BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL
BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL
“Wlh ban yarda ba kace matarka dai ta kwace wayarka ta kashe ta hana ka zuwa wajena na dade da sanin tsoranta kakeji ka sa na sha wahalar dafa maka abinci har konewa nayi a hannu”
“Ya salam dan Allah kiyi hakuri wlh ba da gangan naki zuwa ba ki hakura Mana karki sa na kasa bacci”
“Um um bazan hakura ba sai ka goyani Kuma wlh sai ka biyo gobe kacinye abincin Nan shine kawai zan hakura”
Dariya mahfuz ya kyalkyake dashi Yana “Angama sarauniyar mata idan na fara goyaki sai kin gaji gobe weekend bana fitowa da wuri wajen 10 zanzo a dumama min abincina,kinyi kitso da kunshin”?
“Emana har kwalliya nayi fa da sabon Kaya kak’i zuwa”
“Haha karki damu gobe idan nazo zan ma biya kudin kunshi da kitso amaryata kifita wajen haske na kiraki video call”
Iya abinda na iya jure ji kenan zuciyata kamar ta fado sabida tsananin bakin ciki mutumin daya gama tumurmusheni san ransa da tsohon cikina shine yanzu ya baroni a daki yake zuba soyayya da wata.
Wutar kishi kawai ke ruruwa a raina Ina Jin kamar na rufe kofar na kulle ya kwana a waje ko yaje wajenta ya kwana da bakin ciki da takaici ace kina iya k’ok’arinki akan ki kyautatawa namiji amma shi ba take yake ba zuciyarsa na wani wajen.
So nake na bar gurin amma.kafafuna sunki bani hadin kai,haka na zubawa mijina Ido,dake ta murmushi kamar an Masa bushara da gidan Aljanna har Mai nayi Masa haka,dame na rage shi da zai min irin wannan sakayyar bana ma iya gani sosai sabida hawayen daya cikemin idona.
Nasihar mahaifiyata kawai ke dawo min kaina da kyar na iya danne abinda nake ji da shaidan daya ke ingizani akan na kulle k’ofar ya kwana a waje ko naje na cakumu wuyan rigarsa na dadana Masa ashar.
Dak’yar na koma ciki Ina Shiga daki na kwanta naja bargo har saman kaina hawaye na cigaba da zubarmin zuciyata na suya,daga yanda Mahfuz ke magana da yarinya nan ba karamin so yake Mata ba har baya iya bacci idan baiji muryarta ba, wato shiyasa yanzu bai damu da yaci abincina ba? wacece yarinya nan,da take San kwace min miji,.har tana Masa shagwaba da sai ya goyata,tunani na tafi mai zurfi naga ko dai akwai ta inda na gaza har wnan yarinya ta dauke masa hankali Ina matarsa ta sunna ya baroni a daki ya fita waje dan kawai yayi waya da ita,tsafta, girki mai dadi, uwa uba iya gado,daga samun cikina na zama raguwa,Ina da kunya amma sabida kawai na faranta masa, duk da ni ba jarababiya bace har nemamsa nake da kaina,dan naji matan da suke neman miji da kansu daban suke a wajen mazajensu.
Ganin ya dade bai shigo ba yasa na daga kaina na kalli agogo karfe biyu saura minti goma,wasu matan na can rungume a kirjin mazajensu ni gani a kwance nikadai mijina na waje Yana Shan soyayya.
Motsin rufe k’ofar Palo yasa na d’ad’a Jan bargon kaina.
Ina jinsa ya shigo cikin sand’a har da lekani kafin ya kwanta a gefena a hankali ko minti goma baiyi da kwanciya ba naji Yana sakin munshari.
Haka na kwanta zuciyata kamar tayi bindiga har aka Kira sallah na Mik’e naje na daura alwala na tada Sallah.
Har na iddar bai tashi daga bacci ba ta Ina zai tashi ya kwana Yana waya.
Ko ganinsa bana so nayi hakane yasa na koma Palo, so nake na taushi zuciyata na daure Kar na nuna Masa komai a fuska nabi shawarar mahaifiyata dan tunda na taso duk shawarar da ta bani idan har nabi Ina ganin haske.
Yanda nakejin jikina nasan ko tsinke bazan iya dagawa ba nama wahalar da kaina dafa Masa abinci shi da zaije wajen budurwarsa yaci dumame.
Haka nayi kwanciya ta a dogon kujera wajen tara sai gashi ya fito Palo Yana “Uwar biyu shine yau baki tasheni nayi Sallah ba ko wlh bansan ya akayi na makara haka ba,A’a lubna lafiya kuwa ya Naga idonki a kumbure ko bakida lafiya”?
