BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL
BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL
Dakewa yayi ya mata martanin ita ta Masa laifi amma itace zata ce ya saketa
Kamshin turaren Hadeeza data ce yanayi da Jan bakin da tace Yana kwalar rigarsa yasa gabansa faduwa ya Kai hancinsa jikinsa ya kuwa shako kamshin turaren Hadeeza ya kuma ga jan bakin da bai san garin yaya ta shafa Masa ba duk wani kwarin gwiwar daya shigo dashi ya sace wani irin kunya ya lullube shi bazai yi saurin shiru ba ko yayane gwara ya Kare kansa
Hakane yasa ya yanko mata karya
Amma baiga alamar karyarsa ta Shiga ba hakane yasa ya yanke bata hakuri duk hakurin da ya ringa bata haka ta ringa botsarewa akan dole ya fito daga d’akin ya shige nashi d’akin duk hankalinsa a tashe, idan har baiyi dagaske ba zai iya rasa lubna bai Kuma shirya rabuwa da ita ba lubna ta riga da ta Zama Rabin jikinsa baisan Mai yasa baya iya danne kansa akan Hadeeza ba,Sam baiyi niyyar komawa Hadeeza ba tunda bashida niyyar aurenta zafin da lubna ta hada masa yasa ya kirata a waya gashi turaren da ta fesa ya tona Masa asiri ya zama dole ya Kira mahaifiyar lubna ya fada mata abinda ke faruwa ya Kare kansa
Haka yayi ta sake sake sallah asuba akan idonsa,sai a lokacin ya Shiga bandaki yayi wanka ya daura alwala ya fito a hankali wai Kar ma Lubna taji motsinsa.
Ana iddar da Sallah ya fito daga massallaci ya samu waje ya zauna ya Kira Aunty nurse a waya Yana Kira ta d’auka bayan ya gaisheta cikin marairaicewa ya hau bata labarin abinda ke faruwa a tsakaninsa da lubna ya hada rantswar shi bai hadu da Hadeeza ba tazo ta taimaka Masa ta bawa lubna Baki ya rantse ya rabu da Hadeeza.
Aunty nurse kuwa ranta ya balain b’aci da abinda lubna tayi inda ta bawa mahfuz hakuri akan tana nan zuwa”
Sai a lokacin mahfuz ya samu kwanciyar hankali ya koma gida karfe bakwai daidai sai ga sallamar Aunty nurse.
Mahfuz har kasa ya duka ya gaisheta yayi kasa da murya yana “Dan Allah mama banaso ki mata fada sosai so nake ki kwantar mata da hankali ta daina furta kalmar saki mutuwa nakeso ta rabamu mama,wlh Ina kaunarta bansan Mai takeso nayi ba na riga da nayi kuskure na Bata hakuri amma ta dage sai na saketa wlh na rabu da yarinya nan mama bansan Mai lubna take so na mata ba
“Jeka kiramin ita”
“Wlh tsoron zuwa d’akin nake mama”
A fusace Aunty nurse ta mike tana a wane daki take
Mahfuz yayi sauri ya nuna Mata ta nufi d’akin lubnar da k’arfi ta tura k’ofar tayi Ido biyu da lubna dake zaune akan sallaya idonta ya kumbura gefenta ga akwatin kayanta
Lubna
Nayi matukar ganin mummy da sassafe yanda ta had’e rai nasan Mahfuz ne ya kirata,banason yanda Mahfuz ke neman hadani da mahaifiyata
A hankali na Mik’e nayi waje Dan muna hada Ido ta juya ko gaisuwar da na mata bata amsa ba ta rufeni da fada har tana k’ok’arin kawomin duka,da wane zanji kuka kawai nake idan Ina k’ok’arin Magana sai ta tareni,a karshe sai ta saka kuka akan batasan Mai yasa nakeson dora Mata hawan jini ba idan na Kara yiwa mahfuz ba daidai ba bata yafe min ba idan na kashe Aurena Kar nazo Mata gida.
Bata tsaya taji ta bakina ba ta mike da sauri tayi waje mahfuz ya mike ya bita a baya……..
Page 21
A ganina mummy kawai ce zata iya gane halin da nake ciki mummy ta d'auka kishi ne yasa na kasa kwantar da hankalina,bana jin ko aure mahfuz zai Kara ko yayi zai jefani a cikin tsananin bakin ciki haka, tsanar mahfuz nake ji a kowane sassa na jikina yanzu mummy ce kawai nake ganin idan nayiwa bayanin halin da nake ciki zata karfafa min gwiwa tace na hakura da aurensa tunda har ya kasa rabuwa da budurwarsa bazai daina fasikanci ba mummy da ta barni nayi mata bayani abinda ya faru amma Sam taki saurarana,Allah ne yasan kalar karyar da mahfuz ya mata,da har zata min Allah ya isa idan ban kyautata masa ba har yaushe iyaye zasu gane gaskiya su daina danne yayansu akan su zauna a gidajen mazajen su Idan basajin dadin auren,akwai cutuwa a zamana da mahfuz,dan nasan bazan iya Kara Masa biyayya ba,zan tayin abun da zan jawowa kaina zunubi ne.
Ina nan a zaune hawaye na zubo min har Mahfuz ya dawo palon Yana satar kallona,Allah yasan ko ganinsa bansan yi balle har mu zauna waje daya.
