DARAJAR YAYANA PART 3

DARAJAR YAYANA PART 3

Darajar Yayana3-01
Posted by ANaM Dorayi on 10:48 PM, 31-Mar-16
Under: DARAJAR ‘YA’YANA
__________________NA ___________HALIMA K/MASHI Gudu sosai Aliyu yake tamkar zaibar gari,zuciyarsa ta karaya gani yakeyi lallai yana dauke da ciwon har ya hangoshi kwance a rame ga kuraje sunyi mashi caba caba a jiki.da sauri ya ciro wayarshi ya kira layin likitan, Dr kana Asibiti ne? Dr ya ce eh, amma yanzunnan zan fita.Aliyu ya ce, don Allah ka jirani gani daf da Asibitinka.Sama sama suka gaisa, Aliyu yace likita ana yin gwaji yanxu a fitar da sakamako yanzu? likita ya ce gwajin mene?Aliyu ya ce, (H.I.V) ,Likitan ya zaro ido yana kallon Aliyu ranka ya dade kana zaton ciwon a tare da kaine?Aliyu ys ce eh likitan ya ce, likitan yace za a iya, da kansa yayi gwajin, ya daga ya nunawa Aliyu tare da cewa yanzu dai ya nuna baka da ciwon sai dai ba a gwajin farko ake tantancewaba.bayan wata uku za ayi wani, sanan in an sake yin wani wata ukun sai a sake gwadawa sau uku kenan,induk ya nuna babu to babu din kenan saboda gwajin farko yakan nuna babu kuma akwai.Aliyu ya lumshe ido, kenan likita yanzu bani da tabbas kenan? Likita yace gaskiya babu tabbas.ya dafa kafadar Aliyu cikin murya ta son kwantar masa da hankali ya ce, yallabai kadakadamu, ko da ya kasance kana da ciwon domin akwai magunguna wadanda masu ciwon suke sha duk karshen wata.sanan zakaci abubuwan gina jiki don karin kuzari, su magungunan suna yakine da kwayoyin cutar, suna hana kwayar ta karya garkuwar mai dauke da ciwon.Aliyu ya share zufar da ta keto masa ta goshi, sanan ya ce to nagode likitan ya ce se iyalanka ya kamata a gwadasu.Aliyu yakalli likitan yace ana iya daukar ciwon ta hanyar mu’amulan yau da kullum? kamar misalin ta hada kwanon abinci ko yin hirar fatar baki ne?likitan ya ce a’a Aliyu ya ce, to bana tsammanin suna da ciwon,kafin likitan ya sake magana, ya ce na gode likita, na barka lafiya.Da azama yafita ya nufi gida.Nikam lokacin ina zaune bakin gado, idanuna banda xafi ba abinda suke yi, saboda kuka.hawayena sun daina zuba sun kafe. Nakosa yaya ya dawo, addu’a ta Allah yasa yaya bashi da ciwon, dama gidan bude yake dom haka sallamar shi kurum naji abakin kofa,Zubur na mike ina kallon shi, ya zauna bakin gado tare da sunkuyar da kai na dafe goshina ta re da cewa innalillahi wa inna ilaihi raji’un, yaya kana da ciwon ke nan? Shima da sauri ya mike tare da kama hannuna Sadiya kinatsu mana,nasoma kuka. Yaya ka cucemu, kila nima ina da ciwon, shike nan ka mai da mana yara marayu? Ganin yadda na rude yasa shi rumgumeni a jikinshi tsam.Saurara mana nima fa ba cewa akayi ina dashi ba. Na kalle shi me aka ce? Ya ce, sai anyi gwaji uku sanan za’a tabbatar amma yanxu ma ya nuna babu. Na sauke ajiyar zuciya, sanan na ci gaba da gunjin kuka ina cewa. Duk lokacin da bawa ya bar hanyar Allah tabbas sai ya fada da nasani. Aliyu ya ce kiyi hakuri mana Sadiya, nasan cewa ko da ta kasance ina dauke da ciwon nan, wlh sam nasan