BANBANCIN KABILANOVELS

BANBANCIN KABILA COMPLETE

BANBANCIN KABILA COMPLETE HAUSA NOVEL

〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Da Abdallah ya koma gida, Umma kadai ya samu cikin parlor, tana kallo.
“Assalamu alaikum my darling Umma, na same ki lafiya”? Ya fada yana hugging din ta.
“Waalaikumus salaam my troublesome son”.
“Kai Umma, kin iya ruining din moment, wai troublesome son, abun da zaki ce My handsome son, ko my cool and quite son” ya fada ashagwabe.
“Ohh ni Rukayya! Ya zan yi da kai ne, shagwaba sai kace mace”?
“Toh ni Umma wani shagwaba na maki yanzu”? Ya kara magana ashagwabe.
Da Umma ta daga hannun zata dake shi, ya tashi da sauri. Ta ce “zan kama ka ai. Ai ni da ace kai mace ce ko, ai da anga uwar shagwaba da laziness, da mijin ka ya sha wuya. Amma alhamdulilah, tunda kai na’miji ne, kaga inka fara samun responsibility akai, maybe ka dai na”.
“Umma ai in fada maki, mata ta shagwababiya ce, sai dai mu ita zuba ma juna shagwaba. Kuma dan Allah Umma kar ki buge ni, yau din nan na dawo agajiye ne, aikin nan is not easy at all”.
“Ni kam rashin kunyan ka har ina, Allah dai Ya shirya mun kai. Kuma tun da ka shigo, nake ta jiran ka mun complain, naji shuru, nayi zaton ka chanza ne, amma ina mai hali baya chanza halin sa. Kai da tun 2:30 ka bar aiki, sannan kaje gidan Wasila, sai ka zo yanzu kace ka gaji. Aiki kaje mata ne”? Umma ta tambaya.
“Kai Umma, ni dai kawai baki sona. Abu kadan ina fada, shikenan zaki fara mun fada, ina Abba na ya ke, dan shi kadai ke sona yanzu”. Ya fada ashagwabe.
“Gani nan dan albarka”. Ya ji muryan Abba. Daya juya, yaga yana shigowa ne daga waje, he was thinking maybe yana dakin sa ne. Bisa duka alamu, fita yayi.
“Oyoyo Abba na mai so na”. Ya fada yana kallon Umma, sannan yayi hugging din shi.
“Can ta matse muku”. Umma ta fada.
“Oyoyo my Auta. Ya aikin yau, hope dai bai gajiyar da kai ba ko”? Abba ya tambaye shi, hannun Abdallah acikin nasa, suka zauna tare.
“Ai Abba na ka bari kawai, na jijjigu yau sosai”.
“Allah sarki Auta na, sannu. Ka dinga hutawa fa”. Abba ya fada.
“In Sha Allahu” ya fada, yana ma Umma gwalo.
“Au ni ko, zaka sani ai”.
“Abba kaga Umma ko, ban mata komai ba fa”. Ya fada kaman zaiyi kuka.
“Kayi hakuri ka kyake ta, kishi take, kasan ba mai nuna mata irin wannan son”.
“Haka ne, Hamma Sudais bai zo ba yau, shi yasa”. Abdallah ya fada.
Umma ta kada kai, taki amsa masu, dan ta san indai ta amsa, haka zasu cigaba da tsokanan ta.
“Kaje kayi wanka, ka warware gajiya. Then In Sha Allahu yau bayan Magrib, ina da magana da ku”. Abba na gama magana, ya bar parlorn, ya wuce dakin shi.
“Toh Allah ya kai mu”.Umma da Abdallah suka fada atare.
Shima ya tashi, ya bar parlorn, ya je dakin sa.

