Labarai

Rashin kudi matashi ya wankewa abokiyar iskancin sa kaya don biyan bukata  

“Abokiyar kece rainin sa ta umarci da ya wanke mata kaya ya kuma shanya har sai sun bushe duk hakan a madadin rashin kudi sannan sai yaje ya biya bukatar sa.

Jaridar ALFIJIR HAUSA, ta jiyo cewa. Matashin a tunda yake bai taba yi wa mahaiyar sa wanki ba, sai gashi garin banza ta kare a farau-farau din banza.”

“Wani matashi kenan, da ya kware a wurin bibiyar matan banza da nufin Tarawa da su don biyan bukatar sa.”

“A bana dai matashin bayan ya je wurin abokiyar kece rainin sa gashi baida ko sisi a cikin aljihun sa, sai ya nemi alfarman da ta bar sa ya biya bukatar sa a bisa bashi”

Biyo bayan hakan, ita ko hatsabibiyar taki amincewa da batun sa na kusantarta babu kudi; toh” amma ta Samar masa da wata hanya ta yadda zai samu biyar bukatar sa cikin sauki amma idan ya amince”

“A karshe dai ta kwaso ma sa kayan ta duka ya wanke su tas shine a matsayin kudin da zai biya, bisani matashin bai yi mata musu ba. nanfa ya zage damtse yana wanke mata kayan nan “ita kuma ja’irar tana daukan sa hoto.

“Wannan lamarin ya faru ne a shagamu dake jihar legas tarayyar Nijeriya.”

               

[ad_2]

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button