SAMEEHA E

????SÂMÊĒHÂ????_*
*_(E)_*
Miqewa Umma tayi ta nufi bishiyar mangwaron da take tsakar gidan,rubutun ta bula a hankali ta juyeshi har ya rage saura ledar kadai ce a hannunta ta sake juyawa tayi dakinta da ledar,Moona tabi bayanta da shigowarta gidan kenan.
“Umma ba dai rubutun ya Sameeha kika zuba abakin bishiya ba ya jummai tace dani na kar6a na Kai Mata yanzu yanzu Kar abari ya kwana,..
Memuna!!
Na am Umma.
Memuna.
Na’am.
Sau nawa nakira ki.
Sau Biyu ne umma.
Yadda kika ga nayi da rubutun nan kija bakin ki kiyi shiru shiya fi miki ko tambayar ki ya jummai tayi an kai wa Sameeh rubutu kice,Eh an Kai mata idan kuma naji sa6anin abinda na fada miki wallahi ranki siyayi mugun 6aci.
Amma Umma…..dakata ban nemi shawara ko qarin bayani ba idan ta sameeha ne zanwa tufkar hanci kota tambaye ta zatace an Kai Mata.
Zuwan nawa fa.
Shima ba yanzu ba ki bari ta sake kwana 2.
Haba haba umma Kwan biyun Nan har yanzu basiyi ba ni naqagu Naga ya Sameeha dan Allah ki barni naje na ganta.
Allah babu inda Zakije sai ta qara kwana biyun dai.
Innanillahi,ni ko kwana biyun sunyi ba inda zanje,fuuu Moona ta fito daga dakin ranta adagule, Umma tabi bayanta da kalo.
Hmmm Ke kika sani zuwa ne dai bazaki ba sai ta qara kwanaki..
★★★★
Duk yanda momy tace ayi Sameeha ta gabatar da shirin komai ta Kamala hada kayan motsa Baki da farfesun kaza ta kai inda tasan ake ajiyewa danci ta ajiye ta juya Dan komawa barin Momy,”zaune ta iske momy qafarta daya akan daya tana waya a hankali kamar Bata so aji me take cewa Sameeh tayi sallama da ko amsawa Momy batayi ba ta tsuguna daga baya tace.
“”Na gama hada komai Momy,kanta a duqe.
Mutsssssssss,sabga da jaki a ko Ina sai ya nuna halinsa da gidahumanci ke a hankalinki idan kazo kasami mutum na waya meya kamata kayi.
Kajira ya qarasa wayar dayake yi kayi masa magana.
Amma kika shigo min daki kai tsaye kina son Jin abinda nake fada ko.
Wallahi ba haka bane momy kince idan na gama koma na zo na fada miki shi yasa nazo Amma Dan Allah kiyi haquri bazan qara ba.
Matso nan.
Dan Allah Momy kiyi haquri insha Allahu bazan sake ba.
Kar ki kuma bani hakuri idan nace sai nayi abu sai nayishi ko zan rasa wani abu nawa ki matso nace.
Jikinta duk ba qwari Sameeh ta janyo qafa ta matso Inda momy take zaune,tana matsowa momy na wanka mata mari guda biyu masu zafi a dai dai lokacin Zee ta shigo da jaka a hannunta tana.
Momy Momy…….
Na’am Dota Dota saukar yaushe.
Momy wannan Kuma fa zee ta hade rai.
hmmm ita ce matar Sameer.
Ohhhhh har ta fara 6ata miki rai ne.
Kema kin San ban daukar Rai ni hukunci nayi mata dai dai da ita.
Gaskiya ne momy na aikin ki yana kyau ya Sameer din ma na waje,Zee ta dubi Sameeha sheqeqe tace.
“Ke maza tashi kije ki taya mijin naki dako min kaya duk kin tsare mutane da ido kamar mujiya.
Sameeha ta dubi momy.
Tunda tace ki tashi ki tashi Mana ko sai na furta da bakina.
