BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL
BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL
“Kanki daya kuwa wacce mace na kawo gidan kin fara ko”
Mahfuz yace cikin dauriya numfashin sa na Neman daukewa
“Ai gani nan a waje wlh tallahi idona idonta.mahfuz sai na rabata da numfashinta.mahfuz”
Na katse wayar mahfuz yayi waje da sauri a daidai lokacin da ake buga kofar gidan
Hankali a tashe ya d’auka da gaske Lubnar ce hakane yasa yayi Kan Hadeeza aguje baiyi wata wata ba ya rike hannunta ta ya fara janta ya kaita daya d’akin ya tura ta bandakin daya d’akin nasu
“Mai haka mahfuz lafiya kuwa”?
“Shiii kiyi shiru Lubna ce ta dawo”
Cire hannunsa tayi daga bakinta tana “Toh sai me dan ta dawo ai ba wani Abu mukayi ba shine hankalinka ya tashi haka Mahfuz”
“Dan Allah kiyi shiru Hadeeza Ina zuwa karkiyi magana “
Yace tare da jawo kofar yayi waje da sauri
Lubna
Ina katse wayata Kiran makociyata na Kara shigowa wayata a daidai lokacin da na samu na tare abin hawa Ina dauka tace “gani a k’ofar gidan Ina kwankwasa wa”
“Ki taimaka min mmn Iman Ina hanya yanzu dan Allah idan har Kinga mace a gidana ki rikemin ita har sai nazo Dan Allah dan annabi wata kwartuwa yarinya ce take bibiyar mijina”
“Nidai Naga shigar mace banga fitowarta ba,ba lallai Kuma budurwar tasa bace kila bakuwa kikayi amma dai Ina kwankwasa k’ofar ba’a bud’e ba”
Katse wayar tayi adai dai lokacin da Mahfuz ya bud’e kofar ganin mmn Iman ce dan.ya Santa yasa shi sakin ajiyar zuciya take zuciyarsa ta bashi ita ta gayawa Lubna mace tazo gidan,kila taga shigar Hadeeza gidan.
Ko amsa gaisuwar da ta masa baiyi ba yace “Yanzu Mai amfanin abinda kika yi mace da cikinta kin daga mata hankali,daga gidan mu aka aiko min da abinci kanwata ce kuma tsabar munafirci shine Kika Kira lubna kika ce Mata mace tazo gidana dan Allah bakiji kunya ba da kika zo kina kwankwasa wa dan ki tabbatar toh kishigo kigani”
Yace mata a dan tsawace
Ja da baya mmn Iman tayi sam bataji dadin abinda lubna tayi mata ba
“Wlh ba ni nace Mata mace tazo ba ni muciya nazo ara ma wlh”
Tsaki Mahfuz yayi ya rufe k’ofar
Mmn Iman itama ta juya da sauri ta shige gidanta bakin ciki Kamar ya kasheta banda b’atar basira da rashin hankali irin na lubna name zata kira ma mahfuz da zuwan zatayi ai bai dace ta kira mahfuz ba.
Mahfuz kuwa Yana jikin kofa Yana ganin mmn Iman ta shige gida yayi sauri ya koma bandakin da Hadeeza take itama ta cika tayi fam,bata bari yayi magana ba ta fito daga bandakin ta fito palo ta d’auki Jakarta bata saurari mahfuz dake mata magana ba ta fice daga gidan tana zuba sauri mahfuz ya balain Kona Mata rai har mace yake tsoro haka Kamar wata uwarsa,har da kaita wani bandaki ya kulle wlh da ace ma tazo ba abinda zai hana ta fitowa ta ganta sai dai duk abinda zai faru ya faru,taya Mahfuz zai iya Kara aure Yana tsoron matarsa haka,yanzu Yana nufin ma yafi fifita matarsa akanta,duk wahalar nan da take sha akansa shine zai wani kaita bandaki ya b’oyeta sabida Yana tsoron kar matarsa ta ganta,shi daya Kamata ma ya fara gayawa matarsa tun yanzu akan aurenta zaiyi.
Da tsanin bakin ciki ta isa gida tana zuwa ta hau watsapp ta fara zanna Masa ta WhatsApp akan ta gaji da wanan kumbiya kumbiya idan har yasan ya isa da gidansa ba tsoron matarsa yake ba ya turo manya gidansu.
Mahfuz
Wani irin Ajiyar zuciya ya sauke daya ga Hadeeza ta bar gidan,shi baiga abin Jin haushi dan ya b’oyeta ba yanzu da lubna tazo ta ritsa ta mai zai ce Mata har ga Allah bai tab’a tunanin zata zo Masa har gida batare da ko tsoro ba,har mamakin confidence dinta yake,Koda ba wani Abu suke yi ba ai bai dace lubna tazo ta ga ya kawota har gida ba, duk wanan munafikar makociyar tasu ce ta jaza Masa Kuma sai ya rabata da Lubnar baiji dadin fushin da Hadeeza tayi ba ya Kamata ta fahimce shi.
