Bakar InuwaBAKAR INUWA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELSUncategorized

BAKAR WASIKA 4

“Lafiya Kalau”

Ta amsa tana kokarin juyawa. Sai Ali ya bude motar ya fita.

“Ina zaki je?”

“Ciki zan koma, baka fada min tare da wani zaka zo ba”

Kallon mamaki Ali yai mata, ganin ta yi abun da bata saba ba. Wani irin tafasa zuciyar Talba take kadan ya rage ta kone, bude motar yai ya fito a fusace ya zagayo inda take tsaye.

“Na zo nan ne, saboda Daddy ya saka ni, ba dan ra’ayina ba, na fi karfin daukar wulakancin mace ko wace iri ce, na fi karfi na bawa na kasa da ni hakuri wannan ranar ba zata taba zuwa ba…”

Ali ya rasa inda zai saka kansa, sai kawai ya koma cikin mota ya zauna, shi da ya zo sasanci sai kuma a sake yin fada a gabansa. Talba na gama fada mata haka ya juyo ya dawo cikin motar yadda ya rufe ganbun motar kadai ya isa ya sanar da bacin ransa.
Kamar wanda akai wa gorin tuki haka yai ribas ya rika danna horn, Mai gadin ya bude masa gate da sauri, ya firgi motar kamar wanda ya shirya bakuntar lahira.

“Wannan wace irin soyayya ce Talba me ke damunka, wai anya kana son Leila kuwa?”

Da mugun karfi Talba ya taka burki, he got lucky babu motoci da yawa a titin.

“Fitar min a mota”

Ya fada ba tare da ya kalli Ali ba. Ba sabon abu bane gurin Ali ya saba nasa haka idan ransa ya bace ko suka samu tsabani, sai dai baya hana anjima ya neme shi.

“Kana da matsala Wallahi kana da matsala, wannan mugun fushin ban san inda zai kaika ba”

Ali ya fada cikin bacin rai.

“Ka san bana son ana min ihu”

“Mtsssss”

“And i hate tsaki”

“Ba zan fita daga motar ba”

Ali ya fada yana gyara zama. A take Talba ya bude motar ya fita ya barta kunne, ganin hakan yasa Ali yai saurin fita ya zagaya driver side ya cigaba da tukin yana mamakin rayuwar Talba.
Gefen Titi Talba ya dawo ya tsaya, a ganinsa kaskanci ne ya shiga napep balle kuma ya hau babur zuwa gida, not just that even tsayin da yake a gafen titi ba girmansa ba ne, wayarsa ya ciro ya kira direban gidansu.

“Ka zo ka dauke ni zan turo maka location ta whatsapp yanzu”

Shine kawai abun da ya fada ya kashe wayar ya kunna datarsa ya shiga whatsapp dinsa ya tura masa location din, sannan ya maida wayar aljihu yana kallon titi, har lokacin zuciyarsa zafi take masa saboda Leila ta kira shi da wani, how on earth zata kira shi da wani?
After like 15 min direban ya iso, da kalle kalle har ya hango inda yake ya faka masa motar, Talba ya bude ya shiga ba tare da yace masa komai ba, shi ma direban be yi kokarin yi masa magana ba domin ya san Talba baya son yawan gaisuwa da kuma kallo, idan kuma kana son bata masa rai to ka cika shi da surutu.
Suna isa gida ya bude motar ya fita ya nufi bangarensu, wato shi da Kabir sai dai kowa side dinsa dabam, kai tsaye bedroom dinsa ya shiga ya jefar da wayarsa kan gado ya cire rigarsa da agogo ya shiga bathroom, sannan ya ciri jean din dake jikinsa ya kunna shower ya tara jikinsa yana kallon kansa a katon madubin dake facing dinsa a bathroom din, kamin ya dukar da kansa yana kallon zanen sunansa da tattoo dake kirjinsa wanda babu wanda ya san da shi sai shi kadai, can kuma ya dago ya lumshe ido.

AMINATU POV.

