CikiLabaraiMagidanci

Bayan Sakin Matar Sa:; Wani Magidanci Ya ďirkawa Yarsa Ciki Har Sau Biyu Sabida Karfin Sha’awa

Wani mutumi a jihar Legas ya ɗirka wa ɗiyar cikinsa juna biyu, ya zubar sannan ya ƙara mata wani cikin karo na biyu.

Mahaifiyar yarinyar, wacce ta rabu da mutumin shekarun da suka shuɗe, ta fusata ta kai ƙorafinsa hannun yan sanda.

Kakakin yan sanda, Benjamin Hundeyin, ya ce tuni suka cafke wanda ake zargi kuma zasu gudanar da bincike.

Wani Magidanci mai sana’ar hannu ɗan kimanin shekara 44, Mustapha Abiodun, yanzu haka yana tsare a kurkukun yan san da dake Caji Ofis na Ikeja bisa zargin ɗirka wa yarsa ciki.

Yarinyar wacce aka ɓoye sunanta ta fara rayuwa tare ɗa mahaifinta a yankin Alagbado, jihar Legas bayan iyayen sun rabu kuma ta koma hannun mahaifin tana shekara 14.

Vanguard ta rahoto cewa tun bayan komawarta gidan Mahaifin shekara biyu da suka shuɗe, ya fara amfani da ita.

Bayanai sun nuna cewa lokacin da Mustapha ya fara lalata da ɗiyarsa ya bata hakuri bisa hujjar yana cikin Maye kuma ya ɗauki alƙawarin ba zai ƙara ba.

Amma hakan ba ta samu ba, alaƙar da ta shiga tsakanin su sai da ta yi sanadin ɗaukar cikin ɗiyar a watan Agusta, 2021, Lokacin da cikin ya cika wata huɗu Uban ya sa aka zubar da shi.

Bayan nasarar zubda cikin, Mutumin ya cigaba da holewarsa da cin zarafin yarinyar har ta sake samun ciki a karo na biyu.

A cewar wani maƙocin mutumin, Mustapha ya na da tsauri kan duk abinda ya shafi ɗiyarsa, baya barin tana harkokinta tare da mutanen Anguwa.

Yace idan ka cire lokacin da take zuwa makaranta da lokacin da take fita aiki, a koda yaushe suna tare da juna.

Yace:

“Ba mu san akwai wani abu dake faruwa tsakanin su ba har sai lokacin da muka fahimci ta samu canji a jikinta.”

Shin mahaifiyarta ta san abun da ke faruwa?

A cewar mahaifiyar yarinyar da abun ya faru a kanta:

“Tun tana wata uku na rabu da Mustapha, kuma tana tare da ni har zuwa shekara biyu baya lokacin da tace tana son ganin Ubanta kuma na haɗa su, daga nan ta koma hannunsa.”

“Makonnin da suke wuce na samu kiran gaggawa cewa na zo na ɗauke ‘yata. Lokacin da na iso Legas na tarar Mahaifin da yarinyar sun je Abeokuta wurin Jana’iza.”

“Da suka dawo na gano cewa yarinyar na dauke da juna biyu saboda haka na gaggauta sawo yan sanda cikin lamarin.”

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin hukumar yan sanda na Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce sun kama wanda ake zargin ranar 20 ga watan Maris, 2022 bayan ƙorafin da Uwar ta shigar.

Yace a halin yanzun jami’an sashin jinsi na gudanar da bincike kan lamarin kafin ɗaukar mataki.

Daga Hausa Legit

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button