NOVELSUncategorized

RAINA KAMA (BOOK 3) 19

BOOK 3 ????????19
……………..Su Munaya sunyo nisa da tafiya danja ta tsaidasu, kamar daga sama suka fara jin harbi, y’an tsirarun mutane dake bisa titin suka fara guduwa, dan titin wajen baicika yawan mutaneba, kasancewar wajen tamkar sabuwar anguwane kuma gefen gari kad’an, itace hanya mai sauk’i da zata iya kaisu da wuri shiyyasa suka biyo…..

     Batakai k’arshen tunanintaba taji wani azababben zafi a damtsen hannunta, ko kad’an bataji k’arar wannan harbinba (dam inhar harbi zai shiga jikin mutum aishi bazaiji k’arar bindiga ba) kallon inda akayo Harbin Munaya tayi, glass d’in ya huda ga wani garjejen k’ato yayo wajen motar, a kid’ime ta kalli sarkin mota da hankalinsa shima yake a tashe, sai zufa yake yana waige-waigen ganin yanda police d’in suka fita sunason basu kariya.
    Cikin k’arfin hali Munaya race, “Sarkin mota, ka kar6i Camera d’in nan ka hanzarta kaita kotu, ya tabbatar min lokacin buk’atarta tayi, karka sanar masa komai harsai shari’arnan ta kammala dan ALALH, inason burinsa yacika koda ace zan rasa raina a yau, please karka damu sarkin mota jeka, maza jeka kar Mara imaninnan ya k’ara so.
     Badan sarkin mota yasoba ya kar6a ya fice da sauri cikin dabara, saboda Munaya tabashi tausayi, ga harbi ta samu, amma bata kanta takeba ta cikar burin mijinta takeyi.
    Fitar sarkin mota tayo dai-dai da isowar garjejen k’atonan, ya bud’e murfin motar yana fisgo Munaya waje, fad’owa tayi kanta ya bugu da kwalta sai jini kawai, tuni numfashinta yafara fita da k’yar, dishi-dishi take hango wani Na dukan Nuren da bakin bindiga yana k’ok’arin kare kansa da kiran sunanta yana mik’o hannu, amma ina, sun riga sunci k’arfinsa, idanunta suka lumshe a hankali, yayinda wasu hawaye masu zafi suka gangara ta gefen kumatun data fad’in, fuskarta d’auke da murmushin k’arfin hali.
     Nuren daketa kwala mata kira a rikice yana mik’o hannu, dukda dukansa da ake, ya zube a k’asa yana fashewa da kuka maiban tausayi da ambatar “please Munaya karki tafi kibarmin d’an uwa, ke wani yankin farin cikinsace mai matuk’ar girma ple……
    Shima baikai k’arshenba ya sulale k’asa saboda dukansa da sukayi a kai.
      Wani dake bincika camera d’in a motar ya juyo a fusace yana fad’in “babu camera d’in fa boss”.
       A rud’e Boss d’in dake tsaye gaban Munaya ya taka hannunta da mugun takalminsa yayo wajen, ko motsi kuwa batayiba alamar ruhinta yabar gangar jikinta.
     Ture yaron nasa yayi yafara lalube da kansa, hankalinsa yakai gaban motar. yace, “Ina driver!!? ”.
          Yanda yay maganar a rikice ya saka yaran rikicewa suka hau waige-waige, sarkin mota dayay nisa a gudu yana jiyo ihun ogan, saiya k’ara k’aimi.
    Wani yace, “gashi can zai gudu da camera d’in ”.
     Tuni suka rufoma sarkin mota baya a guje, shima yacigaba da gudu iya k’arfinsa. Cikin amincin ALLAH saiga wani mai mashin tamkar an jehoshi, ya tsaya yana fad’in “maza hau muje”.
       Sarkin mota ya haye, mashind’in nabarin wajen suna k’arasowa, Dutsuna suka d’auka suka dinga jifansu sarkin mota suna binsu da gudu, amma ALLAH bai basu nasaraba. Hardai ubangijin sammai ya kaisu court lafiya.
    Sai lokacin Na lura Ashe Ahmad ne yaron Alhaji Bana, ya kalli sarkin mota yana fad’in “Maza kakai, yanzu haka ita kawai ake jira, kasa nutsuwa a ranka kar boss ya fahimta balle yakasa nutsuwa a shari’ar shima, yanzu haka suma police zasuje su taimakesu, muma can zamu tafi da sauran y’an uwana”.