baki dashi, domin lokacin da na fada wanan kuskuren Allah ya sani ban rabeki ba sai yanzu na tuna ta iya yuwuwa baki da hakki ne shi yasa Allah yasa ban kusance ki ba. Nakalleshi idanuna jajur, tayaya kake zaton abinda ya shafeka bai shafeni ba? Naci gaba kaifa mijinane nasunna, ina sonka koda kai baka sona. Ya maza a ce abinda ya shafeka bai shafeni ba. Yace haka ne kiyi hakuri Sadiya. Tsam! namike nafada bandaki nayo alwala, zuwa nayi na fara jero nafiloli don neman sauki a gurin ubangijina. Can shima sai naga yayi tashi alwalar yazo ya kama yin nafilar, a hankali nake jin zuciyata tana sauka, danagaji sai na dauki alkur’ani littafin da ke dauke da waraka na soma karantawa. Munfi awa uku cikin wanan halin, lokacin zuciyata tayi sanyi kalau. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Shi yasa kullum ina alfaharin kasancewata
musulma. Ina kara godewa ubangijin musullunci
da ya kageni cikin wanan addini ya saukar mana
da Alkur’ani don ya kasance waraka a
garemu.Aduk lokacin da na karanta alkur’ani ko
na saurareshi nakanji sauyin zuciya, ko cikin wata
i ciiin matsala nake.Na kammala nazo na kwanta
yanzu ina jin zan iya jure ko wacce iriin kaddara
da zata hau kaina. Hakanan zan rufawa mijina
asiri inshaAllahu, shima yazo ya kwanta dan nesa
dani muna fuskantar juna. Ya ce kiyi hakuri don
Allah kinji? Na ce, nayi hakuri, na yafe Abban
Kausar, ya wuce a gurina na matsa kusa da shi.
Ya ce baki jin tsoro na? Nace Abban Kausar mu
bar wanan maganar. Ya rumgumeni, yau she
rabom da na kwana hakarkarin mijina sai yau.
Munso mu makara dan haka shine ya jamu
sallah. Zan tafi kicin yace, dawo mu kwanta mu
huta anjima ma karya na dawo muka kwanta
Yadda nake jina yanzu ba zan juya masa baya ba.
Har sai sha daya muka karya, sanan ya shirya ya
nifi gidansu Iya ni kuma na shiga gyaran daki,
minti shabiyar da fitar sa sai gashi ya kira, na
daga tare da sallama. Cikin rudewa ya ce Sadiya
kinga yaran nan sun hadani da Iya ko? Kuka fa
na sameta tanayi please, kizo yanzun kitaimakeni
sam taki saurarena. Hankalina ya tashi. Akofar
gida na sameshi tsaye cikin damuwa nace
meyafaru? Ya ce wlh ban sanme yarannan suka
ce mata ba, na shigo na sameta cikin damuwa
natambayeta me ya faru? Tana kallo na sai kawai
ta fashe da kuka, wai naci amanar ta nasan dai
maganar bata wucea kan matsalarmu dakeba.
Ban san me zance mata ba, domin bani da yanda
zan wanke kaina. Laifi dai nayishi, don Allah shiga
ki bata hakuri, anjima zanxo da Usman neman
tuba gurinta. Cikin hanzari na shige gidan, kan
kujera na sameta cikin tashin hankali nazauna ina
fadin Iya menene? Abban kausar yayi min waya
wai inzo, ya ganki cikin damuwa. Sam idona ya
rufe ban lura da su Kausar ba, sai da naji
muryarta ta ce, wlh Mami ni banibace nafadaba,
Al’amin ne yace yasan yanzu kina can kina kuka,
shine Iya taji tace kukan me? Shine mukayi shiru,
ta ce mu fada nacemashi ni ba ruwana kin hana
mu fada, shine ta tsaremu ta ce, zata zanemu,
shine nace inmun fadamata kada ta fadamaki.
