Labarai

Daga karshe Aisha Buhari ta janye ƙarar da ta kai ɗalibi Aminu Muhammad, in ji lauyansa

Matar Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta janye ƙara da kuma tuhumar da take yi wa ɗalibin nan Aminu Muhammad, kamar yadda lauyansa ya shaida wa BBC Hausa.

 

Cikin wani saƙon tes, Barista C.K. Agu bai yi ƙarin bayani ba game da dalilin da ya sa Aisha ta janye ƙarar.

 

Matakin na zuwa ne bayan ɗalibin, wanda ke karatu a Jami’ar Tarayya da ke Dutse, ya shafe kwana uku a gidan yari da ke Suleja bisa umarnin kotun.

 

A ranar Litinin ake sa ran ci gaba da zaman kotun don sauraron neman beli da lauyan Aminu ya yi a zaman ranar Talata da aka yi, wanda bai yi nasara ba.

 

Matar shugaban na zargin Aminu da ɓata mata suna saboda saƙon da ya wallafa a shafinsa na Twitter maƙale da hotonta tare da cewa “ta ci kuɗin talakawa”.

 

Ƙungiyoyin kare haƙƙi da masu sharhi sun soki Aisha game da matakin da ta ɗauka bayan rahotanni sun yi zargin cewa sai da aka lakaɗa wa Aminu duka kafin gurfanar da shi a gaban kotun.

 

Kazalika, wasu sun soki matashin kan zargin da ya yi wa matar shugaban.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button