    Kai sarkin mota ya jinjina, ya k’arasa gaban k’ofar kotu yay knocking yana share hawaye da tausayin Galadima. Anzo an bud’e masa aka shiga dashi, dama camera d’in kawai ake jira.
       A can kuwa suma saiga Police an k’aro, wad’anda suke tare dasu Munaya su 6 ne kawai dama, gashi bawani isassun kayan aikine dasuba, bindugun hannunsu babu mai bullet, sun daki d’aya yasuma, d’aya kuma yasamu ya sulale domin kira yasanarma ogansu abinda ke faruwa, yayinda biyu suka gudu, biyune kawai a wajen, sukuma sunyi musu yawa y’an ta’addan.
    Isowar police d’in ta saka wasu a cikinsu yunk’urin guduwa, saidai ina, ALLAH yakan ara maka rana, randa kuma zai kamaka babu hanyar ku6ta, dukansu ram akayi dasu, dukda wasu sunso yin gardama, duk aka zubasu a mota, yayinda Ahmad yasake dawowa shi da Yassar tareda Ambulance, suma su Munaya da Nuren aka kwashesu????.
………………………….
         Tunda Galadima yaga sarkin mota ya kawo camera hankalinsa bai kwantaba, dakuma yaso had’a ido da Sarkin mota shi saiya kauda nashi, yak’i yarda su had’a idon…….
    Maganar Alk’ali ta katsema Galadima tunaninsa, yayinda yake bada Umarnin a bud’e camera d’in, takardune aciki guda uku, d’aya abbane ya rubutata yanama Galadima bayanin yanda akai camera tazo hannunsa, d’aya kuma sunayen dukkan wad’anda ke bibiyar sa akan camera d’in ne, d’aya kuma wadda mutumin farko d’an uwan baba Rabilu daya bada camera d’in ne ya rubuta ce.
   Ita kad’ai alk’ali yabada umarnin karantawa, yayinda masana keta k’ok’arin saita camera da TV dake kotu suma, Wanda Galadima ne ke k’ara sanar musu dukkan dabarun daya kamata suyi daga inda yake tsaye.
     Abinda takarda ta k’unsa shine…..
      Assalamu alaikum
       Sunana Habu, wannan takarda ina fatan ta iso agareku, ko yarima, ko gimbiya ko matar Sarki mahaifiyar su yarima, Ku duba wannan camera d’in,  duk yanda aka k’ulla faruwar ciwon mai martaba da wad’anda suka kulla suna a ciki, nidai nasan tawa ta k’are, dan tunda suka ganni ina d’oukar sirrinsu saisun kasheni, wata uku kenan ina 6oye-6oye, yaudai Na yanke shawarar fito fili Na baku koda hakan yana nufin zan mutu, dama can kwanana sun k’arene, koma basu nayi saisun kasheni, ballema bazan ta6a basu d’inba, ALLAH yabama mai martaba lafiya da tsawon kwana mai amfani, yakuma baku ikon hukunta wad’annan tsinannun masu jinin Fir’auna a jiki, wad’anda mulkine da tara duniya kawai a gabansu ba al’ummar k’asarsuba, duk yanda zakuyi karkubar la’anannnun nan yin mulkin al’umma, subasu cancanci zama shuwagabanniba.
      Bisalam.
     Kotufa tayi tsitt, ko tarin wani bakaji sai k’arar fanka, yayinda zufa tagama jik’e su Alhaji balala sharkaf, kallo d’aya zakai musu ka fahimci ruwafa ya k’arema d’an kada.
             Alk’ali baice komaiba, jira kawai yake camera ta daidaita ajikin TV kowa yagani, matsalar camera Ce irin ta da, shiyyasa take bada wahala, da k’yar dai cikin amincin ALLAH ta kawo, tofa, saidai kalar da take nunawa White and black, ga wani rawa-rawa da takeyi saboda ba nutse aka d’aukaba, kuma da alama ana yayyafine.
        Dagani wajen wani ke6antaccen wajene daba kowa ya isa shigaba, shikansa d’an jarida habu kota Yaya yayi hakan? ALLAH kad’ai ya Sani saishi, gashi bashida rai balle mu Sani.
          Mutanene da ak’alla sunkai 20 a wajen.
      Alhaji balala, Alhaji Mansur, Alhaji Lawan tanferu, Alhaji Bana, Alhaji Abdul-Naseer, Alhaji Labaran khacia, Timothy,  Hajia A’i, Victoria, Miracle, Alhaji Sageer, William, Josaya bamma, Kabiru Ibarheem, Alhaji Mamman, Waziri, Sai wani Sarki daba wani k’arfin ikone dashiba, yama rasu tuni, tun ciwon Abie babu dad’ewa, sai Mahaifin Gimbiya Zulfah uwargidan Sarki, shima sarkine mai fad’a aji, Sai mahaifin Mama Fulani????, sauran Biyun turawane.