Mahaukacin bugun da aka yiwa k’ofar yasa shi mik’ewa yayi waje ya ma riga da yasan lubnar ce sai daya je bakin k’ofa ya tuna bai d’auke basket din abincin ba
Yana bud’ewa lubnar ta Fada gidan tana hucci Mahfuz kuwa ya hade rai Yana “Lubna daga yau karki sake ki Kara min wanan haukar ke yanzu ko tararki akayi akace miki na kawo mace gidanan sai ki yarda kina nufin zargina kike”?
Ko ta kansa ban bi ba na ratsa gefensa nayi cikin gidan sai da na hau napep naji Kamar na rufe kaina da duka da nasani ban Kira shi a waya ba da tahowa kawai nayi da kila na ritsa Yar iskar yarinya,ai nasan dole ma kafin na dawo yasa ta gudu zuciyata ko gezau batayi ba na yarda dari bisa dari itace ta biyoshi har gida dan taga bana Nan,
Basket din abincin dana gani ya tsakiyar palon ya Kara tabbatar min da zargina abinci ta kawowa mahfuz har gidan Aurena,kila ma har iskanci sun yi,dandaga muryar ta da naji da goyata da tace ayi nasan yarinya Yar duniya ce Yar iska
Basket din na d’auka a daidai lokacin da Mahfuz ya shigo Yana cigaba da bambamin fadan zargin sa da nakeyi.
“Mahfuz yanzu dan bana Nan shine zata kawo maka abinci har gida”?
“Lubna Nagaji da wanan halin naki ni nace Miki macece ta kawo min abinci tunda kika tafi kabiru abokina yasa ake kawo min abinci wai wanan wane irin Hali Kika tsiro dashi ne?kishi hauka ne”?
Ni kadai nasan halin da nake ciki jikina har rawa yake mahfuz na san sakamin hawan jini, palona na fara karewa kallo Ina ganin kamar Zan iya ganinta ma a cikin gidan,
Ban bi ta kan masifar da yake ba na Mik’e da basket din a hannuna na Shiga dakina tamkar zan ganta a ciki Koda na Shiga ciki ma har karkashin gado na tsugunna na duba na kurawa gadona Ido naga ko an kwanta a akai shigowar mahfuz d’akin bai hanani cigaba da dube dubena ba Inda yaja wani dogon tsaki ya nufi wajen kayansa ya fara zurawa
Na zauna a gefen gadon na zuba Masa Ido hawaye na zubo min
“Mahfuz mai na maka dana cancanci haka daga wajenka, mahfuz ko aure zakayi bai Kamata ka kawo budurwar ka har cikin gidanan tazo ta gane min sirrina ba,mahfuz ni nasan ba rageka da komai ba Ina iya kokarina dan naga na faranta maka rai, a yanzu da nake d’auke da cikinka bai Kamata ka daga min hankali ba,wlh Tallahi budurwar ka tazo gidanan,mahfuz palona kamshin turare yake na daban da nida Kai mun San bamu irin wanan turaren har yanzu bamu yi shekara biyu da Aure ba,mahfuz mai kake nema a wajen wata da bani dashi,wlh tallahi yarinya da ta san Mai takeyi bazata ringa dafa maka abinci ba sabida tasan kana da aure, mahfuz bansan yarinya nan ba amma na mugun tsanarta mahfuz na yarda idan ma auren zaka Kara ka kara ka auri koma wacce Banda tsinanniyar yarinya nan da har dan bana nan zata biyoka har gida duk halin da kake ciki da ita nasani mahfuz magana ce kawai banayi,haka zamu kwanta dakai ka fita ka barni kaje kana waya da ita daddare wane irin kallo kake so tayimin shashasha ko wacce bata da matsayi a wajen mijinta?namiji shi yake fara siyawa matarsa mutunci da daraja a wajen budurwarsa,idan har kana min haka kana tunani ko Allah ya kaddara aurenka da ita bazata balain rainani ta ringa min gori ba,Kai kana tunanin idan ka auro mace irin wanan da bata damu da kana da Mata duk abinda ta ga dama shi zatayi da muyi fada da Kar muyi fada ba abinda ya dameta har kana tunanin zamu zauna lafiya idan ka aurota”.
“Hmm Ke dai kin d’auko wani banzan halin da bansanki dashi ba ni nace miki Ina neman aure ne,ai ko budurwa ma zan kula kinsan dai ba haramun bane Allah ya hallata Mana mu Kara auren ballantana ni bakiji a bakina nace Miki Zan Kara aure ba,amma tunda kin dorawa kanki balain kishi har dasu zargi ke Kika jiyo kizo muje na maidaki gida”