Yana gama wanka, yayi alwala, ya fito, yayi dressing cikin ash jallabiyan sa, ya fesa turare, sannan ya fito parlor, suka hada hanya suka tafi masjid tare.
Da suke hanya, dan masjid din na can kasan gidan su ne, Abdallah ya ce “Abba, akan me zaka mana magana, ka dan bani clue mana”.
“A’a, ka bari in muka koma gida zaka ji”. Abba ya fada ba sign din dariya afuskar sa.
“Toh Abba”. Abdallah ya amsa.
Daga nan ba wanda ya kara magana acikin su, har suka isa masjid.
Suna idarwa, suka kama hanyan gida.
Acan gida ma Umma ta idar da sallah, tana jiran su aparlor. Tana ta tunani, mai Alhaji yake son fada masu ne haka, Allah yasa dai su ji alheri.
Har suka dawo gida, basu ce ma juna komai ba, nan hankali Abdallah ya tashi. Wanan da Abba bai danyi hira da shi ba ahanya, toh abun da Abba zai fada, must be very serious.

Suna isa gida, suka yi sallama, Umma ta amsa. Ko wanan su ya samu wuri ya zauna, sanan Abba ya gyara murya. Ya fara magana. “lokacin da na fita, Baffa Dajjo ya kira ni, yace inzo gida, naje. Da muka gaisa da shi, sai ya ce mun wai yana da magana ne akan Abdallah”. Ya fada yana kallon Abdallah.
“Kuma gaskiya maganan daya mun, ya taba ni sosai. Kuma dai kun san yanda yake, inya fara yarba ma mutum magana, especially mu da yake ganin mu as low class”. Abba ya fada.
Ran Abdallah ya baci sosai, dan yasan mutumin nan, ba abunda bazai iya fada ba, kar Allah yasa ma yayi embarrassing din abban sa ne.
“Kuma dai kun san shi, bayi da mutunci”.
“Ae” Umma da Abdallah suka amsa.
“Maganan akan auran Abdallah ne”. Abba ya fada yana kallon Abdallah. “Wai yaushe zaka yi aure ne, wai shi yanzu yana expecting kace ga wanda kake so, amma shuru. In kuma baka samu bane, wai baga yan mata nan da yawa acikin gida ba, mai ya hana ka zaban daya acikin su. Na ce mai ban sani ba, sai fa ya hau ni da fada, wai bamu iya training ba, duka yaran mu da nasu salon, Sudais kawai ya auri yar family, wai kar mu bari ya maka na dole. Ni yanzu ina son ka fada mun ne, baka da kowa ne”?
“Allah sarki Abba na, ban ji dadin abun da Kawu Dajjo ya maka ba, kuma In sha Allahu zan nema. Wallahi Abba na, dukan su ne basu da features din da nake so, they are just indecent. Sai ma sun zo asibiti, su dinga misbehaving. Amma nasan In Sha Allahu na kusan samun wanda ta mun, In sha Allahu ba zan baku kunya ba”.
“Hmmmmm, gaskiya bana jin dadin abun da mutumin nan ke yi. Ya bi ya raina mu haba. Ni kam kar ma ka kawo mun wata yarinya cikin familyn nan gidan nan”. Umma ta fada.
“Gaskiya ko ni am not in support ka auri yaran nan. Allah ya kawo maka ta gari”.
“Amin ya rab”.
Aranan dukan su sun yi shuru, ba mai ma wani magana. Duk basu ji dadin abun ba.
Shi kuma Abdallah, abun ya masa yawa, ga takaicin abun da kawu Dajjo ya ma Abba, ina kuma zai fara neman mata?

Thanks for reading, ayi sharhi filis, sharhi is life ????????????????????.

Comment
Like & Share.

~Zeexee ce~ ????️????️????️

[8/30, 1:19 PM] Abokiyar Fight????????: ????????????????????????
????
BANBANCIN KABILA
(Short story)
????????????????????????
????

TAMBARI WRTER’S ASSOCIATION

????((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al’umah))

*T.W.A*

https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/

WRITTEN BY ZAYNAB (zeexee)

MARUBUCIYAR

-RAYUWAR HUSNA

-MAHAKURCI MAWADACI (2020)

Dedicating this page to Fatima Zarah Eyman aka abokiyar bus????????????????????. I love you loooodie loooodie

7️⃣&8️⃣

Bismillah

“Babe wake up, it’s time”. Olamide ta tashi Nafisa.
“Dan Allah habibty ki bari in ankira sallah, wallahi jiya ban yi barci da wuri ba”. Nafisa ta fada.
“With all the warnings, kuma kin san bazan tashi ban tashe ki ba ko”?
“Am sorry, bari in tashi kafun kiyi fushi dani”.
“Ko ke fa”. Olamide ta fada.
Da kyar dai Nafisa ta tashi, tayi alwala, ita kuma Mide, ta riga ta fara sallah.

