Al-Ajab

Dan shekara 75 ya yi wa ‘yar shekara 6 fyade a Jigawa

Dan shekara 75 ya yi wa yar shekara 6 fyade a Jigawa

 

Jami’an tsaro na NSCDC a jihar Jigawa sun kama wani mutum mai shekaru 75 da aka bayyana sunansa da Musa Gambo, bisa zarginsa da yi wa wata ‘yar shekara shida fyade a unguwar Sarki Quarters, Malam Madori LGA na jihar Jigawa.

 

Kakakin rundunar NSCDC din, CSC Adamu Shehu ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a garin Dutse babban birnin jihar.

 

ya ce an kama Gambo ne biyo bayan samun bayyanai daga wata mata da ke aiki da gidauniyar Mata ta Hadejia (an sakaya sunanta) ta bayar ga hukumar bayan ta samu tabbaci daga iyayen yarinyar.

 

Wanda ake zargin ya amince da cewa ya aikata laifin kuma ya alakanta shi da aikin shaidan, inda ya nemi a yi masa gafara.

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button