, tukuna ya hau gyaran shagon kamar yadda ya saba.
Be tashi ba sai 7:30 daman haka yake tashi kamin ya isa gida 8 tayi sai ya tsaya yai sallah a massallacin unguwarsu sannan ya shiga gida. A duk lokacin da zai shiga gida da tunani da fargabar abun da Baturiya zata masa, amman a yau haushin shiga gidan ma yake ji, har be san ta inda zai fara mata ba idan ya shiga.
Kamar kullum sai da ya tsaya yai sallah, sannan ya biya gurin mai siyar da balangon unguwarsu ya siye na dubu daya, ya biya shago ya siye shimkafa da sauran kayan masarufi sannan ya nufi gidansa.
Yayi mamakin ganin kofar gidan a bude domin bata saba barin kofar a bude ba, rufewa take wai a cewarta masu kudi ma basa barin gida bude sai takawa, hakan yasa duk wanda ya zo sai ya kwankwasa mata sannan ta bude. Sai dai yau kofar a bude ya same ta, sai ya shiga rike da ledodin a hannu nan ma sai ya samu kofar falon a bude, be yi sallama ba ya shiga saboda ransa a bace yake. Sultan kadai ya samu a falon zaune yana shan bobo, Sultan na ganin mahaifinsa ya sauko daga saman kujerar da sauri ya nufe shi.

“Daddy sannu da zuwa”

Sai da ya aje ledodin hannunsa sannan ya dauki Sultan yana murmushi.

“Sultan ya keke?”

“Lafiya”

“Me kake sha?”

“Bobo Momy ta siya min Bobo”

Jimmm Faruq yai sannan ya sauke dansa ya bude masa ledar naman daya siyo ya aje masa a gabansa.

“Zauna ka ci”

“To”

Ya zauna da sauri ya fara ci yana ta murna.

“Momy ma ta siya min kifi dazun”

Faruq be sake ce masa komai ba ya nufi kofar dakin tana tabawa ya ji a rufe, sai ya juyo ya kalli dansa.

“Sultan ina mamanka?”

“Tana ciki”

Kwankwasa kofar ya fara yi.

“Rafi’a ki bude kofar nan”

Sai ta amsa masa daga can ciki.

“Wallahi ba zan bude ba, ai na san dokana zaka yi”

“Kin san abun da kika yi kenan?”

“Eh mana, haka kawai muna fama da talauci zai zo ya kara mana da wata damuwar kudin haya shiyasa na karbi number sa na zage shi ai”

“To kin jawa kanki ya bamu kwana daya mu tashi mu bar masa gidansa, Rafi’a mi yake damunki ne wai? Miyasa ke baki son zaman lafiya? Duk wani abu da zai tayar min da hankali shi kawai kike nema”

“Ai na bashi 100k yau, na biya shi kudinshi kuma ya bada takardar ya yarda mu zauna”

Natsuwa yake kokarin yi wai ko zai fahimci inda kalamanta suka dosa, ta bashi kudi haya?

“Rafi’a”

Ya kiranta a hankali, sai ta amsa daga jikin kofar da take, rike da sabuwar wayarta.

“Na’am”

“Maimaita abun da kika fada min”

“Na ce na bashi kudin hayar har na kara masa da 20k sama”

“Ina kika samu kudi?”

“Yaya ne ya ba ni Umma ta cika min sauran”

“Bude kofar nan mu yi magana”

“Ba fa zan bude ba, tufafin ka nan a falo na fitar maka, kuma abinci ka yana nan kusa da kujera, kai da Sultan ku kwana a falo ba zan bude ba”

Ba dukan abun da tai kawai take tsoro ba, har da na sabuwar wayar data siya da kuma kudin data biya hayar domin ta san abu ne mai wahala ya yarda da ita.

“Ki bude kofar nan Rafi’a ba zan dake ki ba, na taba dukanki ne? Duka ai ba halina ba ne ina son nai magana ta fahimta da ke”

Shiru tai masa kamar bata gurin.

“Na samu 100k yau”

“Da gaske? Ko dai dan na bude ne”

“Wallahi da gaske ne, Rafi’a i need to talk to you seriously ki bude kofar nan ko kuma na tafi na barki ki kwana a gidan ke kadai…”

“Wallahi Faruq dukana zaka yi idan na bude ni na san abun da na yi, duk abun da na yi ai dai ina sonka ka san dai ina sonka, bakin talaucin nan ne bana so, saboda farar kafa ce da kai Faruq, aurenka be karbe ni ba, da yanzu na yi arziki”

Ta fada da muryar dake nuna tana daf fashewa da kuka. Murmushi jin yadda ta juya abun zuwa kansa, wato shi ne mai farar kafa ba ita ba.

“Na ji bude mu yi magana”

Ta dade tana tunani sannan ta nufi karkashin filonta ta saka wayar, ta nufo kofar ta bude cike da tsiro sannan tai baya ta haye saman gado, shi kuma ya shigo cikin dakin yana kallonta, yana bude baki yai magana sai wayarta tai ringing, yanayin yadda ta razana kadai ya isa ya nuna bata da gaskiya, saurin nufar inda wayar take ta yi ta dauka ta kashe ta gaba daya.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button