BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

BUDURWAR MIJINA COMPLETE HAUSA NOVEL

Mahfuz

Tafiyar lubna gida haihuwa ba karamin Dadi yaji ba dan yanzu kullum Yana gidansu Hadeeza anan yake cin na safe rana da dare,haka ya bude Mata bakin Aljihu.

Waya kuwa idan suka fara kamar bazasu rabu ba.

Duk da yakan ware lokacin da zaiyi waya da lubna gudun zargi.

A haka lubna ta samu sati biyu da komawa gida.

A yau daya kasance weekend ya Yanke ya dan wanke kayansa,ya gyara gidan inyaso yau yaje wa lubnar da ta dage akan yau a gidansu take so ya wuni ta ajiye Mai abinci yau ma zizilewa Hadeeza yake dan baya so tace masa yazo.

Ya gama wanki kenan Yana cikin gyara gidan sai ga Kiran Hadeeza a wayarsa.

Abin mopping din ya ajiye ya daga wayar “lek’o waje”

Shine kawai abinda tace tare da kashe wayar

Wayar yabi da kallo cikin mamaki kafin yayi wajen Yana lekawa waje ya hango ta a machine mai kafa uku taci kwalliya tayi kyau

Wajenta ya Karasa Yana “Kai Ina zakije haka wai dama kin san gidana”

Murmushi ta sakar Masa tana “idan inasan abu dagaske nakesan abun ka gama wankin ne ga abinci na kawo ma kasan bazan bari ka zauna da yunwa ba”

Mahfuz kasa ma magana yayi ta sauko da basket din abincin tana “Wai ko dai bakaji dadin zuwana bane”

Mahfuz keya ya sosa ya hau dube dube dan bayaso Yan unguwar suyi Masa wani fassarar,

“Kinsan Yan unguwar tamu suna da sa Ido”

“Tab Kai kake tsoron Yan unguwa ma muje”

Tace a daidai lokacin da ta bawa Mai machine d’in kudinsa

Mahfuz Kamar Wawa yayi gaba da sauri ya shige gidan.

Yana dan mamakin Hadeeza da tazo masa har gida.

Hadeeza kuwa ko a jikinta da biyu tazo gidan so take taga ya gidan ma mahfuz din yake ta dade tana Neman wanan damar daya ce Mata lubnar ta koma gida.

Suna Shiga palon ta ajiye basket din ta hau kalle kalle tana “Masha Allah gidan namu yayi kyau sai dai ya Mana kad’an nida Auntyna”

Murmushi ya sakar mata Yana “ki zauna na d’auko Miki ruwa ya nufi wajen da fridge ke,Yana d’auko ruwan yaga ta cire mayafi ta d’auko mopstick ta hau mopping….

LUBNA…

mg’s skincare

Shin Ina matan suke????️????️????️maza kuhanzarta kumatso kusa kuma kubani aran kunnuwanku domin sanin albishir dawannan shahararran company yazo muku dashi????????
Hakika tabbas duk macen data amsa sunanta bazataso afita b Koda da kwayar zarra domin hakane wannan shahararren company yazomuku da ingantattun hadaddun kayan gyaran jiki masu matukar gyara fata cikin kankanin lokaci batare da sunyima fata lahani ba domin kayan mg’s organic products ne bawai na bleaching ba zasu gyara ma mutum fatane yafiddomashi da ainihin natural beauty din mutum????hakika duk wacce batayi anfani da kayan mg’s b anbarta acan karshen bayama kuwa domin Koda sabulunsu kadai kuka dana fatanku seya fita dasauran mata ballentana Kuma kuyi anfani da gbdy beauty kit dinsu wohoho wani abun baa mgn sewanda yajaraba shine zai tabbatar❣️
Shin kinafama da
Pimples, black spot,sunburn, stretch mark,acne,black head, wrinkles,knuckles dama duk wani matsalan fata?
Shin fatanki tana tattarewane ko kinshafa cream yabatamiki jiki????
Shin inamasu cewa sunjaraba Basu dace b bi’iznillah sister’s duk Wanda yayi using mg’s sai godiya domin Koda iya herbal whitening black soap din kikayi anfani dashi zakiga ynd fatanki zaiyi clear Yana walwali jikinki zeyi fresh kina glowing my dear bare Kuma ace set dinne gbdy ????ga amare uk wnd yy using bridal set dinnan baya bukatar kowani gyaranjiki domin yadda jikinki zekoma yazarce misali DNT be left behind
Bridal kit:18k
Beauty kit:11k
Student package:7k
Herbal whitening soap:3k
Chat
08062991549
07046881166
07067210195
Call 08064532391
Facebook: mg’s skincare
Instagram:glow_with_mgs
Take note pls iya wadannan numbers dinne kawai zakusamu kyn mg’s babushi akasuwa????
Do you guys wanna achieve that milky skin that turns head wherever you go????
Then @mgs skincare gat you covered ????
Now is time to glow????
Pamper ur skin????
Shine like bride????????♀
Glow????♀️

???? tested nd trusted????
Guarantee

Sannan muna da hadaddun frames masu kyau gamai bukata yayi mgn 07046881166
BUDURWAR MIJINA

         *NA SADNAF*

E.W.F.

