DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVEL

DEEN MARSHALL_
Mamuhgee

ZAFAFA BIYAR 🔥🔥
So Da Zuciya
Miss xoxo
Halin Girma
Hafsat Rano
Dabi’ar Zuciya
Safiyya huguma
Takun Saka
Billyn Abdul
Deen Marshal
Mamuhgee

Pay @08184017082 Or 09134848107

1

BismillahirRahmanir-Raheem

Ahankali ta dago kanta dake ‘dan Sara Mata ta kalli kofar office din nata da aka kwankwasa batareda ta motsaba ta dauke idonta akan kofar tana sake boyayyan numfashin dake bayyanarda qosawarta da halin ABBAS LAMIDO sbd ko ba’a fada ba tasan koba shi bane to koma waye to al’amarine daya shafi sunan Abaas aciki.
Turo kofar akai tareda shigowa ko Bata dagoba Jin takun takalma yasa ta fahimci Sarah ce Dan Haka ta sake lumshe ido tana dago Kai ahankali tareda dauke hannunta daga kan aikin datakeyi a laptop ta aje gefe tareda gyara zama ta Kai hannu ta dauki ruwan data fitar a fridge tun dazu sbd su huce daga sanyi ta bude robar ruwan Tasha kusan rabi ta ajiye sauran tana cewa”

Sarah akwai wani abune?

Sai alokacin Sarah ta matso ta zauna kan kejerar hutawar dake kallon wadda  NAJMA  ke zaune tana jiran abinda zata fada,
Saidata Dan sauke numfashi itama kafin Kai tsaye tace”

Naj dazu kafin isowarki zuwan chairman Abaas biyu office dinnan Kuma Banga alamar lafiyaba a yanayinsa
Zan iya cewa dai yanayin da aka Sabane.

Sai alokacin NAJMA ABDULLAHI BELA ta dago da fararen idanuwanta dasukai laushi da gajiya tareda damuwar Jin abinda aka fada din ta kalli Sarah tsawon lokaci kafin ta sauke nata numfashin itama ta bude Baki da muryarta me taushi dake kokarin boye damuwarta tace”

Meyene matsalar Abaas Kuma yanzu?

Cikeda kulawa Sarah tana kallonta tace”

A yanda nakega inaga bazai wuce akan maganar jiya bace da Dr Sa’id yazo gurinki sbd zuwansa biyu Ana cewa kunfita tareda Dr Sa’id din.

Sai alokacin ta tuno da zuwan Dr din jiya da fitar da sukai zuwa taron makarantar yaronsa a wata private school dake kusa bama nesa ba.
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana daukan wayarta Dan kiransa Dan kuwa ma wannan karon yayi kokarin rashin binta gida tun Daren jiyan yayi abinda ya Saba.

Ringing wayar ta ringa yi harta katse Bai daga ba ta sake saka Kiran Bai dagaba har lokacin
kusan Kira uku Tai Masa baya dagawa ta kashe wayar tareda ajewa gefenta ta waiwayo ta kalli Sarah tace”

Bai dagaba
Baya office dinsa ne?

Banajin yafita Dan ko kafin nashigo Naga wucewar secretary dinsa hanyar zuwa office dinsa.

Juyar da fararen idanuwanta tayi ta maidasu kan wayarta da tadau ringing taga sunan Hanifa ne akai ta lumshe idanu ahankali tana sauke ajiyar zuciya tareda Jin sanyi aranta sbd Hanifa Marshal Alfa Bata Bata lokaci komai kankantarsa batareda takirata ba idan taji wani Abu yafaru da ita.
Kallon Sarah tayi da alamar tambayar cewa”
Kinfada Mata yawon da Abaas yayi na nemana yanzu da safe kenan?

‘yar dariya Sarah tasaki tana miqewa ta nufi hanyar fita tana cewa”

Sorry ma’am itace takirani da kanta ta tambaya.

Ficewa tayi tareda rufo kofar office din har lokacin da sauran dariya akan fuskarta saidai ta baro jikin kofar sukai kusan Karo da Abaas daya qaraso office din sanye cikin suits ash dasukai Masa kyau matuka kasancewarsa kalar ruwan tarwada Kuma cikakken kyakkyawan namiji meji da lokaci da kuruciya da nera.

Da sauri Sarah ta matsa gefe tana sake sake fuska da tace”

Barka chairman.

Ko kallonta beyiba ya bude kofar office din dake daukeda sunan NAJMA BELA ajiki ya shige tareda rufo kofar.

Tana zaune a inda Sarah ta barta bakuma ta juyoba sbd tariga tagane shine yashigo Dan Haka saima Dan lumshe ido datayi Wanda yake tamkar dabi’a gareta.

