BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BM

Page 13

Mummy da mmn Iman ne Suka bini aguje suka rikeni ta baya.

Na saka ihu Ina “ku cikani na kashe shi dan Allah ku cikani”

Mummy ta sakeni ta dawo ta gabana ta kwasheni da mari tana hucci

“Dama haka kike Lubna Ashe bakida hankali kishi hauka ne”?

“Aikuwa ga kishi nan ya sakata hauka ta zama Yar dabba kila har shaye shaye tanayi dan idan ba shaye shaye tayi ba,ba yanda zata zo ta samu Yar mutane ta kulle ta ringa dirmar ta Kai dalla shashasha lusari zoka wuce ka d’auko Yar mutane mu kaita asibiti Kuma wlh a yanzu zaka saketa ka gama aurenta”

Ammi tacewa mahfuz daya tsaya a bakin k’ofa Yana zare Ido,shi kawai na zubawa Ido Ina kallonsa,kallonsa da nake ya Kara tunamin Abubuwan da yamin, kirjina Kamar an dora bullo sabida nauyin daya min da azabar tsanarsa rad’ad’in da hannuna yake yasa na d’auke kaina daga kallonsa na kalli tsakiyar hannuna dana Sha Jan kunshi da baki duk a san na burge namijin daya kawomin budurwarsa har gida ya daidaita ni da ita ko nace ya fifita ni akanta,tunda Abubuwan da ya mata ko rabinsa bai min ba, itama har kunshi ta masa ta Sha kitso,na tuna yanda ta fito da Yan dari bibiyu sak irin Wanda mahfuz yabani nata ma yafi nawa yawa tamin karyar a banki ta ciro take na sake tuna wasu Abubuwan da ya Kamata na nasan gaskiya lamarin,hakane yasa na m’ike Sam bajin ma Mai mummy da Ammi ke cewa ba

“Ina zakije”?

Naji muryar mahaifiyata a bayana duk sun dauka kila dakina zanyi naga alamar tsorona ma mmn Iman da mijinta suke ji,akwai mutane a tsakar gida,Ammi har lokacin bata fasa masifa ba tana “Bari na duba Yar mutane naga ko ta jawo Mana balai tunda wancan shashashan ya kasa zuwa”?

Ta shige bandakin ta rafka uban sallati kafin su ankara nima na shige dakin da gudu na fada bandakin a bakin k’ofa take hakane yasa na bangajeta dan da balain gudu na Shiga dan nasan mummy zata iya rikeni.

Flat tayi a kasa ta saki ihu na danna k’ofar na saka mukulli najiyo takunsu da ihu dan Ammi itama ihu ta saka tana “Shikenan ta hadamu waje daya zata kashemu Mahfuz”

Ta hau kwallawa mahfuz kira ko kallonta banyi ba na tsugunna a gaban Hadeeza dake kwance da alama ta fara fita a hayyacinta jini sai fita yake akanta

“tashi zaune”

“Bazan iya tashi ba Aunty kimin rai wlh jiri nakeji kaina kamar baa jikina ba Aunty kin karya min hannu Hajiya ki taimaka min ku kaini asibiti Zan mutu tace wa Ammi, Ammi kuwa mahfuz kawai take ihun Kira tana yazo ya cecesu a haukace nake.
Ban kalleta ba nacewa Hadeeza

“Kin dauka Wasa nake Miki ko”?

“Aaa Aunty”

Ta fara k’ok’arin mik’ewa zaune tana cije baki Ammi kuwa ihu kawai take tana Mahfuz yazo ya bude kofar zan kashe su sai k’ok’arin balla k’ofar suke, mahfuz na sallati mummy kuwa kuka ta fashe dashi,mmn Iman ma Ina Jin kukanta”

“Damka na kaiwa hannunta da yafi kumbura ta saka ihu”

Nace “Kudin kunshi da kitson nan mahfuz ne ya baki ko”?

“Ee Aunty shi yabani wlh shi yabani dubu Ashirin”

Na cije lebbena

A ranar daya baki kin bashi kanki kenan”?

“Eee Aunty shekaran jiya ne a ranar ya fara sanina”

Murmushin takaici nayi dan Ammi sakin baki tayi tana kallonta na watsa Mata harara
Na Kara kallon Hadeeza dake sallati tana juya Kai dan jinin sosai yake fita a jikinta nasan dole ma a kwantar da ita a asibiti

A gaban ta na ringa hada kayan da nake so nayi amfani dasu dan na farantawa mahfuz kila tama sha wasu bansani ba tunda tana shiga kitchen din Kai tsaye Kuma a Fridge yake take na tuna tsumin dana Sha Mai daci

“Ke Kika zuba min abu
Mai daci a tsumina ko”?

Na Kara matse hannun ta saka ihu tana “eee Aunty shanyewa nayi na musanya Miki da abu Mai daci,na Sha zumar ma dayawa dan Allah Aunty ki cika min hannu zan mutu”

Zanso ta mutun a lokacin data ce ita ta shanye min tsumin dana kashewa kudi,nida siya ita da amfani dashi dan ta jiyar da mahfuz dadi anya na tab’a ganin Mai karfin halin Hadeeza kuwa,sai a yanzu na tuno yanda take hararata a fakaice,har da shigowa dakina duk dan taga ya dakina yake.

