NOVELSUncategorized

BARIKI NA FITO (BOOK 2) 19

BOOK 2
                     PAGE 19
D’an shuru yayi kanshi na k’asa yana zubar da hawaye, yana son Zainab yana mata tsantsar so, but da yasan haka take daya ro’ki mutuwa, daya ro’ki Allah ya d’auki rayuwarshi da yasan zaiga irin wannan mummunan ranan……..
Jin yayi shuru yasa ta Fara fad’in Yarim……

Yace I said keep quiet, I don’t want to listen to you….  Zainab even at once kin taba tunanin irin yanda zanji in nasan gaskiya a kanki???…… Kin taba tunanin ya iyayena zasu d’auki abun in suka San koke wacece??…..  Zainab mai kika d’auki rayuwa??  Mai yasa kikai wasa da feelings dina??  You don’t love me……  Wani hawaye mai zafi ya zubo Mai sannan yaci gaba da fad’in, tunda bakya sona Mai yasa kika aureni, Zainab inda kin fad’amin bakya sona tun Farko kud’i kike so, I will give you d money dat you want…..  Basai kin yaudareni ba kin aure ni b…..
Kafin ya k’arasa abunda yake son fad’a ta Fara matsawa kusa dashi, daka mata tsawa yayi tare da fad’in karki zo inda nake….. Tari ya farayi Sosai……
Da sauri ta nufeshi tare da rik’eshi Tana buga mishi baya a hankali, tana kuka ta Fara fad’in Yarima I knw dat I have lies to you, na boye maka koni wacece Nasan wannan gaskiya ne, but Yarima abunda aka fad’a maka Akan son da nake maka karya ne…..  Yarima you are my life, Yarima I love you, I can’t live without you…… Tsagaitawa yayi da tarin da yakeyi tare da kallon idonta itama idonta nakan nashi……  Taci gaba da fad’in Yarima sonda nake maka shine yasa na boye maka koni wacece, saboda ban son in rasaka…….  Yarima in zaka tuna nasha kuka ina son fad’ama wani abu, sometimes wani abu ya shigo koka katseni….  Yarima I try to tell you who I am but whenever I try to tell you wani abu saiya shigo, and habib yana fad’amin Indai na gaya maka gaskiyan who I am you will hate me and leave me…..  Yarima sonda nake maka bazan iya juran rashinka ba…..  Yarima Wlh Ina Sonka Ina Sonka, how I wish in bud’e maka zuciyata Kaga irin sonda nake maka…..  Yarima plz ka amshi kaddara ta karka juya min baya kaman yanda mahaifina yayi min, Wlh Yarima Idan ka juya min baya zan iya mutuwa……  Jin haka Yarima Aliyu yayi sauri ya rungumeta dukansu kuka Yarima hawaye ita kuma kuka mai sauti…….  Bariki tana rungume a jikin Yarima Aliyu ta Fara fad’in Yarima……..
Ni d’aya mahaifina ya haifa……
Nice y’ar mahaifina ta Farko kuma tun daka kaina bai k’ara samun haiyuwa ba, tun ina y’ar shekara Goma mum dina ta rasu, lokacin na shiga gararin rayuwa, gaba d’aya na tsani komai dake duniya .
Mahaifina babban malami ne a k’asa nan wanda kowa ya sanshi bama kasar nan ba harta kasashen duniya, mahaifina malami ne mai sani Sosai sannan d’an kasuwa ne wanda yayi fice Sunan mahaifina sheik musa monguno……  Dan maiduguri ne, sunyi auren soyayya da mahaifiyata tun a k’asar misra suka had’u lokacin sunje karatu mum dita y’ar Sokoto ce soyayya Mai karfi ya shiga har takai da aure…..  Tunda mum dina ta rasu mahaifina bai kara tunanin yin aure ba, shi yaci gaba da kula dani har Nayi hadda na sauke al’qur’ani da sauran littafai lokacin ina shekara shad’aya a duniya…..  Ina karatun boko komai nawa dad dina yake min tare da taimakon Mai aikin mum dina wata tsohuwa Wanda na dauketa kaman kakata nake kiranta da Ummaa, 
Dangin mahaifina sun dameshi akan ya k’ara aure, domin zamanshi haka bamai  yihuwa bane, ya nuna musu babu tsarin k’ara aure a ranshi, domin bai yarda yayi aure ya bada ri’kona wajan matar daya aura ba, domin yana matukar jin tausayi na, ya nuna musu Ummaa na kula dani baya bukatar ya auri wata mata, koda zaiyi aure yace saiya aurar dani shine zai samu nutsuwa……
Haka dai suka barshi Ina shekara shabiyar a duniya Ummaa ta rasu ????????, naji mutuwar Ummaa Ina tunanin Nafi jin Nata akan sanda naji mutuwar mum dina, har saida na kwanta a asibiti, a lokacin na k’ara yarda ba mutuwa akema kuka ba, shakuwa ce da Sabo akema kuka, haka na k’ara fad’awa cikin gararin rayuwa tare da kadaici, mahaifina yana matukar jin tausayina Sosai…..
