Bakar InuwaNOVELS

BAKAR INUWA 27

Episode 27

BAƘAR INUWA????????AREWABOOKK????????


Assalamualaikum lovely brothers and sisters. Please support our YouTube channel sudais kura for Allah sake our channel is all about Qur’an recitation and other Islamic studies ???????? I am not perfect, but I’m a mother who love to see kids Recite Qur’an. I’m trying my best with the little I know to install the love of the holy Qur’an into sudais heart at this young age. Please support our journey by subscribing to Sudais kura YouTube channel ????we are planning to start some simple craft and art work too on the same channel insha Allah. Just subscribe and you will not regret❤️ the channel link ????????
https://youtu.be/g6BGEBv-X8Y


………..GOVERNMENT HOUSE

Barci sosai tayi har taji babu daɗi. A kowanne motainta Tambaya kan leƙa ta tabbatar tana lafiya. Bata farkaba sai bayan la’asar. Taji daɗin jikinta sosai dan magunguna masu kyau Dr Farhat ta bata. Wanka ta farayi mama tambaya ta gyara mata ɗakin tunda dama aikinta ne. Bata tambayeta wacece ita ba tunda tasan a irin wannan gidan dama dole a samu ma’aikata. Bayan ta gasa jikinta da ƙyau ya sake warwarewa tayo alwala ta fito. Ɗakin ya sake komawa tsaf sai ƙamshi yake. Batabi takan komai ba ta gabatar da sallolin dake a kanta sannan ta miƙe ta buɗe akwatinan da aka zube matan.

Cikin sa’a ta samu ɗinkakkun kaya kala kusan biyar da sai daga baya aka amso a wajen tela dan bai kammala mata na fitar biki ba da a aka kai wancan ranar. Riga ne da skirt na atanfa less Onion color. Sai ratsin milk kaɗan a jiki da stones da aka kawata ɗinkin da shi. Kayan sun mata ƙyau da fiddo kalar fatarta musamman data ɗan rame kwana biyun nan. Duk wanda ya ganta yaga amarya kodan gyaran jikin da tasha na nagartattun kayan *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* da duk amaryar da akaima gyara da su dole tazama abar kallo. (Amare dama mata ƴan ƙwalisa dake buƙatar kayan

 

gyaran jiki na musamman, tun daga kan ƙamshi na turarurrukan gida dana jiki, har zuwa gyaran fata da kayan mata ingantattu ku garzayo ga *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* domin samun naku kuma. Masu iya magana kance siyen nagari maida kuɗi gida????????????), ga lallin ƙafarta da hanunta raɗam tamkar bazai fita ba. Mama tambaya ce tazo ta sanar mata an shirya mata sabon abinci tunda breakfast ya huce, anma fiddashi tuni. Ta amsa cikin mutuntawa ga mama Tambaya dan koba komai zata iyama jika da ita.

 

Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, amma tanajin yunwa. Dan haka tai dauriyar fitowa falon saman inda mama tambaya ta saka kuku ya shirya abincin. Sosai mamaki ya cikata ganin table ɗin a cike, dan babu wani zancen ƙauyencin gidan ko tsarin abubuwansu tattare da ita kasancewar an mata lectures na koma kafin ta shigo. hasalima ta shigo ɗin tun kafin a kawota matsayin matar gidan. “Mama wannan abinci duk suwaye zasu cisa haka?”.

Kan mama Tambaya dake tsaye a ƙasa tai murmushi. “Ranki ya daɗe ke da shugaban ƙasa ne kawai, duk da bamu da tabbacin shigiwarsa gida a yanzun”. Mamaki da takaici ya kume Raudha a rai. dan kai tsaye ta danganta hakan da almazarancine kawai. Talakawa nawane suke wahala babu ko ruwan kunu da zasu sha a yau, amma an shirya abinci fin kala huɗu a dining ɗin gidan shugaban ƙasa wai dan shi kawai da matarsa. Tabbas ta sake yarda mulki BAƘAR INUWA ne kawai. Dan hakkin mutane kawai aka barka da shi ka shiga uku. Ta rumtse idanu da haɗiye ɓacin ranta, cikin saisaita murya tace, “Mama yayi yawa ai, ya kamata a

 

dinga dafa iya wanda za’a iya ci kawai ya wadatar. Dan ALLAH daga yanzu a dingayin dai-dai misali. Idan kuma ansan ma shugaban ƙasa bazai dawo yaci ba adaina girkawa da shi har sai idan shine ya bukaci hakan”. “Amma ranki ya daɗe haka tsarin yake tun a wancan shugaban kasar mai sauka dana sani nidai.” “To mama inaso a canja yanzu danni dai bana buƙata sam”. “Insha ALLAHU za’a gyara ranki ya daɗe, dan dama dai tun ɗazun duk ma’aikatan gidan nan suka gama taruwa domin gabatar da kansu gareki”.

