BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL
BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Shigowar mahfuz da sallama yasa na m’ike Ina “oyoyo Abban Mimi”
Na karbe ledojin daya shigo dasu Ina ta mamakin ko dai kudi ya samu haka da yawa wanan uban leda haka.
Wajen da Mimi ke kwance ya nufa bai ko kalli b’arin da ummi take ba ya d’auki mimi a daidai lokacin da ummi ta Masa sannu da zuwa sai a lokacin ya kalleta ya amsa ya d’auke idonsa daga kallonta a daidai lokacin da ta mik’e ta nufi daya d’akin sai dana tabbatar da ta shige ciki nace “itace wacce Abdul ya kawo bakuwar tamu”
“Naganta takura Mana kawai yakeso yazo yayi dan rainin hankali”
Kasa yayi da murya ya matso kusa dani yana “Wai kina nufin a wancan d’akin zata zauna”?
“Emana da a Ina kakeso ta zauna”?
“Lallai bakida hankali,ga dakinmu ga d’akin da take ciki kinsan kuwa duk motsin da akayi a daki ana jiyowa”
“Kai jamaa toh Ina kakeso na kaita”?
“D’akin tsakar gida amma zamanta anan ai da takura gaskiya”
“Haba Mahfuz d’akin tsakar gida sai kace namiji taya zan sauketa a tsakar gida sai nake ganin kamar hakan bai dace ba ko Abdul ne yazo gidanan yaga na ajiyeta a tsakar gida zaiji ba dadi wlh”
“Wlh ba abinda ya shafeni nida gidana baza’a a zo a takura min ba a d’akin tsakar gida zata zauna na gama magana”
Ya fara k’ok’arin mik’ewa yanda ya had’e rai.yasa ban Kara magana ba na fara bude ledojin daya shigo dasu,gwanwanin Madara ne dasu bournvita har dasu cornflakes, siyayya sosai har dasu kifin gwangwani da balangu bredi mai yanka yanka mamaki yasa nace “A ina ka samo kudi haka mahfuz”
“Wlh wani kudi yau aka raba Mana shine nayo Mana siyayya”
Tunda na aure shi bai tab’a yo Mana irin wanan siyayyan ba, shiyasa mamaki rufeni farinciki Kuma ya gaza b’oyuwa a fuskata,dan dama ni mayyar cornflakes ce dan sacet nake siyowa
“Yeee nima na faso gari mun zama yan gayu Kai wanan bakuwar ta zo da goshi”
Bai kulani ba ya nufi daki Yana bari yaje yayi alwala
Cikin farinciki na kwashi kayan na Kai kitchen na hau jerawa a dan glass din dake kitchen din har dasu bama ya siyo Mana na kuwa ji dadi sosai.
Sai da na gama jerawa na dauki balangun na juye a plate na dibar wa ummi na saka mata tuwo mulmule biyu da Miya na dauki karamin exotic na hada a faranti gabad’aya na Kai Mata har daki a kwance na tarar da ita da alama daga wanka ta fito dan jikinta da lema ta saka karamin t shirt da bakin dogon skirt,sai da gabana ya Fadi dana ga surarta take na karbi shawarar mahfuz na in maidata d’akin tsakar gida tab.
Tana ganina ta rarumo hijabi tasa ta tareni tare da karbar farantin hannuna tana “Sannu Aunty”
“Yauwa nace Mata cikin murmushi Ina ga abincin ki nan idan kin gama ci zanzo na Kai ki d’akin can Kamar sai kinfi sakewa acan”
“Toh Aunty ngd da dawainiya”
“Lah ba komai na sakar mata murmushi na fito daga d’akin.
Na Shiga nawa mimi ce kawai a kwance da alama mahfuz ya fita massallaci.
Wanka na Shiga dan tuni na watsar da wankan jego na koma normal wanka.
Ina fitowa daga bandaki yayi daidai da shigowar mahfuz bai d’auke idonsa akaina ba ya zuba min Ido
Nida kayana nasan hali, ya matsu yaga Ina sallah
“Mallama Wai har yanzu shiru nafara gajiya fa”
“Tab kwana ashirin kawai da haihuwa sai nayi arbain fa”
“Wlh baki isa ba tab so kike na mutu kenan ya zauna a gefen gado,na gama shafe shafena na saka kayan shan iska.
Ina sai kayi sallah zamuci abinci ko na zubo yanzu”?
Bari ayi sallah Isha Kar nazo na kasa tafiya massallaci.
“Tom mu tafi Palo mu zauna”
Na dauki Mimi nayi gaba ya biyoni a baya.
A Palo muka zauna Muna kallo muna tab’a hira Yana latsa wayarsa hankalinsa dai Yana Kan wayar gabad’aya.