Shine muka fada mata cewa kullum Abban mu in
ya dawo sai ya sa ki kuka, yayi ta zaginki. Na
kama musu kunnuwa, muryar Iya naji ta ce sakar
musu kunne, in ba ke ma kinaso inyi fushi dake
bane. Ni na san cewa wanan ramar taki akwai
bakin ciki a cikinta. Wato dama gadanga cin
amanar da aka bashi yakeyi? Shine ke kika zabi ki
zauna ki hadiye bakin cikin da namiji kina kan
kanuwarki. Sai yanzune kike cikin shekara ashirin
da biyar, amma kika juri wulakanci. To ki sani ni
ba xan yarda ba, ai kodanace in matsala ta taso
kada ki nemeni ban ce haka dan kicutu ba, na
furtane dan in tabbatar kina sonshi badole
nayimakiba. Da naga ta nunfasa sai na ce Iya
yaran nan karya suke yi, dan sabanine
mukasamu kwanan baya, kuma mun sulhunta,
dan Allah Iya kada kiyi fushi da yaya, ko mai ya
wuce. Ta ce yaro da wuya yayi karya. Daidai
lokacin yaya yasake shigowa,Iya ta dube shi Aliyu
ina son ka sani,Sadiya bazata koma gidan ka ba,
dan ba zan yardaba ace har yayanku sun san
cewa kana cutar uwarsu ba. Shi yasa tun farko na
ki batun auran, don nasan halinka. Hankalin yaya
Aliyu yasake tashi, ya curo wayarsa ya kirawo
Usman, ya ce dan Allah Usman kazo gidan Iya
yanzunnan. Ba tare da ya jira Usman me zai ce
ba, ya kashe wayar shi. Sadiya ta tsurawa su
Kausat ido sam bata so suka fada wa Iya wanan
maganarba.badon kar a rabata da mijinta ba, sai
dan bata son Iya tashiga damuwa, musanman
yanzu da ya kasance Iya batada koshin lfy. Iya ta
ce, kun tsaresu da ido ne don sun fadi gaskiya?
Na ce Iya yaran nan fa karya suke yi. Aliyu ya ce
ba karya bane Iya, sai dai sunfada maki a daidai
lokacin da muka shirya na san in Usman yazo zai
gamsar da ke. Wasa wasa har Usman ya shigo Iya
ba ta daina fada ba shi ma shiru ya zauna yayi
har sai da iya ta numfasa, sanan ya shiga bata
hakuri tare da lallashinta. Ya tabbatar mata da
cewa an daidaita, ta ce ina son jin wacce matsala
ce ta taso har yarinya ta kode haka? Sanan in san
wake da matsala? Muka kalli juna ni da yaya,
Usman yace zai fi kyau Iya abin da ya wuce ya
wuce muyi adu’ar Allah ya kare gaba. Ta ce sam
sai fa ta ji menene ya haifar da rashin jituwar
saboda gudun sake faruwar abin nan gaba dan ta
san wane irin mataki zata dauka. Inko ba’afada
minba to sai dai ya rubuta takardar sakin Sadiya
ya bani. Kai Usman ai kasan ko mai, badan son
raina akai auran nanba sabo da gudun haka, don
haka yanzun ma bata baciba ya bar min ‘yata.
Aliyu ya ce Usman fada ma Iya komai duk
hukuncin datayanke a kaina na cancanceshi. Nayi
saurin kallon Usman, ko da wasa bazan bari Iya
tasan ainihin abin da ya faru ba duk da na san
Aliyu dan ta ne amma bazanso tajiba. Muryar
Usman ce ta katseni, wato ainihin abin da ya
faru….Nayu zaraf na katse shi gaskiya Iya ainihin
abin da ya faru laifinane.Na kalli su Kausar kufita
waje. Suka fita nasun kuyar da kai ina tunanin
wane laifi zan dorawa kai na? Dama na ce ne
bana so in sake hai huwa, yara uku sun isheni,
shi ne yaya ya dauki gaba dani. Dakin yayi tsit,
na fada haka ne dan nasan babu abun da iya
take so kamar taga yayan ta suna haihuwa, na
saci kallon ta ni ta ke kallo cikin bacin rai. Ta
soma sabon kuka yanzu Sadiya ke ce baki son hai
huwa? In baki haihuba me zakiyi? Wasu ma son