Duk maganar da yake ban daga kaina na kalleshi ba,ban tabbatar idan na Budi baki dan na masa magana ba magana zan gaya Masa ba hakane yasa ban magana ba na ja bakina na tsuke Kai kawai na gyada masa da Sunan banida lafiyar”
Kamar gaske ya nufoni da sauri ya zauna tare da jawoni jikinsa Yana tattab’a jikina.
Na janye na koma na kwanta sam bana San ganinsa duk abinan da yake na munafircine Yana da wacce yake so da kauna.
“Jiya Kuma kalau kika kwanta fa,Allah dai ya saukemin ke lafiya sannu kinji”
Yace tare da manna min kiss a goshi,nidai lumshe idona nayi, ba’a zagin miji amma na danna masa Ashar a zuciyata.
“Bari na dan gyara gidan mai zakici na dafa miki”?
Ganin ban bashi amsa ba yasa ya kara yimin sannu ya fita waje nabishi da mugun harara inajin Kamar na jawo shi na rufe shi da duka,sabida me zai nuna min kulawa alhalin Yana da wacce yake so da idan baiji muryarta ba baya iya bacci,a yanzu Kuma banida burin daya wuce na san wacce yarinya ce wanan da har ta d’auke masa hankali.
Bai dade ba ya dawo da leda a hannunsa daga kamshin nasan kosai ya siyo Ina balain san kosai da kunu,Yana cikin abincin dana fiso na karya dashi da safe kitchen ya wuce dama muna da garin kunu,da alama shi yake damawa.
Yanda yake nuna damuwarsa a kaina yasa wani bakin cikin Kara turnikeni duk abinan da yake min da wata a zuciyarsa.
Motsinsa da naji yasa nayi saurin maida idona na rufe Ina jinsa ya ajiye kofin daya damo kunun a ciki ya ajiye Yana “Lubna tashi ki karya kinji ga magungunan ki nan sai ki sha.
Ya jawo kafafuna kasa.
“Bana Jin cin komai”
“Ki daure mana kinsan baaso mace Mai ciki ta ringa wasa da abinci ko dan abin cikinta”
yace Yana kawo kosai bakina na d’auke kaina Ina “zanci anjima”
Tilasta min ya ringa yi naci nasan nacinsa akan dole nasaka hannu na fara cin kosai na karbe kofin a hannunsa dan bana San munafircin wani bani a baki.
Dadin daya min yasa na zage naci kosai baifi biyar ba na bari, na Sha maganguna na, ya dauki flasks din ya Kai kitchen,ya fito da tsintsiya ta share palon har da mopping mahfuz ba dai baya ba wajen aikin gida idan dai Yana nan, wanke wanke ne kawai bayamin.
Mai Mahfuz yake nema a wajen wata ya mace dan Allah mai na rage shi dashi daga kaina nayi na kalli agogo tara da rabi karfe goma sukayi da budurwarsa akan zaije wajenta bari naga ko zai hakura da fitar na ayyana a raina a daidai lokacin daya gama goge kayan kallon ya fara k’ok’arin nufar d’akin da a raina nasan wanka yakeso yayi ya fita.
“Kai mai zakaci”?
Na jefa mishi tambaya tare da zuba Masa Ido
“Ai zanje gida yanzu inaje can sai na karya na taho Miki da abincin rana ba sai kin wahalar da kanki wajen girki ba kiyi kwanciyarki ki huta kawai”
“Indai har dan abincin zaka fita yau weekends daya Kamata ka zauna a gida na samu kulawarka Zan daure na maka girkin ba sai kaje ko’ina ba”
“Ba iya dan na karya zan fita ba,Hajiya tace tana san ganina Yau bansan neman da take min ba”
Ko kunyar yanko karya baiyi ba na gyada kaina kawai ina Jin wani irin zafi a zuciyata bai kara cemin komai ba ya shige daki na fara tunanin.hanyar da zan bi na hana shi fita.
Tunanin daya darsu a raina yasa ni mikewa na nufi d’akin nawa Ina k’ok’arin.murda.kofar naji muryarsa Yana “Nan da minti goma Zaki gani wlh na shirya”
Murda k’ofar nayi na Shiga yaya saurin sauke wayar daga kunnesa ya cigaba da goge jikinsa murmushin da bai Kai har zuci ba na sakar Masa Ina “bari na saka Kaya nabika dama na kwana biyu banje gidan ba”
“Keda bakida lafiya Lubna Kika je can ma hayaniya kawai ta isheki kiyi kwanciyarki ki huta kawai bazan dade ba Zan dawo”