BAKAR WASIKANOVELS

BAKAR WASIKA 15

“IPhone? Ina kika samu IPhone Rafi’a?”

Ta yi shiru sai kallonsa take. Shi ma kallon tsoro yake mata domin lamarinta a yanzu ya fara bashi tsoro ta fara wuce tunaninsa.

“Ko yaya ya siya miki?”

Nan ma shiru tai, at first ya fusata sai dai a yanzu kwakwalwarsa cike take da tunani kala kala. Karasa yai kusa da gadon ya zauna gabansa n mugun faduwa, yana ta kokarin ganin ya kawarta yaye yayen da zuciyarsa take son masa akan Rafi’a. Zaunawa yai bakin gadon yana kallonta.

“Rafi’a ki saka tsoron Allah a ranki, ina son ki san cewa duk abun da aka samu a duniyar nan a nan ake barinsa, ba a zuwa lahira da komai sai aiki da mutum ya aikata, Rafi’a dan Allah ki zama mai tunani ki duba future din Sulta da abun da yake cikinki, na san ni talaka ne ba zan iya miki komai yadda kike so ba, amman da ki je ki aikata wani mummunan abu da aurena kuma kina uwar yayana kara na sauwake miki ki auri mai kudi idan har hakan zai kawo miki mafita”

Yana maganar idonsa ya cika da hawaye, domin har ga Allah be fatar matarsa ta aikata abun da zuciyarsa take raya masa.

“Ina son ki Rafi’a amman Wallahi zan iya sauwake miki saboda yayana da aurena”

“Ni fa ba iskanci na yi ba, Wallahi ban taba iskanci ba”

Ta fada tana soshe soshe kamar mai kuraje.

“To ina kika samu wannan kudin da wannan wayar?”

“Yaya”

“Kin yarda na tambaye shi?”

“Eh na yarda”

Ido ya kura mata domin ya san karya take, yayanta yana da rufi asiri amman ba zai iya siya mata iPhone ba, duk be san ko wace irin iPhone bace amman ya san tana da tsada tun daga yanayin wayar da kuma yadda yake ganinta ga yan mata. Kasa yai da kansa ya lumshe ido be isa yace ba zata rika wayar ba tun da har ta danganta cewar yayanta ne ya siya mata, ya san idan ya hana mahaifiyarta zata saka baki ko kuma tace zata yi fushi ta tafi gida, ko ma suce ya rabu da ita.

“Ina da ciki idan ka dake ni ka daki cikinka”

Dagowa yai ya kalleta.

“Saboda ban da kudi shi ya baki damar yin duk abun da kike so?”

“To Faruq kai ma kasan ni ba ajin ka bace amman…”

“Haka ne…”

Ya fada sannan ya mike tsaye.

“Bari ki sauke abun da yake cikinki, labarin rayuwarki da tawa zai canja komai zai zo karshe”

“Da gaske?”

Ta tambaya cikin farinciki har ga Allah babu abun da take so kamar Faruq ya sake ta ta auri mai kudi, tana sonsa kan amman tafi son ta tafi inda zata huta. Kallonta kawai ya dauke kai ya fice daga dakin, falo ya dawo ya zauna yana kallon dansa cike da damuwa.

“Dady ba zaka ci ba?”

“Aa Sultan ci ka ragewa Momynka”

Ya fada yana shafa kansa cike da so da kauna, haihuwar da Allah ya bashi kadai ya san wani babban arziki ne.

Shin kin san Kamshi na daga cikin abun da yake daga darajarki? Kamshi yana saka a ga kimar mutum a girmamashi musamman ma na Ramla incense, tana da turaruka kala ka kama daga na jiki dana daki da na tufafi, irin su Halud
Sandal flakes
Sandal wood
Signature
Kajiji
Damboun kajiji
Halud ball
Wardrobe ball
Coconut sandal
exclusive gowe
Black humra
Body milk
Kulaccam
Misik humra. Ramla Incense ta shirya tsab domin aika muku da turarenku har garin da kuke, da kudinki kalila ki samu turare mai kyau mai dadin kamshi da sanyaya zuciya, domin siye ko sari ku tuntubi Ramla incense ta wannan number 07038392576 tana aikawa har wajen Nigeria. You can check her Instagram handle ramla_incense. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=1fl5k3wnc4opb&utm_content=43xtopa

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button