Ajiyar zuciya sameeha ta sauke dafe da kuncinta ta miqe a hankali ta fuce fito daga dakin ranta duk babu dadi ga wani tashin hankali data ga Zee irin wayayyun “yan matan nan ne marasa kunya don kallon da zee ke bin sameeha kadai ya nuna akwai wani abu aqasa,hannuwanta ta miqa sama.
‘Ya Allah gani gareka dakai na dogari bani da kowa bani da komai bazan iya ba ka iya mun ka fiddani daga qangi da baqin cikin dake shirin tunkaro ni Allah ka dube ni.
Ta sauke hannayenta daga sama hawaye suka sulalo mata.
“Bayan taje ta Taya Sameer shigo da jakun kunan zee kai tsaye barinta ta koma danyin wanka ta gabatar da sallah magariba tashiga fallo kenan Sameer yashigo da sauri Yana doka mata Kira,amsawa tayi a hankali ya qaraso daf da ita suna jiyo nufashin junna yace.
Kije Momy na Kiran ki da sauri,gaban sameeha atake ya Fadi jin Momy na Kiran ta,dakewa tayi tace.
To bari na gabatar da sallah kar lokacin ta ya wuce sai naje….
Aa ki bar yin komai kije kiji meye idan kin gama da ita sai ki dawo kiyi sallar.
Haba samee sallah fa nace zanyi kasan lokacin yanzu zai gota.
Ni kuma nace kije ki dawo ko ban Isa dake bane,cikin tsawa sameer yake magana.
Nan da nan Kan sameeha yafara juyawa zuciyarta tashiga Yi mata zafi a hakan ta dore ta fito daga nata barin tayi na momy.
A zaune ta same su Kan Deaining ko wace ta harda qafa daya Kan daya duk fuskar su a hade momy tace.
Sai yanzu kika ga damar zuwa?
Shiru Sameeha tayi tana kallon su,ran Momy yasake quluwa.
“Momy nifa yunwa nakeji idan baza’azo azuban ba natashi naje na huta dama agajiye nake,”Sorry Dota yanzu zata zuba Mike, Momy ta dubi Sameeha,” idan kin gama qare Mana kallon sai kizo ki zubawa dota abinci in kuma kina ganin wuyanki ya Isa yanka ki cigaba da tsaiwa a gurin wlhy Sameer zan saka ya Zane mun ke ciki da Bai…..
Da sauri Sameeha ta bude baki tace.
Dan Allah Kiyi haquri na tsaya yin sallah ne.
Ashe malama ce bamu sani ba mu ai bamu san sallar ba sai ke da kika santa Wai ma dakika zo kika ajiye kayan abincin wazai zuba ko abincin da kansa nezai zuba kansa.
Aa kiyi haquri zan zuba mata.
Sai anyi magana tafi kowa bakin bada haquri gashi ni kuma ban San shiba Naga alama idon ki a tsaye suke amma nasan me zan miki ki wuce ki zubawa zee abinci.
Sim sim sameeha ta wuce ta zubawa Zee abince sai hararar ta take kota kanta Bata bi ba tana gamawa ta tsuguna tace.
Na gama zan iya tafiya.
Nan da 10mnt ki dawo ki kwashe kayan sannan ki goge wajan da safe kar kiyi lattin hada abin karyawa idan kikayi kuskure jiki zai tsami, sameeha ta amsa da to ta miqe ta baro barin bayan ta dawo taje tayi alwala tayi sallah ta jima tana gayawa Allah tana kuka qasa qasa akan Allah yabata ikon cinye jarrabawa data sameta sannan ta miqe taje ta kwashe kayan ta maidasu kicin din gidan Bata iske kowa awajan ba ta dawo ta shiga wanka….
Dare ma hutar bawa sai bayan 11:30 na dare Sameer ya dawo daga 6arin Momy akan sallaya ya iske sameeha yaje ya watsa ruwa ya dawo yai kwanciyarsa ko ci kanki bai tanka taba bare yaji ko taci abinci.
Ta Dade tana Addu’o’i kafin taje ta kwanta sitl abinda ya faru a wanchan daran shiya sake faruwa sai dai Dan ban banci kadan dake tsakani……………..
_*By*_
_*Mâmâñ Dr @ff@ñ*_