BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL
BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Ina da saurin sabo da mutum kamar na dade da saninta haka na hau janta da hira bamu tashi ba sai da aka Kira sallahr laasar.
Na nuna Mata d’akin bakin akan ta Shiga ciki tayi sallarta.
Nima na shige d’akina dan na canzawa Mimi Pampers dan bansamu tsarki ba tukunna Ina cikin sawa Mimi Pampers Kiran Mahfuz ya shigo wayata Ina dagawa yace “Ashe har Abdul ya tafi yanzu nan ya kirani Kuma kinsan dan wulakanci bai biyo ta office dina ba wlh sai na Masa rashin mutunci”
Murmushi na saki Ina “kunfi kusa kaima kasan bazai tafi batare da ya ganka ba kila anjima kaga ya dawo,tare yazo da wata bakuwa Wai zata yi wani program Yar yayarsa ta Lagos bansan bai fada ma ba sai daya zo tafiya Wai Idan ka dawo na fada maka”
“Wlh Abdul ya Raina ni yanzu nida gidana zai kawo min wata bai nemi izini a wajena ba”
“Kai Kam da rigima kake wlh yanzu dan Yar yayarsa zata zo tayi kwana biyu a gidanan shine sai ya nemi izininka”?
Tsaki yayi Yana “Zan Masa rashin mutunci ai sai mun hadu dashi tukunna”
Murmushi na sake yi nace “ba ruwana Ina daga gefe”
“Ina Mimi”?
Gata nan yanzu nan na canza Mata Pampers goyata zanyi na Shiga kitchen
Hira Muka dan Kara tabawa kad’an kafin ya kashe wayar na goya mimi na fito nayi kitchen banga ummi a palon ba nasan tana cikin d’akin kila hutawa take tunda Lagos ba nan ba duk da banga alamar gajiya a tare da ita ba kila jirgi suka hau dan su Abdul din nada rufin asiri.
Ina cikin kitchen din na jiyo muryar Mmn iman tana kwankwasa k’ofa.
Ajiye muciyar hannuna nayi naje na bud’e Mata k’ofar ta shigo da ledoji a hannunta ko bata fadamin ba nasan na menene kayan gyara ta kawo min dana bata sautinsa dan so nake na tsantsame kafin na samu tsarki.
“Ke Kaya masu zafi ta kawo wlh sai kinyo ciko”
Gefenta na zauna na fara duba kayan a daidai lokacin da ummi ta fito daga d’akin motsinta yasa muka dago muna kallonta nace “kinfito kenan da zan shigo nace ban sani ba ko baccin gajiya kike”
Murmushi tayi a daidai lokacin da ta karaso wajenmu ta zauna a kasan kafet tana “Aa idona biyu ai ba wani gajiya da nayi tunda jirgi muka biyo Ina wuni”
Ta gaida mmn iman ta amsa cikin sakin fuska tana “kice bakuwa kikayi”?
“Eee wlh tun daga Lagos tazo”
Na bawa mmn Iman amsa na cigaba da duba jarkokin tsumin data shigo dasu da dan bokitin da aka dafa min ciccibi a ciki.
Kice Abban Mimi zai Sha Dadi na kashewa mmn Iman Ido data dafe baki tana “lah bakida kunya fa agaban bakuwar kike badala ko dai matar aure ce”?
Sunkuyar da kai tayi da muka hada ido da ita dan ni banma San kallona take ba
Murmushi nayi Ina “ba matar Aure bace wlh Mai dan nayi wanan hirar a gabanta ai Yan matan suma yanzu sun San komai”
Na karashe Ina dariya a daidai lokacin da nake dandana wani zuma Nan ma na sake hada Ido da ita ta sunkuyar da Kai da sauri
Mmn Iman tace “nidai mallama ki bani cikon kudin dana ranta Miki”
“Har nawa Kika ranta min”?
“Dubu bakwai na cika Miki wlh”
“Kai dubu ashirin na baki fa”
“Kwarai kuwa ai kayanta masu kyau ne da tsada wlh tamkar budurwa Zaki koma duk Inda Kika saka kafarki bbn mimi na biye dake”
Washe baki nayi Ina “Zan baki kudinki idan na Kai shi duniyar can kila na baki fiye da Dubu bakwai din”
Tafawa muka yi da ita ta mik’e tana “naji ma kamar abincin da kika Dora na kauri bari naje Nima na dora nawa girkin na biye miki ba abinda zan zanyi.
Tayi hanyar waje nayi mata godiya tare da kwashe kayan da dan bokitin cicicibin nayi hanyar kitchen dan a kitchen nake ajiyar irin kayan nan sabida wani zubin mahfuz akwai dube dube,Ina zuwa bakin k’ofa naji muryar ummi tana “Aunty ba abinda zan kama miki a kitchen din”?
