BidiyoLabarai

Bidiyo:; Na Haifi Yara 4 Tare Da Yayana Munyi Aure Bansan Cewa Dan uwana Bane

wata mata ta ba da labarin yadda ta auri dan uwanta ba tare da sani ta ba.

Matar mai suna Domitila ta taso ne ba tare da ta san tana da dan uwa ba kuma ba ta ma san iyayenta ko kamanninsu ba.

Ta tafi birni tana budurwa neman aiki sannan ta hadu da yayanta sai suka fara soyayya daga nan sukayi aure ba tare da sun san su yan uwa ne ba Legitng ta rawaito.

Matar mai suna Domitila ta ce ta auri dan uwanta ne ba tare da saninta ba saboda bata taba sanin tana da dan uwa ba.

Kamar yadda labarin ya nuna, iyayensu sun yi watsi da su tun suna ƙanana kuma suka watsu a wurare daban-daban babu mai kula da su.

Sun haifi ‘ya’ya hudu

Bayan sunyi auren su haifi ’ya’ya huɗu kafin a gano tushen danginsu kuma an tabbatar iyayensu ɗaya ne.

Bayan gano hakan akan su yan uwa ne da minin nata jama’a sun yi wa Domitila saniyar ware saboda babu wanda ke son alaka da ita. ‘Ya’yanta duk sun yi kama da nakasassu kuma mutane a shirye suke suna nuna hakan a matsayin hujja.

Domitila ta kasa jurewa wannan abin kunyar, ta bar auren ta dauki ‘ya’yanta hudu suka zauna a cikin wani gida har sai da wata kungiya mai zaman kanta da aka fi sani da Giving Life Foundation ta same ta.

Gidauniyar ta siya mata sabon gida ta kuma bata gidan da  ita da ‘ya’yanta.

Afrimax English su suka daura bidiyon  akan shafin su na YouTube.

Ga bidiyon ku kallah:;

 

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button