LabaraiMatar Aure

Yadda Wata ​Matar Aure ta kashe wani Boka A Kano

Daga Muhammad Inuwa Zariya

Wata matar aure ta kashe wani boka bayan dataje wajan shi neman taimako a tudun wadan Dan kade dake jihar kano.

Matar auren me suna safiya, taje wajan bokanne da niyyan ya taimaka mata da maganin da zata sama mijinta a abinci don yaci yakara sonta.”

Bugu da kari! Sai bokan yace ga matar taje bayan kwan biyu ta dawo, bayan tadawo sai ya dau magani ya bata bisani ya gayamata yadda zatayi amfani da shi.”

Rahoton ya cigaba da cewa! bayan da matar ta koma gida sai tayi amfani dashi, mijin yanacin abincin anan take mijin nata ya kama ciwo , lokaci kadan mijin yace ga garinku nan, “Hakan ya tabbatar cewa! Ashe maganin mutuwa ne yaba matar.”

Hakan ya kara bude wani sabon shafi ne, ganin yadda tun daga lokacin da bokan yaga matar yaji Yana sonta, shine ya bata maganin mutuwa a domin mijin yaci ya mutu”

Bayan kwana biyu Safiyya take shaidawa bokan mijin nata ya mutu, nan take bokan ya tayata jaje”

A dai-dai wannan lokacin, sai bokan ya bullu mata damaganar soyayya Kuma ya nuna mata auranta zaiyi sai safiya ta yarda.”

Ana nan dai Bayan sunyi aure sai shima ta barbada Mai raguwan maganin daya bata tayi amfani da shi ga dayan mijin nata.”

Safiyya ta zubawa boka maganin ne a cikin fura ya sha shima ya kama rashin lafiya na kwana biyu bisani shima ya mutu”

Daga baya wannan bayanan, duk daga bakin safiyya ne suka fito, inda take bayyanawa da kanta a dai-dai lokacin da duk abin duniya ya dameta.”

Wannan lamari ya farune a tudun wadan Dan kade ta jihar Kano.

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button