Bayan rasuwan Ummaa family din dad dina suka k’ara taso mishi da maganan aure, wannan karan basu mishi da wasa ba, kusan duka y’an uwanshi suka had’u harda mamanshi wato kakata tunda mahaifinshi ya dad’e da rasuwa, dole yasa ya amince ganin yanda suka nuna fishinsu akan ya k’ara aure……..  Wata y’ar uwarshi aka aura Mai Mai suna Falmata wacce mijinta ya rasu ya bar mata yara biyu Mata, ganin abbana yana da kud’i yasa akace zai iya ri’ke yaran dan haka tare aka kawota da yaran, gidan dad dina dake Abuja.
Falmata Tana nuna min so Sosai, bata Bari koda kud’a ya tabani, mahaifina yana jin dad’in hakan, sannan komai zai mana tare yake mana da Kananan yaranta, haka dai rayuwa taci gaba dad dina wata rana ya d’aukeni mukaje bank aka bud’emin account, gaba d’aya kud’in da mum dina ta bari aka samin kud’i masu uban yawa a lokacin kusan 20mil banda kadarori data bari tare da gidan gona Wanda kullum cikin samun kud’i ake, komai na mum dina dad dina yace cikin account dina za’a dinga sawa…. Na nuna ma dad dina daya Bari a wajanshi amma yace a’a in ri’ke hakki nane…….. Mahaifina yana nuna min tsantsar so Sosai har baya iya boye son da yakemin gaban kowa kullum magananshi ni tare da fad’in irin tausayi na da yake ji………  Dad dina yana yawan zuwa gari gari wa’azi da kasashe, ganin matarshi Tana kula dani yasa ya yarda yake tafiya yabar mata ni….
Lokacin da nake shekara Goma sha bakwai komai nawa Ya fito, kyau diri Kirjina komai nawa dai tubarkallah, Falmata duk kawayenta kana kallonsu zaka gane y’an duniya ne, sannan basa zuwa gidan sai dad dina baya k’asar……..
Wata rana Ina d’aki na fito daka wanka daka ni sai towel, ina zaune ina shafa mai saiga Falmata ta shigo, da sauri na tashi Ina kokarin in d’auko abu in rufe jikina A Kai rashin Sa’a towel din ya fad’i, gaba d’aya idon Falmata na kaina, da sauri na shige towel na rufe Ina kuka domin naji kunya Sosai ranan
Ranan dai a d’aki na wuni banko le’ko ba
Washegari na fito da yake lokacin ina zana waec kuma ranan shine paper na karshe na fito zani skul cikin jin kunya, saiga Falmata tazo ta ri’ke min hannu tare da fad’in haba zainab, mai yasa tun jiya kika k’i fitowa nifa mamanki ce kiyi hakuri dana shigo ba tare dayi miki nocking ba, tunda ta ri’ke min hannu sai wani murmurzawa take kaman filo ta ri’ke, ganin zanyi lati gashi tana ta wani shafa min hannu yasa nace ummi zanyi lati.
Murmushi tayi tare da fad’in muje in rakaki mota, har mota mukaje ta sani tare da fad’ama driver ya kaini a hankali
Tun daka ranan Indai Falmata zata min Abu saita tabani ban taba zarginta da wani abu ba, duk tunani na tanayi ne saboda in saki jiki da ita, domin tunda Abun nan ya faru nake jin kunyanta Sosai, haka zatai taja na da fira ni gashi ban cika son magana ba……
Wata rana dad dina yaje saudiya umra ,ina d’aki ina karanta wani hadith daka ni sai kayan bacci a jiki na, kawai Falmata ta fad’o d’akin  dama kwana biyu ban cika bari muna had’uwa ba inma mun had’u nesa nesa nake da ita domin ban son yanda take yawan tabani…..  Ganin ta shigo d’akin yasa na tashi tsaye domin taban tsoro irin kallon da take min…..  Nufoni tayi tana y’ar murmushi tare da fad’in baki bacci ba har yanzu?
