BAKAR WASIKA

BAKAR WASIKA 16

Ad

_____

AMINATU POV.

Daga jiya zuwa yau da aka canja mata daki sai ta ci kadaicin ya karu, domin a can tana jin hayaniyar mutune a wannan dakin komai babu kowa sai ita kadai, sai duk ta ji tana kewar gidansu da rayuwarta ta baya.
Bata san dalilin daya saka aka canja mata daki ba, bata san ranar da wani zai zo nemanta ba, bata san ranar da rayuwarta zata koma daidai ba, har yanzu ji take kamar komai mafarki ne.
Tana fara tunanin ta ji wani irin tsoro ya taso mata, sai ta ji wani abu yana mata yawo a cikin kai karar bindigogi ya dawo mata hayaniyar mutane da rokon da Baba yake musu ya dawo mata kamar lokacin yake faruwa. Wani irin abu ta rika ji kamar kanta ba zai iya dauka ba, gashi tana son ta yunkura ta sauka saman gadon amman dama domin kafafuwanta basa iya komai a yanzu, bakinta ma ya dantse gam duk yadda ta so tai ihu ko kuka sai ta kasa. Ji tai bata bukatar komai a lokacin sai tafiyar da babu dawowa. Da wani irin karfi ta tashi zaune ta fisgi robar ruwan dake hannunta wanda hakan ya bawa jini hanyar fita ya fara zuba, jiki na rawa ta fisgo robar da karfin da bata taba sanin tana da shi ba sai karfen ya fado gefen gadon, bata tsaya komai ba ta hada robar a wuyanta tana kokarin aika kanta da kanta inda take ganin kamar idan ta tafi ta huta da komai.
Wannan karon ta samu sukunin bude baki, sai dai ko kadan hakan be bawa muryarta damar fita ba, hawaye kawai take babu kakautawa tana ta yaki da numfashinta, kamar an zare mata lakka haka ta ji wani abu ya sauko mata wanda ya zare duk wani sauran kuzari dake jikinta. Tun tana kallon kofa tana numfashi a hankali har numfashin nata ya fara nisa ta komai ya fara mata dishe dishe alamar ta fara ban kwana da duniya, ga jinin hannunta sai zuba yake.

TALBA POV.

As usual every weekend a falon Momy ko Daddy ake karyawa tare da kowa ciki har da Daddy da matarsa, sai dai mafi akasiri an fi cin abincin safe a bangaren Momy, Daddy zai zo bangarenta aci tare da shi, idan an gama ko kamin a fara duk wani mai wata bukata zai gabatar masa.
Sai dai wannan karon a bangaren Daddy Momy ta saka masu aikinta su kai komai wanda hakan ke nuna cewar a bangarensa za a karya.
Duk abun da ake Talba na zaune dinning yana lasa wayarsa, be dago ba har sai da ya ji saukowa Momy, sannan ya dago ya kalleta.

“Momy ina kwana?”

“Lafiya kalau an tashi lafiya?”

“Alhamdulillah”

Ya amsa yana tashi tsaye sai da ya bar dinning din ta kira shi.

“Talba”

Juyowa yai ba tare daya amsa ba.

Ad

“Ka yi hakuri da abun da ya faru jiya, raina ne ya bace”

“Babu komai Momy, ke ai uwata ce Wallahi ban rike ki da komai a rai ba”

Wannan maganar da yai sai ya saka Momy ta dan ji nauyinsa, kasa hada ido tai da shi har ya juya ya fice daga falon. Kai tsaye bangaren Daddy ya nufa a bude ya samu kofar shiga falon, hakan yasa be yi sallama ba kamar yadda ya saba ya nufi gurin da suke karyawa.
Leila kadai ya samu zaune a dinning din ta saka plantain a gaba tana ci, tana sanye da wani jan yadi kanta sanye da bakar hula, fuskarta ta ji hoda sosai sai dan janbakin data shafa, ta yi kyau sosai abu ne mai wahala mace ma tai mata kallo daya ta dauke ido balle kuma namiji. Talba yaja kujerar dake facing dinta ya zauna yana kallonta, shi kansa ya san ta yi kyau, sai dai ba al’adarsa bace fadawa mutum cewar yayi kyau ko yana da kyau, musamman mace, no matter yadda take da kyau ba zai taba iya bude baki ya furta cewar ta yi kyau ba, kuma ba zai zake da yawa gurin kallo ba gudun kar a ankara da shi.
Dauke idonsa yai bayan ya zauna, sai a lokacin ya tuna cewar yau be tura mata sakon barka da safiya ba, kuma ba zai iya tura mata a yanzu ba gudun kar tace saboda ta yi kyau ne.
Gaba daya ya tattara hankalinsa ya maida gurin wayarsa, sai yai kamar be san da zaman Leila a gurin ba, ita kam daman gaisuwa ba halinta ba ne bata saba gaishe da mutane ba bayan Momy da Daddy, balle kuma shi duk kuwa da irin sanin da tai na son a girmama da yake, sai dai ta kasa dauke idonta daga barin kallonsa duk kuwa da irin bugawar da zuciyarsa take after every blink. Har ga Allah bata iya fadar irin son da take yi ma Talba, da ace ta dauki biro da zayyano irin kaunar da take masa da alkalumman rubutu da takardun duniya sun kare bata gama rubuta irin kaunar da take masa ba. Sai dai har yanzu ta rasa gane manufarta a kanta, miyasa ba zai dauki rayuwa da sauki ba? Ya sauko da kai su yi soyayya kamar sauran masoya? Har yaushe zata yi ta jiran ya canja rayuwarsa? Anya ma zai canja din? Bata raba dayan biyu ba ta ji yana amsa waya, bata iya fadar cewar kiransa akai ba ko kuma shi ya kira domin wayarsa a silent take.

“Yeah ni ma na kwana da yarinyar nan a raina”

Furucinsa ne yasa ta kara tattara hankalinta tana saurarensa.

“Okay”

Shine last abun da ya fada sannan ya sauke wayar, ya daga kansa yana kallo Amal data nufo inda suke sanye da riga da wando yan patistan.

“Good morning Ya Talba”

“Morning Little Sis”

Ya amsa yana aikawa PA sa sakon kar ta kwana.

‘Ka yi magana da wannan number zai fada maka ko nawa yake bukata sai ka tura masa’

Aje wayar yai bayan ya aika sakon. Leila bata fahimci komai a wayar ba, sai dai ta fahimci da Ali yake magana domin yanayin yadda ya amsa wayar ya tabbatar mata da hakan. Sai da kalmar da ita na kauna a raina ya fi tsaya mata a rai.

Ad

_____

1 2 3 4Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Related Articles

Back to top button