 

Duk da gaban Raudha sai da ya tsinke ya faɗi dan fargaba tausayin kanta sai ta dake tace, “Ba damuwa sai a sanar musu na tashi to”. “An gama ranki ya daɗe. A fito lafiya”. Kai kawai Raudha ta iya ɗaga mata, dan babu abinda ƙirjinta keyi sai luguden daka. Ita Raudha, ɗiyar Mal. Ɗan-azumi da Asabe na Hutawa ce a wannan ajin na ƙaddara. Itace akema wannan girmamawar duk da ƙarancin shekarunta. Itace matar shugaban ƙasa wadda kowa zai iya kira da first lady a ƙasar NAYA da ƙetare a yanzun. Itace matar shugaban ƙasa *_Ramadhan B. Hameed Taura_*.

 

Ɗan ƙwalisar gayen nan maiji da giyar kuɗi da lokaci, ƙyaƙyƙyawa mai girman kai da jan aji wa manyan mata. Wannan wace irin ƙaddara ce haka mai kama da almara ko hikayoyin marubuta. Badan tayi imani babu mai iya ja da ikon ALLAH ba da tace kodai ta mutune ko barci take har yanzu komai nazo mata a mafarkine ba gaske ba. Wannan ƙaddara ta mata nauyi da yawa a zahirin rayuwa da baɗini. Gaskiya mahaifiyar Ramadhan ɗin ta faɗa ita ba kowan kowa bace, sannan Ramadhan yafi ƙarfin yafi ƙarfin kowa nata. Sayyadi Abubakar ma da bai kama ko ƙafarsa ba iyayensa suka tabbatar da ya fita balle shugaban ƙasa. Waɗan nan tunane-tunanen suka hanata sakin jiki taci abincin kirki har mama Tambaya ta sake dawowa ta isar mata da saƙon taruwar kowa. Tambayar mizai hana su shigo nan tayi.

 

Cikin girmamawa mama Tambaya tace, “Ranki ya daɗe basu da wannan hurumin sai mu huɗu kawai. Ni da Chief kuku da mai gyaran ɗakin shugaban ƙasa sai mai gyaran falon nan kuma.” Ɗan jimm Raudha tayi tana dubanta, sai dai komai bataceba ta miƙe da ɗaukar milk gyalenta data fito dashi ta yafa har saman kanta sannan suka fito. Tana gaba mama Tambaya na take mata baya ★Falo ne babba da za’a iya kiransa mafi girma a duk falukan gidan.

Komai na cikinsa kalar tutar ƙasar NAYA ne. Ya ƙawatu matuƙa da kayan more rayuwa. Ma’aikatan da adadinsu zai kai kusan hamsin suka rissinar da kai domin girmamawa. Gareta suna miƙa gaisuwa. Duk da ba kabilarta bane su duka haka ta amsa musu cikin mituntawa dan babu wanda bai kere shekarunta ba a cikinsu.

 

Shugaban ma’aikata na sashen nata ne ya fara gabatar da kansa, sai shugan kuku’s da sauran kukus ɗin, sai Mama Tambaya da mai gyaran ɗakin shugaban ƙasa. Kafin sauran su cigaba ɗaya bayan ɗaya. Tun ma Raudha na fahimtarsu har da daina tunaninta ya tafi wani wajen da ban. Cikin nutsuwa ta ɗaga musu kai da fara faɗin, “Masha ALLAH naji daɗi, ina kuma fatan zaku riƙe amana dan nasan babu wani addini dake goyon bayan cin amana ko zalunci. Bazance karku cutar damu ba ko a haɗa baki daku wajen cutar damu. Sai dai zance kuji tsoron ALLAH karku zaluncemu da son zukatanku ko biyewa ruɗin kuɗi. Idan kun kiyaye kuma ALLAH zai kiyayeku ya ɗaga darajarku zuwa wani matsayi da baku taɓa zato ba.

 

A duk lokacin da bawa ke tsoron rasa wani abu wani nacan ya samu yayi shi. Idan murna da farin cikin samu kake wani nacan shi kukan rasawa yayi. Sai musa a ranmu duk zamu iya zama ɗaya daga cikin wannan matsayin. Dan a duniya babu mai wahala sama da _mai buƙatar abu a lokacin da abun baizo ba. Da kuma mai ƙin abu bayan ana tsaka da samuwar abun_.

 

ALLAH yasa mu dace, ya bamu ikon sauke nuyin juna bisa bigiren tsoron ALLAH da cire son zukatanmu ko yanke hukunci akan umarnin zuciya”. Sosai sunji daɗin kalamnta, wasunsu da zamansu nada alaƙa da kalamnta na son cutar dasu sai jikinsu ya fara sanyi. Gata dai ƙaramar yarinya amma tanada cikar kamala da kwarjinin manya.

 

Uwa uba iya sarrafa harshe cikin taka tsantsan da mutunta kowa. Wasu kuwa da yake zuciyar ta bushe ko’a jikinsu, a ganinsu ma ta cika iyayine da son nuna ita mai addini ce. Sun shiga mata godiya bayan ta sallamesu. Daga haka ta koma ciki abinta. Zaman ɗaki ta cigaba dayi har ƙarashen wannan yini babu shugaban ƙasa babu alamarsa. Maganinta da tasha ya sata barci da wuri ma batare da ta damu da yanda wanda ya aurota ya banzatar da ita ba.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button