D’an murmushi nayi tare da fad’in eh ummi.
Matsowa tayi gab dani tare da min wani irin kallo da yasa gabana ya fara fad’i….
Tace Zainab nazo ne muyi wata magana wacce nake fatan zaki amince min??
Cikin rawar baki nace eh ummi insha Allah
Shafamin fuska tayi tare da fad’in yauwa my daughter
D’an ja baya nayi kad’an
Murmushi tayi tare da matsowa kusa dani ta janyoni jikinta ta rungume har ina jiyo sautin ajiyan zuciyarta, a hankali tace Zainab plz ina son ni dake mu dinga biya ma juna bukata, Wlh sonki ya kamani dan Allah ki yarda kiban had’in Kai…..
Da sauri na fara kokarin tureta amma na kasa domin tayi min ru’ko Sosai, bakinta take kokarin kaiwa nawa ina kuka ina tureta har Allah yaban Sa’a na cije ta a hannu da sauri ta sakeni, na shige toilet na rufe, kuka nake Sosai tare da tsoro da mamaki, dama ummi tana yin mad’igo Innalillahi’wa inna ilaihirajiun, ranan na tsorata Sosai tare da k’ara jin tsoran duniya…..  Tunawa da irin azaban da Allah ya tanadar ma masu yin mad’igo sannan zamanin annabi ludu an kifa duniya saboda luwadi da mad’igo, yau shine ummi take aikatawa…… Tunawa tayi da sanda malaminsu yake musu wa’azi akan masu aikata mad’igo ko luwadi…… Inda yace
Mad’igo ko luwadi babban zunubi ne a musulunci, wanda za’a iya cewa Idan aka cire shirka, da kafirci to yana iya biyo baya…….
Sannan hukuncin wannan mummunan aikin luwadi ko mad’igo yana kusan dai daine da mutumin daya zagi Manzon Allah…..  Kuma Kun San hukuncin Wanda ya zagi Manzon Allah…..
Manzon Allah (S A W) yace
Mafi girman abunda yake jin tsioranshi akan Al’ummata shine aikin mutanan Annabi LUD….
mai nene aikin mutanan Annabi LUD??……   shine luwadi da mad’igo Allah ya tsare…..
A wani hadisi so uku ajere Manzon Allah yana tsinema Wanda yake aikata irin aikin mutanan Annabi LUD…..
Manzon Allah (S A W)  Yace….
ALLAH YA TSINEMA WANDA  YAKE  AIKATA IRIN AIKIN MUTANAN ANNABI LUD, ALLAH YA TSINEWA WANDA YAKE AIKATA IRIN AIKIN MUTANAN ANNABI LUD,  ALLAH YA TSINEMA WANDA YAKE AIKATA AIKIN IRIN MUTANAN ANNABI LUD
        Asara da tabewa ta gama tabbata akan mutumin da Manzon Allah ya jera Mai tsumuwa har guda uku akanshi.????????????
Sannan Manzon Allah yace….  Duk Wanda kuka samesu suna aikata irin aikin mutanan Annabi LUD to kukashe maiyi da wanda akeyi dashi
Sai dai a cikin hadisai ana samun rauni da wanda bai inganta ba……. 
Sannan malamin mu ya kara dacewa duk mai aikata luwadi ko mad’igo hukuncin shi Indai aka kamasu wasu sunce……..
A jefesu wasu kuma sunce a k’ona su, wasu kuma sunce a sami bene ginin gidan sama wanda yafi tsawo a jefo su aita musu haka har sai Sun mutu???????????????????? Wlh muji tsoran Allah, y’an mata da samari kunji wannan babban laifi ne wlh masuyi ku tuba ????????????????
Bariki kuka take Sosai tare da tsoran Falmata lallai Asara da tabewa ya tabbata akanta aikata lesbians, kuka take Sosai tare da burin Dad dinta ya dawo ta fad’a Mai……
MARYAM OBAM

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button