     Duk suna zaune kowanne da kwalbar coca-cola a gabansa (sannan shinsa sai manya????).
       Alhaji Lawan tanderune ya mik’e yafara jawabi kamar haka.
       Masu girma saraki dake wannan waje, da bak’inmu (turawa) sai abokaina shak’ik’ai ina muku sallama gaba d’aya
     Duk suka amsa a tare. yaci gaba da fad’in,
      Muduka nan mun tarune akan mak’iyinmu guda d’aya, Wanda ya tare mana gabas ya tare mana yamma, hakama kudu da arewa, mun bishi ta lallami akan yabamu goyon bayan cikar burinmu amma yak’i, yana wulak’antamu saboda yaga ALLAH yabashi k’arfin iko da izzar mulki a hannu, a daren jiya mun yanke shawarar kasheshine kowa ya huta, amma yanzu mun fasa hakan, zamuyi masa abinda saiya gwammaci yazama gawa, dan zai rayune shiba mutumba Shiba butun butumiba, ahaka naman jikinsa zai ringa ru6ewa sashe-sashe, mukuma zuwa sannan mulkinnan dai dayake ganin bazai dafa mana muyiba ya dawo hannunmu, dan mungaji da mulkin soja hakannan, gashin kanmu muke buk’atar ci koya kukace?”
      Hannu suka d’aga suna fad’in eh hakane hakane.
       Alhaji Lawan tanderu yayi dariya yana gyara babbar rigarsa, ya d’akko wani ruwa a kwalba yana nuna musu, “kunga wannan itace gubar ruwan allurar da za’ai masa, ita cikin mintuna biyu zuwa biyar take fara tasiri koba haka kaceba Mike?”.
      Cikin turawa biyu dake tare dasu d’aya ya gyad’a kai yana murmushin mugunta.
    Gaba d’aya suka sanya tafi, raf! Raf! Raf!, saikuma suka koma tafawa da musabaha a junansu (irin sun samu cikar burinsu d’innan).
         Tanderu yacigaba da magana bakinsa a washe.
       “Wannan aiki ba kowane zai mana shiba sai wazirinsa, Munaso da asubahin yau kamasa wannan allura dakagani, inamai tabbatar maka inhar ya Idar da sallar to bazai shiga gida da kansaba”.
      Waziri mahaifin Harun ya kar6a yana washe baki tamkar gonar auduga, da fad’in “lallai nafi kowa farin ciki da samun wannan dama, domin kobabu komai zanyi maganin mak’iyina da kaina, daga yanzu sainaga da bakin dazai kuma cin zarafina da jifana da kalaman banida hali, toshi mai halin saiya cigaba da shukashi muda bamu dashi muyita girba munakaiwa gidanmu munaci….”.
      Gaba d’aya suka kwashe da dariya suna tafawa, a Na wannan dariyane Alhaji Bana idonsa yakai ga camera, alamun yaga habu kenan, ajiye k’aramin kofin silver dake hannunsa ya zuba coc yayi yana mik’ewa zumbur.
     Sauran suka fara tambayarsa mike faruwa?, tuni habu daya farga dasu ya shek’a da gudu. Daga nan ba’a sake nuno kowaba, sai gudu da habu yakeyi da hakkinsa, Camera d’in Na wani shuw-shuw harma aka bar ganin komai.
    
    Kwakwkwaran Motsi kowa ya kasayi acikin Court d’in, Galadima ya duk’ar dakai yana kallon k’asa hawaye Na zirara suna d’iga, hakama Abba Hayatuddin kuka yake saboda tausayin d’an uwansa da takaicin waziri daya kasa zama kusa dashi yanzun, ga takaicin wai harda kakansu Wanda ya haifi mahaifiyarsu, shin shikuma miye matsalarsa da d’an uwansa ne? Kenanma mama Fulani mahaifiyarsu itama tasan komai? Innalillahi wa inna’ilaihiraji’un, wannan wace iriyar masifacene hakan?.
      Alk’ali daya buga gudumarsa a sanyaye ya katse tunanin mutane da yawa dake cikin kotun, cikin sauke nannauyan numfashi yace, “yanzu babu tanderu a duniya, shin ko akwai mai wakiltar wannan group a yanzu?”.
