ganyen moringaGyaran JikiLabaraimoringaZogale

Cin zogale ga mata masu ciki na da matukar illa ga jariran cikinsu 

Cin zogale ga mata masu ciki na da matukar illa ga jariran cikinsu

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Ba bakon abu bane idan aka sanar da mai karatu cewa zogale na maganin manyan cututtuka masu yawa.

 

 

 

Sai dai kuma masu bincike sun gano illar ganyen zogalé, ‘ya’yan shi da man shi ga mace mai juna biyu.

 

Yana sa mace ta haifo da mara wasu sassa na jiki ko kuma yaro mara karfin kasusuwan jiki Sanannen abu ne cewa zogalè ganye ne dake dauke da sinadarai daka samar wa mai ci lafiya da kuma kare shi daga kamuwa da cututtuka.

 

Hakan kuwa bai hana binciko wasu illolin da ke tattare da cin shi ba musamman ga mata masu juna biyu.

 

 

Garkuwa ga mata masu ciki

Ganyen zogalē na taimaka wa wajen kawar da hawan jini, cututtukan dake kama zuciya, ciwon suga, cutar daji, inganta fatar mutum da dai sauransu.

 

Sai dai kash! Duka amfanin da zogale ke da shi a jiki, ma’abota bincike daga jami’ar Ibadan sun yi kira ga mata masu juna biyu da su guji cin ganyen zogale, ‘ya’yan zogale da man zogale domin yana yi wa dan dake ciki illa.

 

Farfesa Adefolarin Malomo, Foluso Atiba da Dr Innocent Imosemi ne suka gano haka a binciken da suka gudanar a jikin wasu beraye 20 da ke dauke da ciki.

 

wajen magani Sakamakon binciken ya nuna cewa ganyen Zogalè na yi wa kwakwalwa, jijiyoyi da kasusuwan jaririn dake ciki illa matuka tun kafin ya zo duniya.

 

Malamin ya ce alamun illolin da Zogale ke yi wa jarirai sun hada da haifo dan da bashi da kafafuwa ko kunne ko baki ko cibiya sannan kuma da kasusuwa marasa karfi da dai sauran su.

 

Likitocin sun yi kira ga mata masu ciki da su hakura da cin ganyen Zogale a duk lokacin da suke dauke da ciki.

 

 

Zogale

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button