Yanzu da ace ta zubamin guba a abinci naci fa dan duk Wanda zai iya abinda ta yi zata iya kisan Kai har da fasa min bokiti dan tagani da mahfuz.

Idan har shekaranjiya ya fara kwanciya da ita hakan na nufin jiya ma wankan tsarki yayi ya nemeta,yaji dadinta kenan ya koma mata na saki murmushi takaici hawaye masu zafi suka hau kwaranyo min

Banida nauyin bacci banida Jin bacci da wuri tunda tazo gidanan na fara bacci da wuri mai nauyin gaske har ta Kai idan mimi ta farka sai nayi dagaske nake iya bud’e idona

“Mai kuke min keda mahfuz nake bacci da wuri”?

Na matse hannunta da k’arfi

Wlh magani yake samiki dan kiyi bacci da wuri har yazo dakina ya tafi hannuna zai fita na Shiga uku

Maganarta ta dakeni,Ashe Mahfuz ne yake samin magani a exotic din da yake min tayinsa idan muna cin abinci Na runtse idona jikina da kirjina wani irin rawa yake

Na sakar Mata hannu a daidai lokacin da sukayi nassarar balla k’ofar, Mummy ta shigo da sauri tana shigowa ta rufeni da duka

Tana “Lubna ko dai dagaske shaye shaye kike kanki daya kuwa wanan wane irin azababben kishi ne daga mijinki ya kawo kanwar abokinsa gida sai ki nemi kasheta.

Ban bar zubar hawaye ba ina kallon mahaifiyata nace “Abinda yace miki kenan,Hadeeza ke kanwar abokin Mahfuz ce”?

Na jefawa Hadeeza tambaya da k’arfi ta bani amsa da sauri

“Aaa Aunty wlh ni budurwarsa ce”

Mahaifiyata wani irin dafe kirjinta tayi ta maimaita kalmar budurwa ban kalleta ba na fito daga bandakin mahfuz yayi sauri yayi baya,bana kaunar ganinsa a rayuwata na fito daga d’akin inajin mijin mmn Iman na “A gaskiya baka kyauta ba idan har hakane Mahfuz ya za’ayi ka kawo budurwar ka har gida kaci mutuncin matarka wlh baka kyauta ba har gidan Aurenka fa mahfuz”

“Kanwar abokina ce Hamisu ba budurwata bace tsorata ta tayi shiyasa ta Fadi haka,zarginmu take na rasa Mai ya hau Kan lubna daga na fita massallaci na dawo ta kulle k’ofar zata kasheta ya fada cikin rawar murya

Naso na juya inda akwai tabarya a hannuna ko muciya na jefa masa sanin ba komai a hannuna mahaifiyata na biye dani yasa ban juya ba,Koda na fita palon jiki a sanyaye mahaifiyata ta biyo bayana mmn Iman kuwa sai jijjiga Mimi take tana kallona.

“Ammi ta fito tana dafe kwankwaso tana na karyata,har lokacin mahfuz bayani yakewa mijin mmn Iman dake ta Masa fada ce Masa yake yazo ya taimaka Masa ya Kai Hadeeza asibiti kar ta karasa mutuwa,mijin mmn Iman yace haram baa motarsa ba ya dauka mahfuz mutum ne mai hankali da sanin darajar Aure Ashe haka yake ya fito daga d’akin a fusace yacewa mmn Iman tazo su wuce su tafi ya kalleni cikin tausayawa Yana “Kiyi hakuri Lubna wlh bai kyauta ba bai kyauta ba koma waye dole ya dauki mataki yaci mutuncin Aure ya fita a fusace.

Sai a lokacin kukan da nake dannewa ya kufcemin na rufe fuskata na fara kuka mahaifiyata ta tsugunna a gabana itama idonta cike da kwalla mmn Iman itama ta tsugunna a gefena ta fara k’ok’arin rike hannuna dake ta zubar jini naga tsumma a hannunta kila so take ta dauremin itama sai hawaye take tana rike hannuna na fusge a fusace cikin kuka ina “kinsan komai mmn Iman,kinsan budurwar sa ya kawo min cikin gida Baki taba fadamin ba Kika sa na Zama shashasha na ringa hidima da ita,Mmn Iman idan nice bazan miki haka ba”
Ban bari tayi magana ba na cigaba da rusa kuka itama kukan yaci karfinta dan har ga Allah taso ta fada mata a ranar da taga mahfuz ya tsaya nesa da gidan Hadeeza taje ta same shi ya dauketa suka tafi a ranar tsananin mamaki yasa ta kasa tabuka komai,anan ta Kara tabbatar da zargin da take akan Hadeeza ba dan Allah take zaune da lubna ba taso fada mata amma batasan ta hadata fada da mahfuz hakane yasa ta bata shawarar ta sakawa hadeezar ido ta daina sakar mata fuska.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button