     Su Alhaji balala da duk jikinsu yay lak’war kunya da nadama duk sun lullu6esu sukayi tsitt.
       A fusace cikin daka tsawa Alk’ali yace, “waishin! Ba’a jini bane?!!”.
      Jiki Na rawa Josaya bamma ya mik’e, tsufa sosai ya kamashi, danma akwai jin dad’i tattare dashi, ko a wancan lokacin dagani ya girmi tanderun ma gaba d’aya.
    
    Wani cikin ma’aikatan kotun yaje inda alk’ali yake suna magana k’us-k’us, komi yake fad’a masa oho, nagadai alk’ali yayi alamar a kawosu, wancan ya sakko, shikuma alk’ali ya maida hankalinsa ga Josaya bamma dake k’ok’arin shiga inda ake buk’atar ganinsa.
     Josaya Yaje inda ake tsayawa ya tsaya, Alk’ali ya kallesa cike da tsantsar tsana yace, “kotu tanason jin shin minene kuka nema ga adalin Sarki mai gaskiya da son ayi gaskiya irin Sarki Saifudden yak’i baku goyon baya har kuka nakasashi?”.
          Josaya bamma ya gyara tsayuwa kansa a duk’e saboda kunya. Yace, “Ya mai Shari’a, mu mun kasance y’an k’ungiya d’aya masu burin kafa gwamnatin farar hula a wacan lokacin, mafi yawa acikinmu tare mukayi karatu a landan, tunkuma munacan wannan shine babban burinmu, dan haka koda muka dawo najeriya muna kan wannan buri, duk da mulkin soja shike gudana a k’asar tamu, kuma babu wani mahaluki daya Isa yin koda kwakwkwaran tarine, da farko mun fara janyo wasu mutane da yawa suka shigo jikinmu, sannan muka farabin sarakunan gargajiya Na kudanci da arewaci dan samun had’inkai, wasu sun amince mana, wasu kuma sun nuna babu ruwansu, Sarki Saifudden yana sahun farko Na manya-manyan sarakunan gargajiya da akeji dasu da girmama maganarsu a arewaci, munada yak’inin inhar ya bamu goyon baya mun gama samun abinda mukeso, wannan yasa muka fara binsa ta k’ark’ashin k’asa, wato su Mike sukaje ga wazirinsa suka gana da samun manya-manyan sirrika a wajensa, sunje da kwanaki biyu muma sai muka tunkari Sarki Saifudden bisa jagirancin Waziri. Cikin lalama da rok’o muka fahimtar dashi manufarmu, amma saiya fusata, yakuma jamana gargad’i karya kuma ganin koda masu kama damune a masarautarsa, kuma lallai shi da kansa zai nemi shugaban k’asa mai mulkin wancan karon ya sanar masa manufarmu, munta k’ok’arin fahimtar dashi amma yak’i saurarenmu, daga k’arshema saiya koremu daga masarautarsa, wannan shine dalilinmu Na shirya cewar zamu kasheshi, amma daga baya saisu Mike suka kawo mana shawarar masa allurar poison, bamusan ya akayi wannan d’an jarida ya San da shirinmuba harya biyomu inda muka ke6e dan tattaunawa, munta bibiyar rayuwar d’an jarida amma bamu sameshiba, marigayi tanderu ya k’arfafa mana gwiwa akan karmu fasa yin shirinmu, waziri zai kula da motsin kowa a masarautar, a ranar Waziri yatafi da wannan allurar guba, dakuma asubahin washe gari yacika mana aiki, bamu sakejin labarin d’an jarida ba saida Sarki Saifudden yacika watanni uku da fara jiyyasa, saigashi cikin yaranmu wani ya samoshi, sun bishi dansu kasheshi amma saiya 6oyema ganinsu, Ashe yabi motar mai dawakai ne daya gani akasuwa yazo sayen abincin dawakai. Wani bawane yaga wannan d’an jarida tareda mai dawakai a barga, shikuma bawan yana d’aya daga cikin wad’anda waziri ya baza a masarautar domin saka ido, dan yasan komai Daren dad’ewa d’an jaridarnan saiya so kawo camera d’in a masarautar, a lokacin yasaka ancigaba da bin d’an jarida, yakuma k’yale su mai dawakai har zuwa dare yaje garesu. Camera dai tacigaba da walagigi, har muka samun kashe d’an jarida, a lokacin bamusan Alhaji Rabilu munafuki bane yasan komai, har yazo ya shiga jikin mu da cewar