“Kai habibty, today is going to be stressful fa, ki ci abinci da kyau”. Nafisa ta fada.
“Wallahi na koshi haka. Ko so kike inyi loosing din shape dina ne”? Olamide ta tambaye ta tana daga gira.
“Toh! A yau kuma?
Ai ke kam no matter what you eat, ba zaki taba yin kiba ba. Just imagine, ni dake zamu narka abinci, at the end of the day, kiga ciki na ya karu, amma naki na nan flat”.
“Kai habibty, banda karya fa?
Kema fa cikin ki ba wani babba bane, sai an lura ake gani”.
“Ae, ai still dai ana gani ko”? Nafisa ta tambaya
“Ban sani ba”. Olamide ta amsa mata tana yatsina fuska.
Ta kara cewa “ni dai kiyi sauri mu wuce, indai abinci ne, zamu samu a cafeteria”
“Toh naji uwar masifa”. Nafisa ta fada
“Yauwa uban masifa”.

Suna isa school, suka fara zuwa bursary, suka bada receipt, dan daman sun riga sun biya school fees din su a bank. Daga nan suka fara biyan student unions, sukayi online reg ma. Arannan dai sun dade a school, dan basu bar school ba, sai misalin 5:30pm.
Agajiye suka koma gida. Suna shiga gate din gidan, wasu neighbours dinsu su biyu, suma student ne, suka rungume su. “Oyoyo Olami’s” daya daga cikin su mai suna Hafsat ta fada.
“Oyoyo my yar’fara”. Olamide ta amsa.
Nafisa kuwa, abun ya kai mata har wuya. Ta tsani taga ana shishige ma habibtyn ta haka.
“Ooh Olami’s, ko dan kiban nan baki yi ba. Ni na rasa irin wanan jikin naki, ba ya karuwa, kuma baya raguwa”. Halima dayan kenan, ta fada. Halima da Hafsat, dakin su daya suma.
Gidan da suke, one room apartment ne, bedroom, kitchen, and toilet. Kuma apartments hudu ke gidan.
“Nima na rasa roomie. Kuma gata da zubin fulani. Abun dake bata show, shi ne inkaji ance Olamide. Nan ma in baka san ita bace, toh zaka nima Olamide ka rasa”. Hafsat ta fadi.
“A’a Hansey, kar muyi haka da ke. Kuma bari mu shiga daga ciki tukun, kunga yanzu agajiye mu ke”. Olamide ta fadi.
“Awww, haka ne fa. Fisa baby, ya gajiya, na ma manta kina wajan”. Hafsat ta fada.
Nafisa kuwa ta riga ta cika, tayi fam, amma bata son su gane, sai tayi faking din murmushi, ta bar wajan. Olamide ko ta riga ta san abun dake damun kawar ta, sai tayi murmushi, ta ce masu Hafsat “zaku biyo mu dakin mu ne yanzu, ko kuma sai bayan isha ku shigo kaman yanda kuka saba”?
“Hmmmm, zamu zo bayan isha, saboda alokacin hira ke yin pepper ko Hafsah”? Halima ta tambaye ta.
“Ae hakan ma yayi. Amma Olamis, baki kyauta ba, ko kiyi tambayan su Khausar da su iklima”.
“Awww sorry, na ma manta da su wallahi”. Olamide ta fada
“Sun ce sai next week zasu dawo. Kinsan Khausar da Hafiza cousin’s ne, kuma rana daya suke zuwa. Su Iklima da Mufida ma, suma sunce sai next week”.
“Gaskiya ne, zamuyi complete kenan next week. Allah ya dawo dasu lafiya”.
“Amin”. Halima da Hafsah suka amsa.
“Yauwa, kunga bari in shiga ciki, na gaji sosai”. Tana fadan haka, ta bar wajan, bata ma tsaya jin amsan su ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button