haihuwar suke da kudi amma ba su samu ba, sai
ke ishashshiya. Na soma hawaye don tausayin
kaina, nazama kyandir in kona kaina don in haska
shi, na ce Iya ki yafe min, domin shi ma yaya
tuni ya yafe min. Na kalli Usman a gabanka aka
yi komai ko? Usman ya lumshe ido, zuciyar shi
cike da mamaki bai taba ganin irin Sadiya ba. Duk
irin cutar da mijinta yayi mata amma ta yarda ta
shafawa kanta kashi, don kurum ta wanke shi. Na
danyi dim dan tsoron kada Usman yatona dan
naga yayi shiru, na ce yaya Usman kuba Iya
hakuri. Iya ce ta daka min tsawa da cewa, kada
ki damu mutane, kuma ina son ki sani wanan ya
zama na karshe, in na sake jin wani laifi
makamancin wanan zaki ga matakin da zan
dauka. Ta kalli yaya Aliyu cikin taushin murya kayi
hakuri Aliyu, inshaAllahu bazata sake kwatanta
haka ba. Yaya Aliyu dai ya kasa koda daga kai,
jikinsa kuma ya mutu.Zan mike ta ce ke zauna
ban gama da ke ba,nakoma na zauna. Ya aliyu
ya zuba min ido, sanan ya kalli Iya. Iya kada ki
damu, ko mai ya wuce ta shi mu tafi. Iya ta ce
kuje zatazo yanzun, suna fita Iya tace, na san
cewa abin da kika fada ba shi bane ainihin
matsalar ku ba, kilama kin fada ne dan ki wanke
shi. Amna in haka ne da gaske ina mai yi maki
nasiha ki jitsoron Allah, ki bi abin da mijinkike so,
duk mutum na kwarai ba zai ki yin murna da
kyautar da Allah yayi mashi ba. Koma menene
zan ci gaba da yi maku adu’a, tashi kije. Na mike
zaraf ta re da cewa, to Iya nagode, insha Allahu
bazaki sake jin kan mu ba. Ta ce kuma kar inji kin
daki yaran nan, gashi a ban za kin sa suna jin
haushin mahaifin su, har suna fadin basu son
yadawo. Na ce bazan masu komaiba. nakirasu
muka fita.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Usman ya kalli Aliyu bayan sunfita ya ce aboki in
har ka sake cin zarafin matarka hakika Allah
bazai kyalekaba. Dubi yanda ta dorawa kanta laifi
don ta wanke ka. Aliyu ya ce, nikaina baka ga na
kasa maganaba? Lallai Allah ya taimakeni Sadiya
ta taimakeni, wlh kaji na rantse maka yau da Iya
ta ji ko mai na kade, ba zankara kima a
Idontaba. Sannan sai ta raba ni da matata.
Usman ya ce, to sai kayi mata adalci tunda abin
yazo da sauki. Da muka fito duk suka nufo gun
mu Usman ya ce Sadiya Allah ya shi maki
albarka,da’a ce mata da yawa suna da hali irin
naki, na tabbata da aure da yawa ba zai mutuba.
Nakalli Aliyu, shima ni yake kallo. Ya ce my choice
na gode, ina sake rokonki afuwa ki yafe min. Na
ce ya wuce. Na tasa yarana muka tafi gida
nazaunar dasu,Kausar nace yanzu kun kyauta
kenan da kuka sa Iya kuka? Kausar ta ce Momy
Al’amin ne. Na ce to kar ku sake, Al’amin ya ce,
momy ba zan sake ba.
Ko daran ranar Aliyu banda hakuri babu abinda
yake bani, duk ba wannan ce matsalata ba, ya ya
za’a kare da batun (H.I.V) da kuma batun
yarinyar nan? Don haka na waiwayo na dube shi
daga inda nike kwance, shima rigingine yake
idanunsa suna kallon sama. Tsakaninmu mutum
guda zai iya kwanciya tsakaninmu, na ce ‘ Yaya!
Bai amsa ba, na daga murya ‘Yaya’ shru, da
alamu tunaninsaya tsawaita. Don haka na mike
na kunna fitilar dakin,haske ya mamaye ko
ina,na tsura mashi ido cikin faduwar gaba.
Nagirgiza da ganin hawaye suna gudu layi bibbiyu
daga idananun Yaya daya yamiko zuwa kumatu.