yazo shiga tafiyarmune, Ashe munafuki yasan komai, dan bamuga fuskarsa ba lokacin damukaje fadamar bayan gari, shi Badi shikad’ai muka gane tunda dama waziri ya sanar mana. Muncigaba da Neman Badi har tsawon shekaru 4 amma ko labarinsa babu, saidaga baya cikin shekara ta biyarne muka samu labarinsa a wani k’auye, munta bibiyar rayuwarsa daki-daki, har randa yabaro k’auyen muka cigaba da binsa, lokacin daya farga damu shine ya gudu Alhaji Auwal Fharuk ya bigeshi da besfa, lokacin da yaranmu sukazo shi Alhaji Auwal Fharuk saiya gudu, dan haka basuga fuskarsa ba, shikuma Badi ya suma, a tunaninsu ya mutu, suka daddike gawarsa suka dawo suka sanar mana babu camera d’in a hannunsa, sannan kuma ya mutu, amma suna k’yautata zaton yabama wani kafin zuwansu, kilama mai besfa d’in daya bigeshine, bamu hak’uraba, mun cigaba da lalube dukda bamusan wanene ba, ana cikin hakane kuma muka samu damar kar6ar mulki, burinmu ya cika, Alhaji Labaran Khacia yazama shugaban k’asa kamar yanda muka tsara, dan dukya fimu arzik’i a lokacin, saidai kuma yana shekara biyu kacal da hawa mulki Alhaji Lawan tanderu ya rasu sakamakon had’in mota, shugabanci k’ungiya yadawo hannuna, Tanderu bai dad’e da rasuwa ba shima Alhaji Labaran yakwanta jiyya, kwanansa baifi 6 ba ya mutu shima, lallai wad’annan rashin sun girgizamu matuk’a, har yanzu kuma mun kasa mantawa. Tun daga wancan lokacin duk Wanda zaiyi shugabanci a k’asarnan da taimakonmu yake yinsa, kuskuren da mukayi shine mantawa da Sarki Saifudden nada d’a namiji, kuma komai Nisan lokacin zai iya Girman da zaibi ba’asin ciwon mahaifinsa, gaba d’aya sai hankalinmu ya k’arkata ga son samun Camera kawai, a tunaninmu damun sameta dukkan magana ta k’are. Har lokacin da muka fahimci Alhaji Rabilu shima munafukinmu ne, shine muka titsiyeshi akan camera, amma yace bai saniba, Alhaji Shehu ya d’auki mataki a kansa, dan dukkan Wanda yasan da zancen camera burinmu mu kaudashi kawai magana ta k’are, Bamu farga da yarima Sameer ba sai lokacin da ya fara bibiyarmu, Ashe a time d’in shi C.I.D nema, mukuma duk bamu saniba, da taimakon d’an waziri Harun muka samu bayanan sirrin Documents d’in shi yarima Sameer, dan haka Kabiru Ibraheem da shima masanin Computer ne ya shiga yimasa kutse, dan munason musan shin yarima Sameer yana sane da mune? Inhar yana sane damu mukaudashi shima. Saidai kuma yaron ya wuce da dukkan tunaninmu, yanda muke bashi wahala haka shima yayta bamu wahalar, aka cigaba da yak’in sunk’uri, kowa baya ganin kowa kenan, kwatsam saiga Alhaji Shehu Darma yazo mana da labarin Camera fa Na hannun Alhaji Auwal Fharuk, wannan yasa muka koma bobiyarsa, mun masa tayin dukiya mai yawa sau babu adadi amma yak’i saurarenmu, munma rayuwarsa barazana nanma a banza, daga k’arshe muka nemi kasheshi shima, amma ya tsira bai mutuba, Yarima Sameer ma ya d’aukeshi zuwa India, dukda a India d’inma bawai mun barsa bane, canma musha bibiyarsa da barazana, amma taurin kansa yahanashi bamu har zuwa yau d’inan,  munsha kaima rayuwar Sameer hari shima ta 6angarori da dama amma yana shallakewa cikin tsarewar Ubangiji, wannan shine abinda ya faru yamai shari’a”.
 
       Babu abinda kakeji a kotunnan sai sauke ajiyar zuciyar jama’a, alk’ali yace yaje ya zauna.
    Yad’anyi rubuce-rubucensa sannan yace “kotu tana buk’atar son ganin Waziri a gabanta”.
        Waziri Munafuki, saikace an tsamo 6era a ruwa haka yafito yana wani kakkange fusaka, shima inda kowa ke tsayuwa yaje ya tsaya, bayan ya fad’i sunansa Alk’ali ya jeho masa tambaya.