PAID BOOK

PAGE 6

Mahfuz duk kasa sakin jikinsa yayi Kamar Mara gaskiya sai yake Jin Kamar Lubna zata iya fadowa gidan.

Hadeeza kuwa ko a jikinta ta zage ta gama mopping ta fara goge kayan kallon sai ce mata yake ta barshi amma fir tak’i har sai da ta gama tsaf ta koma ta zauna tana “da akwai wuta har guga zan maka”

Murmushi ya sakar mata Yana “haba dai wankin ma bayarwa nake Mai wankin ne baya gari”

Tana k’ok’arin Magana wayarsa ta fara ringing gabansa ne ya Yanke ya fadi daya ga Lubna ke kiransa.

Mikewa yayi da sauri yayi hanyar d’aki ya kalli Hadeeza data kura Masa Ido Yana “Ina zuwa”

Yana shiga d’akin tayi sauri ta mik’e ta leka k’ofar da ta gani,ganin kitchen ne yasa ta tab’e baki ta leka daya d’akin da ke bud’e ta daga labulen nan ma ta tab’e baki tana “ko kayan kirki.ma Babu a gidan da sannu Zan shigo kifita insha Allahu”

Tayi sauri ta koma ta zauna ta cigaba da karewa palon kallo,Sam palon lubnar bai wani burgeta ba kayan lubnar ma duk ba masu tsada bane da zasu daga mata hankali.

Rigar jikinta ta kara gyarawa na fulaninta ya fito ta saman riga sosai,dan so take ta rikita mahfuz yayi ya fito ya aureta.

Da zata samu yanda take so da lubna ma kafin ta dawo daga haihuwa zata zo ta tarar da sunyi aure da mahfuz har ta tare,sai dai ta rasa mai yasa mahfuz ya kasa motsawa duk gani take tsoron lubna yake,so take ma taga hoton lubnar amma babu ko daya data gani a palon,wayar mahfuz Kuma akwai password a wajen hotunan,da alama shegiyar matarsa ce ta kirashi ya wani shige daki,take taji ranta ya fara b’aci ta had’e rai.

LUBNA

Kwalliya nayi sosai na gyara d’akin kanina dan nayi kewar mijina duk da yana zuwa ganina so nake yau idan yazo mu dan keb’e dashi na faranta masa rai dan nasan halin kayana hakuri kawai yake.

Da taimakon kanwata zainab na tuka Masa tuwon semo da miyar wake na jera duk a d’akin kanina.

Karfe biyu muka yi dashi akan zaizo idan ya gama wankin da yake.

Ganin biyu da rabi tayi baizo ba yasa na fara k’ok’arin kiransa a daidai lokacin da kiran makociyata ya shigo Mmn Iman”

Ina dauka tace “Lubna kin dawone”?

“Na dawo Ina”?

Shine tambayar da na mata cikin mamaki

“Ina nufin kin dawo gidanki ne”?

“Aaa Ina gidanmu mmn imam Mai zai dawo dani nida na zo gida haihuwa lafiya kuwa”

“Eee toh lafiya ba lafiya ba wata naga kamar ta Shiga gidanki sai na dauka ko kin dawone”

Kirjina wani irin bugawa yayi nace “wata kika.ga ta Shiga gidana wacce”

“Nima bansani ba wlh ko bakuwa kikayi batasan bakya nan ba”?

“Mmn Iman da idonki Kika ga mace ta shiga gidana Dan Allah jeki dubamin wacece”

Tana k’ok’arin Magana na katse wayar da sauri ko dai budurwa Mahfuz ce taje har gidana dan taga bana nan,? Yanzu mahfuz zai iya cin amanata?

Mikewa nayi da sauri hankalina ma na neman barin jikina sosai zuciyata ke sak’a min kila budurwar mijina ce taje har gidana,

Wayar Mahfuz na Kira jikina sai bari yake sai dube duben mayafi ko hijabi nake akwai tazara daga gidanmu zuwa gidana amma tabbas zanje gidana na indai har naga mace wlh tallahi sai na raba ta da numfashin ta,Yana daga wayar nace “Mahfuz kana Ina”?

“Gani a gida na shirya yanzu zan taho”

“mahfuz karya kakeyi wlh mace ka kawo min har cikin gida sabida kaga bana nan, yanzu cin fuska da cin amanar taka har ta Kai ka kawo min mace gidana Mahfuz innalillahi wa Inna ilaihi rajiun”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button