Yayin da dayan ya bi gefen ido. A fili nafurta’Inna
lillahi wa inna ilaihir raji’un! Yaya! Na kira shi tare
d zama kusa dashi na kwantar d kaina a kirjinshi,
kunnuwana suna jiyo yanda yake ta kokawa d
kukanshi a kirjin. Ina zaton yana kokowar danne
kukan ne, yayinda shi kuma kukan ke ta yunkurin
fitowa. Da sauri na dora tafin hannuna a kirjinshi
ina ta shafa kirjin, wai nufina in taya shi lallashin
kukan. Bakina ya soma fadin ‘Haba Yayana, me
kuma ya faru? Tuni na yafe abinda kayimin,
namaka alkawarin rayuwar da tafi wadda muka yi
baya dadi. Sai naji hannunsa a gadon bayana, ya
damki rigata d dan karfi alamun har yanxu yna
ckin cikin kunci, muryarshi sarke cikin rawa irinta
mai kukan baqin ciki. Ya ce, Sadiya ba anan
matsalar take ba, Sadiya baqin cikina ciwon in ya
kasance ina da ciwo…” kasa karasawa yyi don
kukan da ke son subuce masa. Nace Yaya ko
kana da ciwon nan zan zauna d kai,ko banidashi
zan yarda ka sa min. Nima kukan ne ya kufce
min,cikin kukan na ce ‘Yaya zan zaunada kai haka
ina sonka.” Sosai ya rungumeni tsam ”Sadiya ba
zan cuce ki ba, bayan Allahya tsare ki,nikuma
nine nacuci kaina, domin duk wanda ya bar
dokar Ubangijinshi ya dauki son zuciyarshi, ya
saki koyarwar Abul Kasim, Manzonmu mai tsira
da aminci, ya bi ta Yahudu d Nasara to bako
shakka karshenshi nadama da kuma danasani,
lokacin da ba su da amfani. Sadiya lokacin da
shaidaniyar yarinyar ta ziyarce ni da ban bi son
shaidaniyar zuciyata ba duk da haka bata faruba.
Ba ina kukan ciwon da kila zai zama ina da shi
bane, ba ina kukan ci gaba da rayuwata ba ne
ina kukan yanda zan bar ki da wahalar jinyata da
dawainiyar yarana. Sannan kukan abinda da zan
tarar a cikin kabarina ban san me zan gaya wa
Ubangijinaba, Yayi shru cikin shassheka, nima
kukana ya qaru. Nace, Yaya inshaAllahu
bakadashi, ka ci gaba da neman gafarar
Ubangijinka, Allah mai amsar tuban bayinshi
ne.Ya yunkura ya tada mu zaune ya dago fuskata
muna kallon juna ido cikin ido,ya ce ‘Sadiya ban
makara ba ko? Na girgiza kai, Baka makara ba
Yaya. Ka daina tunanin cewa zaka mutu ka bar
ni,insha Allahu kai ne wakilin gawata,kai zaka
fara binne ni Yaya. Ya rungume ni tsam a kirjinsa
tamkar ya buda kirjin ya saka ni. ‘Ina sonki
Sadiya,ina son yarana,ina son iya. Amma haka
nan in ta kasance zan barku…… Wayarshi ta
katse maganarsa, tamkar kada ya dauka don ji
yake komai ma ya tsara shi rayuwarshi ta kare.
Ni ce na dauko wayar na mika masa, Adewalene
direbansa na can, tamkar kada ya daga na
ce’Yaya ka amsa mana.’ A kasalance ya yi
sallama,Ade ya amsa sannan ya ce, ‘Oga dama
madam ce a Asibiti ba lafiya,shine take tasa aka
dauki lambata a ka kira ni. Me? Naji Aliyu ya
furta da karfi, ‘Mujidat ba ta da lafiya?? Nima
gabana ya yi wata mummunar faduwa,tamkar ni
ce na daga wayar. Idanuna waje ni ke tambayr
me ya same ta? Aliyu ma da ya rasa me zai fada
sai ya maimaita tambayar da nayi. ‘Adewale
meyasame ta? A can bangaren Adewale ya amsa
da cewa, shi fa bai sani ba,amma ga ta bari ya
bata. Aliyu cikin daga murya ya ce,kada ka
bata,bana son jin muryarta,macuciya. Na yi
saurin fadin ‘Yaya a bata wayar mu ji daga
bakinta, da gaske tana da ciwon? Shiru Yaya yayi
yana kallona,hankali tashe bayn ya katse wayar.