      “humm Waziri, kotu zataso sanin minene ya had’aka da Sarki Saifudden da zafi haka? Harka za6i cutar dashi wajen had’akar wasu bare can?”.
       Waziri yakuma k’asa da kansa, murya a raunane yace, “maganar gaskiya son zuciyane kawai ba wani abuba, danshi mai martaba ya kasance mutum mai zama akan ra’ayinsa, sannan mai gaskiya da sauk’in hali, nikuma nacika tsugunne-tsugunnen rashin gaskiya, sannan inada sonkai, komai nafison a masarautar gagara badau a fifitani saman kowa, akuma girmamani, wannan halin nawa nason handame komai Na mutane yasaka kullum Sarki kemin nasiha dason gyara halayyata, nikuma nak’i saurarensa, saina kallon hakan danake matsayin cin zarafina yakeyi a kullum, lokacin dana fara ganin take-taken Sarki nason tu6eni sai hankalina ya tashi, nafara Neman mafita, (kusan dai ita sarautar waziri ba gadonta akeba a k’asar Hausa) ina cikin fad’i tashine Neman mafitane wad’annan turawa biyu su Mike sukazo min da tayin mak’udan kud’i da wasu alk’awura, bisa sharad’in sonjin sirrin masarautar gagara badau, babu wani 6oye-6oye Na sanar musu komai, karaf sai’a kunnen wani dogari amintacce ga Sarki, shine yaje ya sanar masa komai, Sarki yakirani har turakarsa ya titsiyeni, yaci mutuncina iyakar iyawarsa, wannan Abu shine ya fusatani, naje Na samu su tanderu muka had’e, dan aganina Sarki ya tozartani a masarauta, tunda gashi yana niyar tu6eni kamar yanda ya fad’amin, nikuma aganina kafin ya tu6eni ya tozartani gara ni nahad’a kai da wad’anda zamu tu6eshi, wannan dalilinne yasakani basu had’inkai, akuma washe garin dana amso allurarna da asuba muna salla, anyi sujudar farko ta sallar asubahi Na kafa masa allurar a cinya Na tsiyaye ruwan kafin a d’ago, amma Sarki dukda nasan yaji zafi, yakumasan cutar dashi akeyi baiko motsaba, saida aka idar da sallar dashi, anayin sallama ya juyo muka had’a ido, baisamu damar min maganaba ya yanke jiki ya fad’i, tun daga wannan lokacin yakoma shida gawa banbancinsu kad’annane, to dama shima wazirin Sarki Abdul-Fatah kuma  d’an uwansa shima da nashi shiri akan Sarki Saifudden, dan yanajin haushin ba jikokinsa y’ay’an y’arsa gimbiya Marawuyane (mama Fulani) zasuyi mulkiba, dan lokacin su zaharadeen sunyi had’arin jirgi sun mutu, to burinsa kullum ya durk’usar da Sarki Saifudden jikansa Jalaludden ya gaji mulki, wai tunda gimbiya Kahdija matar Sarki Abdul-fatah ta gaje musu masarauta, shima dolene d’iyarsa mama Fulani ta gaje ta gagara badau, wannan ya sakashi shigowa cikin tawagarmu dasu tanderu, Sarki Saifudden Na kwanciya jinya kuwa aka d’ora Jalaludden bisa karaga a matsayin mai ruk’on kwarya, bisa alk’awarin zan cigaba da wazircinsa, sannan kuma sarautar waziri tazama din din din, y’ay’ana ma zasu iya gadona, shiyyasa lokacin da aka sanarmin ga camera a hannun mai dawakai nayi azamar son kar6a, amma yamin gardama, nikuma Na kashesu shida matarsa dan karsu tonamin asiri, nakuma saka yara subimin d’ansa daya gudu da camera, a masarauta kuma nace Badi da kansa ya kashe iyayensa. Maganar gaskiya mama Fulani batasan mahaifinta yayi wannan shirinba, danya ta6a tuntu6arta da batun kashe Sarki Saifudden amma tace Sam bata aminceba, bazata ta6a kisan kaiba, shiyyasa bai ta6a sanar mata yanda akayiba, shikansa Sarki Jalaludden baisan komaiba, dan yana masifar son d’an uwansa, bayason abinda zai ta6ashi, shiyyasa nikuma Na dinga kwantar masa dakai dan karma ya fahimci wani Abu, nasaka d’ana Harun yake bibiyar mana dukkan motsin Sameer. Wannan shine dalilina yamai shari’a”.