Sai ni kedai ke zuba surutuna har aka Kira sallah Isha ya fita massallaci bai dawo gidan ba sai wajen tara daga zuwa massallaci abincin ma da na jera Mana ya hucce tuni na cika nayi fam zuciyata ta fara rayamin kodai zance yaje take naji hankalina ya tashi,Ina tsoron tsinaniyar yarinya nan Mai nacin tsiya ce ta dawo rayuwar mijina wayata na d’auko dan na kirashi sai gashi ya shigo,da carbinsa a hannu da jalabiyar sa.
“Daga zuwa massallaci abban Mimi”?
Ina k’ofar gida wlh da Hamisu muke ta hira da kin leko zaki ganmu ai
Sai a lokacin hankalina ya kwanta
Muna cikin cin abincin Muka ji motsin bud’e k’ofar d’akin sai ga ummi ta fito da dogon hijabinta har kasa mahfuz ko kad’an bai dago ba Ina k’ok’arin Magana tace “Aunty dama bacci nakeji shine nace ko Zaki nunamin d’akin”?
Mik’ewa nayi Ina sude hannuna nace “eee zomuje nama dauka kinyi baccin ne wlh’
Nayi gaba tana bina a baya har muka fice daga palon,dama d’akin duk da baa kwana a ciki Ina yawan gyarawa Ina Kuma turarawa sai dai ba bandaki a ciki, bandakin a tsakar gida yake idan nayi baki da bandakin tsakar gidan suke amfani ,Yan uwa ke Shiga bandakin cikin daki.
Muna Shiga d’akin nace “dafatan d’akin ya Miki”?
Kai sosai ma wlh yayi aunty ngd Allah yasaka da alheri”
“Lah ba komai ai an Zama daya sai dai nace sai dasafe kenan”
“Toh aunty sai da safe a shafa min Kan Mimi”
Da murmushi na amsa Mata na fito daga d’akin.
Sai da muka gama cin abincin na kwashe komai na Kai kitchen na dawo na tarar da mahfuz na latse latse a wayarsa.
Nima wayata na d’auko na hau latsawa Ina chatting Ina kallo kafin goma naji bacci ya fara k’ok’arin daukana.
Hakane yasa na kashe data na kalli mahfuz daya danke wayar sa da hannu biyu nace “Tom nidai bacci nakeji zanje na kwanta”
“Kije kiyi kwanciyar ki dan ni ba bacci nake ji ba ko na biki daki ciwon maran zaki sani a banza nidai na fara gajiya fa tam”
“Kazo muje mu kwanta na maka tausa wlh Zan maka dabaru”
“Naki fa kibar ni na cigaba da hira da abokina”
Ya hasko min fuskar wayarsa Inda naga sunan Abdul din da Abokina
“Ai shikenan sai ka shigo”
Bai bani amsa ba Ina shiga ciki na canza kayan jikina zuwa na bacci Ina kwanciya bacci yayi awon gaba dani bansan lokacin da ya shigo ba.
Washegari da wuri na tashi dan na hada breakfast dan mahfuz da wuri yake fita.
Ina cikin soya dankali naji sallamar ummi.
Na amsa Mata daga kitchen ina mamakin me ya sa ta tashi da wuri haka.
Har kitchen tazo ta sameni muka gaisa da ita Ina satar kallonta Ina San yanda take shigar hijabi har kasa da alama tana da kamun Kai
“Aunty Ina tsintsiya nayi shara”?
“Ummi dan Allah koma kiyi kwanciyarki dan kawai ki tayani aiki Kika taso”
“Dan Allah karki hanani tun jiya nakeso na tayaki kina hanani” karfe Tara zanje wajen da zamuyi program din shiyasa na tashi da wuri”
Duk yanda naso hanata ki tayi akan dole na nuna Mata wajen da tsintsiya yake ta d’auko ta fara share palon.
Har tsakar gidan naji tana sharewa.
Sai da ta gama ta Kara shigowa da bokitin mopping da abin mopping din tana cikin mopping mahfuz ya fito daga d’aki cikin shigar suit sai kamshin turare yake.
Adaidai lokacin da Nima na fito da farantin abincin karyawarsa.
Gaisuwar ummi ya amsa ba yabo ba fallasa ya tambayeta ya bakunta ta sunkuyar da Kai tana murmushi nidai idona nakanta atoh karta sake ta kallarmin miji ganin na ajiye farantin a gabansa yasa ta ajiye abin mopping din tana “idan ya gama na dawo na karasa”
Hankalinta na Kara gani,dan naga tana nesa nesa da mijina haka nakeso shima mijina ya iya tsare gida.
“Mai kike murmushi ke kadai”?
Tambayar da mahfuz ya jefomun kenan
“Wlh yarinya nan nada hankali mahfuz da gani ta samu tarbiyya sosai duk da a Lagos take zaune”