“Lah tuwone kawai zanyi ba abu Mai yawa ba inada Miya dama ngd ki saki jikinki dan Allah Nan ma gidane ki kunna tv kiyi kallo”
Ina daga kitchen din nake Mata maganar na fara k’ok’arin tuka tuwon.
Muryarta da naji a bakin k’ofa yasa na juya
“Bari na Kama miki wani Abu aunty ki kawo na tuka miki”
“Kai haba wlh ki barshi”
Dak’yar.na samu ta koma Palon na tuke tuwon na kwashe.
Na Kara gyara ciccibin da aka kawomin na dumama na juyo a plate na dauki tsumi daya da na zuba a fridge din kitchen na nufi palon.
Tana zaune wanan Karin a saman kujera tana latsa wayarta har yanzu da hijabinta a jikinta har kasa.
“Wai bakya Jin zafine ki cire hijabin naki ki Sha iska Mana dagani sai ke a gidan fa kin k’i sakin jikinki”
Murmushi tayi bata ce komai ba na kwantar da mimi akan kujera na zauna a kasan kafet na mik’ar da kafafuna sabida naji dadin cin cicibin.
Ban taba ci ba na dauka dadi ne dashi ai Ina kaiwa bakina naji daci daci na kwabe fuska Muka hada Ido da ita dama tunda zu Ina Jin idonta a kaina
Dak’yar na hadiye Ina “Kai kinji daci kuwa da kina da Aure da kinci kinji”
Murmushi ta sake yi wani zubin Ina da surutu na hau zuba “Kinsan mace sai da gyara idan baka dage kayi gyaran nan ba sai namiji ya fara k’ok’arin hango ta waje kuma idan mace ta haihu Salam take komawa dole sai ta zuba gyara sosai zata koma yanda take sai kinyi Aure zaki gane haka,Amma dai kin kusa shiga daga ciki ko”?
“Eee”
Washe baki nayi Ina “Masha Allah ansa Rana.kenan kice Muna da zuwa Lagos Shan biki dama ban taba zuwa ba Kinga ta silarki sai naje”
“Insha Allahu”
“Saura wata nawa”?
“Saura wata uku”
Masha Allah Allah ya nuna mana shima acan Lagos din yake”?
“Eee acan yake”
“Saurayine ko Mai Mata,kiyi hakuri Kinga Ina ta zuba miki tambayoyi”
“Lah ba komai wlh Mai Mata ne”
“Kash amma banji Miki Dadi ba auren mijin wata ai bashida wani dadi,ki more aure shine ki samu santalellen saurayi ki aura ku Sha soyayyar ku,kai amma na tausayawa wacce zakije ki tarar nasan tana nan zuciyarta kamar tayi bindiga kishiya ba dadi sam Allahu ya tsare mu da ita ya nisanci mazajen mu da tsinannun Yan matan Nan dake makale wa mazajen mutane,kiyi hakuri fa karki ce da ke nake wlh nima Ina da wata shegiya da ta makalewa mijina sai da nayi da gaske suka rabu matar saurayinki Allah ya bata hakuri da juriya kema dan Allah karki cutar da ita”
“Aunty ai har yan matan baa san ransu suke auren mai Mata ba sai dan kawai ya tsago a kaddararsu nima saurayi naso aura Allah baiyi ba toh ya zakayi da kaddara”
“Hakane Kam mudai Allah ya rabamu da mumunan kaddara”
Ji nayi nama kasa cin ciccibin hararowa nake ni zaa kawo yarinya irin ummi,satar kallonta nayi Muka hada Ido,ta sakar min murmushi ta sunkuyar da Kai Ni kuwa ban d’auke idona ba na zuba Mata Ido,doguwa ce mai zagayyen fuskan hancinta nada tsayi gashin girarta yakusa hadewa waje daya,tana da dan.manyan ido,da karamin baki,bata fiye duhu ba bata fiye haske ba,duk da banga kalar jikin nata ba,daga zaunen da take Ina iya hango tudun kirjinta indai ba ciko tayi ba tana da na fulani manya kiris ya rage ta shiga sahun masu kib’a indai kishiyar tata ba mai balain zafi bace lailai wanan zatayi saurin kwace shi,badan tace an sa Mata rana ba da gidanmu Zan kaita wlh bazan bari ma mahfuz ya ganta ba na ayyana a raina.
Kiraye kirayen sallah magriba yayi daidai da tsayuwar machine d’in mahfuz a k’ofar gida.
“Aikuwa ga maigidan ya dawo”
Mik’ewa tayi da sauri nace “A Ina zakije ki koma ki zauna idan ya shigo ku gaisa”
Komawa tayi ta zauna a kasan kafet ta sunkuyar da kanta sai Wasa take da zoben hannunta inasan yanda take da dan kunya.