      Alk’ali yace, “toshi mahaifin gimbiya zulfa uwargidan Sarki na yanzu minene ya kawo shi a ciki? tunda dai yanzu bashida k’arfin da zaizo kotu ya bamu amsa saboda girma ya kamashi sosai, nakuma San Kasan komai shima a kansa?”.
     Waziri ya gyara tsayuwa yana jinjina kai, yace, “shima dai shirinsa bai wuce akan mijin y’arsa yayi sarautar ba, wato Sarki Jalaludden Na yanzu kagadai dolene jikokinsa su gaji sarautar anan gaba, sannan kuma yanajin haushin sarki Saifudden d’in, dan shi yaso ya auri d’iyarsa zulfa amma sai Marigayi Sarki Abubakar ya had’ashi da d’iyar Amininsa gimbiya Zaitun, bayan rasuwarta ma Yakuma masa tayin wata y’ar tashi amma sai aka maye gurbin gimbiya Zaitun da gimbiya Zeenah, shi burinsa dai ya nuna inhar ank’i aurama Sarki mai sarauta y’arsa to jikokinsa koda tsiya saisunyi sarautar gagara badau d’in, lallai wannan dai shine dalilinsa shima”.
    Babbar magana, wai dukdai akan mulki kayan duniya aketa wannan k’ulla-k’ulla, Wanda gashi yanzu a cikinsu wasuma sunbar duniyar baki d’aya, wannan wace iriyar masiface haka?.
     Alk’ali ma kasa magana yayi, saida yad’au ruwa yasha tukunna, Galadima kam ai babu mai iya tantance halin dayake ciki, ya kwantar da kansa jikin kujera yasaka handkerchief ya lullu6e fuskarsa gaba d’aya.
      Alk’ali yace, “Lallai a gaisheku, Ku yanzu dan girman ALLAH bakuji kunyar kankuba? Kamarku manyan mutane da k’asa ke alfahari daku da girmamaku Ashe ru6a66une a bad’ini, maciya amanar k’asa, lallai barin irinku ma ai had’arine wa duniya baki d’aya, dan duk abinda aka nema Na wulak’anta k’asarku zaku iya mik’awa domin cikar burinku, kune masu 6ata shugabanni Na kwarai masu k’yak’yk’yawar zuciya,  ALLAH ya cigaba da tona mana asirin irinku a k’asarmu”.
      Gaba daya Kotu ta amsa da Amin!!!,
   Alk’ali yay k’asa da kansa yana bincike a k’aton books d’in gabansa kusan hud’u, kotu tayi tsitt kowa ya zuba masa ido, ya d’auki tsawon lokaci yana rubuce-rubuce kusan 30minute’s sannan ya d’ago yana cire eyeglasses d’in idonsa, yasaka handkerchief ya goge fuskarsa sanan ya goge eyeglasses d’inma ya maida a idonsa yana kuma gyara zama dayin gyaran murya. Yace,  “Bisa ga hujjoji da bayanan da suka fita a bakin wad’anda ake zargi kai tsaye, wannan kotu mai adalci ta yankema wad’annan mutane 20 da sukayi gamayya wajen ciwon Sarki Saifudden hukunci d’aurin rai da rai a gidan kaso, saboda kisa da suka dinga sakawa a nayi bayan laifinda suka aikata”.
    Kotu ta d’auki sowa gaba d’aya, saida alk’ali ya tsawatar ta hanyar buga gudumarsa, kowa yay tsitt.
    Alk’ali yacigaba da fad’in “Wazirin Sarki kuwa hukuncinsa shine kisa ta hanyar rataya, sakamakon kisan mai dokuna da matarsa, Hakama Alhaji Shehu darma, d’aurin rai da rai da horo mai tsanani saboda bada had’in kai wajen kisan d’an Uwansa Alhaji Abdul-Hakeem uba, dakuma tsiyatakun da suka dinga sakashi yanayi. Akwai yaransu dake hannu bisa laifi daban-daban da suka sanyasu, suma dai d’aurin rai da rai ne akansu, Irinsu Alhaji Halluru, Timothy da sauran su shekaru 30-30 ne hukuncinsu, da horo mai tsanani, dukansu babu maganar beli, dolene saisun rayu a gidan kaso. Sannan wannan kotu ta wanke Muhammad Sameer Saifudden bisa zargin ta’addancin Garkuwa da yara da yayi, dan bai ta6a kowaba a cikinsu, dagashi har tawagarsa da suka bashi gudunmawa kotu ta wankesu tas. Akwai d’angidan Waziri mai Suna Harun, kotu ta yanke masa zaman kaso Na shekaru goma bisa ga cin dunduniya Muhammad Sameer daya dingayi wajen sato bayanansa, ina fatan kowa yasamu hukunci dai-dai da abinda ya aikata, kuma duniya ta gamsu da hukuncin da muka yanke?”.