Mik’ewa nayi na nufi dakina Ina shiga ciki naji motsin sa a bayana gefen gadona na zauna na sunkuyar da kaina kasa har lokacin hawaye nake,da zalincin mahfuz zanji ko da hadani fadan da yayi da mahaifiyata.
“Lubna dan Allah kiyi hakuri wlh nasan na miki ba daidai ba,dan Allah ki tsaya mu fahimci juna ki cire komai a ranki insha Allahu bazaki Kara kamani da laifi irin haka ba,bana Jin dadin irin zaman da kikeso muyi wlh gwara ki hukuntani kowane irin hukuncine indai zamu koma yanda muke ada”
Mai zancewa mahfuz babu dan ba sabon kalma a maganarsa maimaici ne,kafin na dawo yamin kalamai da suka fi haka amma duk da haka bai fasa koma Mata ba ko dan daga kafa baiyi ba.
Mike’wa nayi na shige bandaki banasan ma jin muryarsa.
Har a yanzu kirjina zafi da ciwo yake min, wanka nayi dan naji sanyi a jikina bansani ba Yana bandakin ko baya nan, towel din dake rataye a bandakin na daura na fito ko ban kalli mudubi ba nasan fuskata a kumbure yake,Yana nan a zaune a gefen gadon ya dora mimi a cinyarsa ban nuna nasan Yana d’akin ba a nutse na shafa mai na zura doguwar riga na bar masa d’akin idan ya ajiye mimi sai na dauketa na mata wanka.
Tunda har ya dage bazai rabu dani ba bazai ji dadin Zama dani ba,kwanciya nayi a 3 seater dan karfe tara nake san Shiga kitchen,na samawa kaina abinda zanci tunda jiya yaki cin abincina na Sha alwashin bazan sake girki dashi ba.
Fitowarsa daga d’akin yasa na lumshe idona sai nake hango shi a kirjin Hadeeza,a jiya Abubuwan da yake min yake mata rudewar da yakeyi idan muna tarayya haka yakewa Hadeeza ba aurenta yayi ba jiya ma Allah ne yasan iya abinda sukayi ahaka mahfuz yakeso na share komai mu cigaba da Zama Kamar ba abinda ya faru.
Nayi saurin goge hawayen daya zubomin ta gefen idona bansani ba Yana palon ko baya palon dan idona a rufe yake,
Saukar numfashinsa naji a fuskata kafin na bud’e idona ya kamo bakina da nasa ya tsotse lebbena kafin na Mik’e ya hau ruwan cikina Yana “Dan Allah Lubnata ki taimaka min komai ya wuce wlh banasan ganinki cikin damuwa wlh tallahi zan rabu da Hadeeza ga wayata nan ki kirata duk abinda kika ga dama ki fada mata na miki alkawari bazan sake kulata ba”
So nake na saka ihu na tureshi huccin numfashinsa a jikina kamar garwashin wuta haka nake ji amma kalmar mummy ke dawo min na bata yafe min ba idan na kara Masa ba daidai ba hakane yasa na Kara runtse idona,shi kuwa hakan da yagani yasa ya cigaba da min magana Yana bin fuskata da sumba, na d’auka zan iya daurewa ya kashe kishinsa a kaina na riga da nasan jikina yake yiwa nasan abinda yake so ya samu kenan,bama zai iya hakurin a kwana biyu ba,ko zuwa lokacin zan daina Jin zafin da nakeji a kirjina,kansa kawai yasani bai damu da halin da nake ciki ba,bansan mai yasa idan har zai tabani sai na Tuno yanda na gansa da Hadeeza da Kuma yanda ya shigo jiya Yana kamshin turaren ta idan har yasan Ina da matsayi a wajensa ai ba yanda zaayi yaje wajenta jiya.
Wani iirn hankada na amsa adaidai lokacin da yake kokawa da wandona
A gigice ya taso yana “lubna karki min haka wlh idan na sama miki nutsuwa Zaki yafemin komai zai wuce a wajenki dan Allah kibari mu farantawa juna,ki barni na gwada miki kaunar da nake Miki wlh Zaki yafemin lubna”
Ya Kara yowa kaina gadan gadan
Sai a lokacin na dago idona na kalleshi “Mahfuz ka rabu dani idan kana so na sauko mu daidata dan Allah ka nisanceni har zuwa na samu nutsuwa ka riga da ka dage sai ka zauna dani bazaka bani takarda ta ba,kaje ka hadani da mummy Mahfuz har tana ikrarin bazata yafemin ba idan na maka ba daidai ba mahfuz kamin adalci kenan?mahfuz aure anayi ne dan Jin dadin,a yanzu bata ni kake ba ka samu wacce ta fini ka sakeni Mana ka koma gareta ka samu nutsuwa nima na samu sabida me kakeso kaga kayi ajalina ta hanyar doramin hawan jini,jiya da kamshin turaren ta.ka shigo gidanan”
“Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun lunbna dan Allah kicire komai a ranki idan kina tuna baya wlh bazaki iya yafemin ba karki manta Allah ma muna masa laifi mu nemi yafiyarsa ya yafe Mana haba lubna mai yasa kike da ruko haka dan Allah ki manta da duk abinda ya faru wlh na Miki alkawari na rabu da ita har abada”