Kusan ko wane gida dake garin an taba, wasu an kashe wasu an kwashe duka da dabobi, wasu an tafi da yayansu da mata, wasu kuma anyi ma matan fyade, sai dai ba kamar gidansu Aminatu ba, domin wulakancin da akai wa mahaifiyarta ya wuce na kowa mutum goma shadaya a lokacin daya, kuma aka kashe yayyayunta hudu, aka kona rumbun hatsinsu, aka raunata wasu, aka kora dabobinsu.
Ba gidan kadai ba garin gaba daya tsit yai duk kuwa da kasancewar barayin sun yi iya barnar da zasu yi sun tafi, amman tsoro ya hana kowa fitowa, sai kuke kuke kake ji a gidanje, sai dai gidansu Aminatu ya fita dabam da baka jin kukan kowa, har asuba Aminatu na boye karkashin gado, mahaifiyarta kuma tana zaune a bakin kofar idonta a bude amman bata iya komai kamar an zare mata lakka a jiki haka take ji, Sanusi kuma na tsakar gidan a sume. Kamar macijiya haka Aminatu ta fito karkashin gado, ta janyo zanen gadon dake kan gadon karfe dan bono na Inna ta nufi Inna dake kwance tsirara tana kawar da idonta tana kuka har ta karasa kusa da ita ta kulluba mata zanen. Sannan ta juya ta koma inda fitilar kwai take ta dauka ta kara haskenta, ta taka kamar mai koyon tafiya ta fito waje. Wani rawa jikinta ya fara yi hango rumbun abincinsu na ci da wuta, sai kuma ta juya a hankali ta sauke idonta kasa ta kalli gawar Iro, da ta Amadu, ga kuma Sanusi shi ma dake kwance, kafa na zubar da jini, gaba daya ilahirin jikinta ne ya fara rawa kamar yadda bakinta ma yake yi.

“Ya… Ya… Ya.. Ya..”

So take ta kira sunan daya daga cikinsu amman ta kasa, hawaye sai aikinsu suke a fuskarta. Ta saki fitilar numfashi na fitar mata da karfi, wani kuma na shiga da sauri. Juyowa tai ta kalli Inna dake kwance bakin kofar har lokacin idonta na zubar da hawaye, sai wulakancin da akaiwa mahaifiyarta ya fado mata a rai, komai ya zame mata sabo.

“Me muka musu?”

Ta tambayi kanta tana wani irin kuka na fitar hankali, sai kuma ta ruga da dugu gurin yayanta Sanusi ta taba shi. Sai kuma ta juya ta kalli yayanta Amadu dake kwance kai a fashe, take ta girgiza kai.

“Ba da gaske ba ne aa, wannan be faru ba, yan’uwana ba su mutu ba, ba ayi ma mahaifiyata fyade ba, wadandan nan mutanen ba su zo ba, komai be faru ba”

Ta tashi da sauri ta ruga da gudu daki ta koma gurin kwanciyarta ta kwanta taja abun rufa ta lullube ta kame guri daya ta runtse ido, da gaske so take ta farka daga bachin, so take komai ya zama mafarki. Sai a lokacin Inna ta samu kuzarin motsawa ta fashe da kuka.

“Allah ka isar mana ga bayinka Allah….”

Ta fada tana kara fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi ta taba zuciya. Jin kalamanta ne yasa Aminatu ta saka hannayenta ta toshe kunnuwanta ta kara runtse ido ta kwara wani irin ihu da muryar da bata taba sanin tana da ita ba.

“Aaaaaaaaaaaaaaaaaaaaa”

Ba makotansu kadai ba, har gidan dake tsakaminsu dashi gida biyar ne sai da suka ji ihun Aminatu.

>
Anya Leila zata kai labari kuwa na cewar sai ta koyawa Talba darasi?

Nikan nace Ali yana hakuri da wannan aboki nasa mai wuyar sha’ani da jin Kai????????????

Allah sarki Aminatu, ko da yake mahaifiyarta ce abar tausayi. ????????????


Na zo muku da albishir guess what? A have alot of kayan mata masu kyau gaske, akwai na infection, akwai maida tsohuwa yarinya, akwai set din da ake hadawa for matan da basa gane kan mazajensu, akwai na mallaka kala kala, muna kaza mai magani, tantabaru, akwai kaza mai Yasin, akwai na mallaka sirrine mai karfin gaske. Ina masu son zama madubi a gurin mazanje su? Ina matan dake cewa na gwada ban dace ba? Muna da gumba da garin magani kala kala da na tsarki ga Humra da turarunka kala kala amman fa na kayan mata. Akwai dan wata bakwai.
Ga masu bukata za su iya tuntubar number nan 08036126660 zan saka miki a mota na aika miki har inda kike da yarda Allah.

Serious Buyers Please idan ba ki shirya ba kar mu batawa juna lokaci.

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button