   Kotu ta d’auki sowar gamsuwa da ALLAH wadai da halin irinsu waziri dasu Darma. Kowa tur yakeyi da halin masu.
     Alk’ali ya buga gudumarsa alamar kotu ta tashi, daganan kowa ya mik’e saida ya shige sannan aka kacame da hayaniya, harda masu kaima su Alhaji Halluru duka, ana musu ihu, saima da aka fidosu mutane sukaita jifansu da duwatsu, sai y’an sanda suka dinga karesu har aka zubasu a mota, wasunsuna kuka sukeyi rurus dan ganin iyalansu ko damuwama basuyiba, wasu a cikin yaransu ai ko’a kwalar rigarsu, k’alilanne a cikinsu suka damu.
    Galadima har kowa yafita a kotun shi yakasa motsi, saida Abba Hayatudden da baffi da Abban munaya sukazo kansa, baffi ya cire Handkerchief d’in daya lullu6e fuskarsa saisukaga ashema a sume yake?, rikicewa sukayi, aka samo ruwa Abba Hayatudden ya shafa masa a fuska ya kawo numfashi.
              Zabura yayi, saida Abba Hayatudden ya rungumesa, jinsa a jikin k’anin  mahaifinsa saiya saki wani irin kuka maiban tausayi, daga Abba har Baffi suma idonsu yacika da kwalla, Abba Hayatudden yashiga shafa bayan Galadima alamar allashi. Kusan mintuna uku ya d’ago da hanzarinsa yana fad’in “Abba Munaya da Nuren, lallai ban yarda darashin zuwansu kawo camera ba, alamun sarkin mota sun nuna akwai wani abu”.
    Da sauri baffi ya fita Neman sarkin mota, a waje ya iskeshi tsaye yana jiran fitowar Galadima.
    Baffi ya tambayesa miya faru, bai 6oye masaba ya sanar dashi komai, hankalin Baffi a tashe yakoma ciki yace su fito suje, hakkanne ya tada hankalin Galadima da tabbatar da lallai akwai matsala.
    A rikice suka shige mota, ko kallon y’an jarida dakeson jin bayani a bakinsu basuyiba, balle bi takan jama’a dake jiran su fito sumusu jaje………………..????
Lallai K’arshen munafuki dama duk inda yake jin kunya, duk yanda kakai ga k’ulla kuttun sharri watan watarana saikaga k’arshenka, a duniya ne kokuwa a lahira, babu abinda ke dawwama sai ALLAH, Idan khairan ka shuka lallai saika girba khairan, idan kuma sharranne shima saika girbe abinka, duk danne Gaskiya da k’arya zatai wlhy watan watarana sai gaskiya tadawo sama k’arya ta koma k’asanta, kwanaki 99 ne suke zama Na masheranci, 1 tak kuma suzama namai gaskiya da k’yak’yk’yawar zuciya, d’ayarnan kuma saikaga yazo maka da nasarorin daka rasa shekaru aru-aru, duk nisan jifa k’asa zai fad’o, gashi dai yau su Harun sunzama a k’asa, k’asanma cikin matuk’ar k’ask’anci, musamman ma iyayensu.
    Ya rabbi ka tsaremu ka tsare mana zukatanmu, ka hanamu cutar da wani koda da fatar bakice, ko’a social media bana fatan kwana da hak’in wani ko hassadar wani, idan nabar duniya wace amsa zanbama ubangiji akan d’aukar zunibin wandama banta6a ganiba a zahiri????, ya ALLAH ka gafartamana muda iyayenmu da dukkan musulmai baki d’aya, ALLAH ka rabamu dacin hak’k’in kowa koda kwayar zarrane????????????????.
    Kumuje zuwa asibiti, danjin wane hali Munaya take ciki itada Nuren kuma?.????
*_Nagode sosai da addu’oinku gareni, da mahaifina, ALLAH ya bada ladan zuminci Yakuma kar6a mana baki d’aya, bansan yazan nuna godiyata ga masoyanaba, saidai nace kuma ALLAH ya biya muku buk’atunku, kaini har mak’iyinama ALLAH ya biya masa buk’atarsa ta alkairi,  dan saida mak’iyi duniya ke dad’in zama????????????????, idan babusu tamkar miyace lami babu gishiri da magi????????????.????????????????
ALLAH ka gafartama iyayenmu????????????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button