Kureta yayi da kallo daga tsayen kyawunta da dabi’unta masu sanyi suke taruwa su sace zuciyar mutum wainda shima sune suke dawo dashi gareta Koda yace ya rabu da ita,
Duk neman matansa yakasa samun wadda tafi Masa Naj kyau da sanyin dabi’u tareda wani irin aji Wanda ko jinin sarauta zai shafa Mata lafiya
Daya samu da tuni ya rabu da Naj sbd gabaki daya tagama Cinna Masa hauka bayan yanada tarin mutunci da dukiyarda yake iya shimfida duk abinda yakeso Amma gashinan yaqare da aiki a ALFA’S sbd ita ‘yar  daba ‘yar kowaba face wadda ke amatsayin babbar Aminiya ga ‘yar Marshal alfa Wanda sbd hakan ne take anan din shikuma yafiso ko ruwa idan zatasha tafada Masa Amma duk yabi yazama wani zararre akanta Wanda abin ke matuqar Kona Masa Rai duk da yasan tana tsananin hkr da dauke ido akan abubuwan dayake Mata Amma shima duk son dayake Mata bazai zauna Yana zuba ido tana yanda takeso ba Dan gwara ta Saba ko bayan aurensu tasan dokarsa baya daukan reni.

Jin shirun yayi yawa yasa ta dago ahankali ta Dan kalli gefensa da idanuwanta ta bude Baki cikin muryarta me taushi da nutsuwa tace”

Akwai wani Abu ne?

Rintse ido yayi wani takaici na taso Masa ya budesu akanta tareda qarasa matsowa gabanta ya fige wayar hannunta ya dangwareta kan kejera da qarfi cikin bacin Rai yace”

Akaro da danban adadiba Ina sake tambayar meye asalin boyayyar alaqarki da wannan likitan sbd bazai yiyu ko yaushe nayi tambayar mu’amalarku kinamun shiru sbd bansan meyake bakiba Wanda Ni bazan iya bakin ba da kinkasa rabuwa dashi,
Kyanki kike rudarsa dashi?
Kokuwa wani abun ne Wanda bansaniba ni……

Kashesa tayi ta hanyar zuba Masa manyan idanuwanta farare dasukai jajir atake da zallar takaicin kalamansa da basuda mutantawa ko darajantata amatsayinta na wadda zai aura din.

Miqewa tayi tsayi tareda daukan wayarta ta batareda tace Masa ko kala ba ta nufi table din office din da Jakarta ke Kai ta dauka ko kallon inda yake bataiba ta nufi kofa ta bude ta fice tabarshi tsaye Yana bin bayanta da kallo zuciyarsa na Kuna Kamar zai cinnawa kansa wuta yakeji.

Tana fitowa Sarah ta taso daga kan table dinta na matsayinta na secretary dinta ta qaraso tun kafin Tai magana ta lura da yanayin Naj din Wanda tasan dama za’ai Haka indai Abaas ne Wanda kullum ne qaida sai sunyi fada da Naj da Abaas din duk da dai kullum fitinar da tashin hankalin na Abaas din ne.

Batareda ta kalletaba da murya me ‘dan nauyi tace”

Sarah ki tattara takardun Dana Bari a table da laptop Dina ki kawomun gida idan kintashi.

Ok Naj Allah yatsare hanya.

Tana saukowa qasan building din ta nufi gate zata fita tahau taxi sbd dama Abaas din yawanci ke daukota daga gida Kuma idan sun tashi ya maidata idan Kuma suna fada taxi take hawa wadda dama tafi hawanta shiyasa ma takeda me taxi dinta na musamman Wanda kiransa kawai takeyi yazo Dan kuwa ranaku daddayane basa samun matsala da Abaas Wanda take Jin wani lokacin Kamar zuciyarta zata Gaza bazata iya cigaba da hakuri tana hadiye halayen Abaas ba dan kuwa gabaki daya Babu inda sukai dace da juna dazasu iya rayuwar aure bayan aurenba,
Ta Yaya zata auri mutuminda baisan darajarta,mutuncinta,qimarta ba tareda mutunta alaqarsu,
Tariga tasani tsananin kyawuntane yasa Abaas yake son aurenta Dan tazama tasa abin ado agaresa Wanda Bata saniba ko tsananin zafin ransa da zafin kishinsa zai Bar kyan nata ta tsufa da abunta Dan ita shakkar aurensa yafara mamaye zuciyarta sbd a dukkanin halayensa Babu Wanda baya Bata mamaki.
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana sake shanye damuwarta Kamar yanda ta Saba akan al’amarin Dan kuwa fasa auran Abaas gareta babbar matsalace dazata sake sako Kai tsakaninta da mahaifiyarta dama Dada kakarta uwa uba Dattijo Wanda yake mijin mahaifiyarta Kuma tawainiyan mahaifinta daya auri mahaifiyarta bayan rasuwar mahaifinsu.
Fasa aurenta da Abaas idan tayi shine zai zama Karo na hudu biyar kenan Ana fasa aurenta…

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46Next page

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Enable Notifications OK No thanks