Labarai

Ban damu a tsoma ni a Jahannama ba: Mai kudin duniya ya girgiza intanet yayin da ya ce ya kusa mutuwa

Babban attajirin duniya Elon Musk ya girgiza jama’a bayan ya bayyana cewa sam bai damu ba don an saka shi a jahannama bayan ya mutu.

Musk ya yi martani ne ga wani mabiyin shafinsa na Twitter da ya shawarce shi da ya yarda da Allah a karshen rayuwarsa bayan ya wallafa cewa ya kusa mutuwa.

Mai kudin duniyan ya bayyana cewa mutane da dama za su wuta bayan ya nuna godiya kan kulawar mutumin a gare shi.

Mai kudin duniya, Elon Musk, ya yi wani rubutu a shafinsa na Twitter wanda ya girgiza mabiyansa a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, yana mai cewa ya kusa mutuwa.

Koda dai bai bayar da cikakken bayani kan halin da yasa shi fadin haka ba, mai kudin ya nuna rayuwarsa na gab da zuwa karshe.

Ya rubuta:

“Idan na mutu a cikin yanayi mai ban mamaki, ina alfahari da sanin ki/ka.”

Da yake martani, wani mabiyinsa mai suna @Almisehal wanda ya nuna damuwa game da rayuwar biloniyan ya ce ba zai mutu ba kafin lokacinsa.

Cikin haka sai ya kuma tambayi Musk kan ko har yanzu bai gane cewa akwai mahallicin duniyan nan ba, sannan ya bukaci da ya bayyana hakan idan har ya gano hakan kafin fitar ransa.

Da yake mayar masa da martani, Elon Musk ya fada masa cewa shi bai damu ba don an saka shi a wutar jahannama. Ga yadda hirar tasu ta kaya:

@Almisehal:

“Ba za ka mutu ba kafin ranar ka Elon.

“Duk da haka, kai ka kasance mutum ne na musamman a wannan duniyar.

“Abu daya nake mamaki: A matsayinka na haziki, ba ka gano cewa akwai babban mahaliccin wannan duniyar ba tukuna?

Idan ka yi, ka tabbata ka furta wannan kafin bugun zuciyarka ta karshe.

“Allah ya albarkace ka.”

@elonmusk:

“Na gode da sa albarkar, amma ban damu da shiga jahannama ba, idan har wannan ne makoma na, tun da yawancin mutanen da aka haifa za su kasance a wurin.”

Daga Hausa Legit 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button