Na ce Yaya don Alla ka kira a bata mu ji, ba don
son ranshi ya kira ba,sai don na nace da cewa ya
yi hakan.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
A handsfree ya saka ta, Ade ya daga ya ce
bata,murya can kasa ta ce ‘Hello’ ya katseta da
cewa,’Kiran ubanme kikace amin? Na fada miki
bani bake, kuma ina Allah ya isa da sanin da na
yi miki,macuciya.Dama kin san cewa kina da
(H.I.V) shi ne ki ka like min sabida ki cutar da ni
da Iyalina? Wani kara ta saki mai karfi tana fadin
‘A’a, a’a ni ba ni d (H.I.V) sai dai in kai ne kasa
min. Muka kalli juna ni da shi, ya ce ‘Yanzun
wane ciwo ki keyi dazakice baki da (H.I.V)? Tace,
‘Ina dauke da cikinka ne yana wahalar da
ni,amma bani da (H.I.V)….’ Ya katseta da karfi
Cikin tsawa cikin masifa take fadin ‘Kada ka sake
zagin ubana,wannan cikin naka ne ban taba
yarda na bi wani ba tare da abin karyar cuta ko
ciki ba sai kai daya danike So. In ma (H.I.V) ne
kaika samin kamar yanda ka sa min wannan
cikin,kuma ina sonka sani ba zan taba cire shi
ba,zan haifi dan soyayya,zan zo har garinku gurin
danginka don su san kana da da’ ko ‘ya da ni.
Haka nan masoyiyarka da ka yi min wulaqanci
sabida ita,ita ma ya dace mu san juna. Duk da
tsawar da yake daka mata bata yi shuruba,sai
data kai aya. Ni kam baqin ciki ya hana ni
magana,sai hawaye. Na mike zan fita,ya riko min
hannu tare da finciko ni na fado jikinshi,ya kashe
wayar yana fadin. ‘Haba Sadiya, ina ce murna
zamu yi tunda ba ciwon gare ta ba? Na mishi
wani kallo tamkar in hau shi da duka,cikin zafin
rai na ce ‘Ba gara ciwon ba da cikin da ka yi
mata? Yanzun me ka shirya fadawa danginka in
ta zo musu da da’? Ya ce, ki barta bata ma isa ba
ne,taje can ta nemi Uban cikinta. Ya tausasa
murya. ‘Na rantse miki bazan karbi cikinba,
kibarta zan nemi transfer in bar garin ba
shienanba. Yayi ta lallashina ina kuka, ya yi ta
tsara min zantuka har nayi shiru,amma sam naki
magana, ga ciwon kai tamkar zai rabe. Ya jawo ni
jikinshi ‘Ba kincekin yafe min ba? Na dafe kaina
tare da fadin ‘Wash Allah na.. A rude ya
tambayeta ”kan ki na ciwo ne? Na daga kai
alamun ‘Eh”ya kawo min panadol ya ba ni na
sha. Haka ya yi ta ririta ni da lallashi tare da
maganganun kwantar da hankali har bacci
yadaukeni. Shi kuma ya mike ya shiga sintirin kai
kawo dakin, daga bisa niya dau ki wayar shi ya
nufi can harabar gidan, dan kada ya tashi wani
daga cikin iyalin sa. Yanzu ya fi shakkar yaran sa,
domin ya fahimta lallai in yayi wasa zai sha
mamaki dasu. Layin mujidat ya kira, ringing na
uku ta dauka Aliyu yace, na kirakine in gargadeki,
kiyihanzarin fita harkata, kuma ki nemi uban
cikinki, ni ba nine uban sa ba. Dama karuwa tana
da miji ne da har zata sami uban da? Ta soma
kuka, tana cewa kaine ubansa, kabidani ta lalama
in ba haka ba zaka ga yanda ake iskanci. Kana
kirana karuwa kai ya sunan ka? Gara ma kazo
cikin satin nan in ba haka ba za ka ganni a
Kaduna. Aliyu ya ce dole zan dawo tinda gurin
aiki nane, amma ki sani babuke, zai fi maki sauki
ki zubar da wanan cikin tunda baki tuna
ubansaba… Mujidat ta katse shi ina zaton baka
sanni ba ne shine yasa ka ce haka, amma zan
nuna maka kalata. Kuma bazan zubar da cikin
ba, wanan cikin shine ya zo min dai dai lokacin
da nake bukatar shi zai tai maka min sosai.
Wanan cikin shine zai hana rabuwar mu ni da
kai, kasani mun hadu har abada . Ta katse
wayar.
Ranar da zai koma tamkar inyi me don ta kai ci,
nasan dole sai sun hadu da yarinyar nan ga ciki.
Shi kanshi tunda akayi batun cikin ban sake ko
dariya ba, ya lura da hakan. Da zai tafi sai min
dadin baki yake gaskiya ni fa Abban kausar gara
min ace daga ni har kai muna da ciwon kan
jamau da batun cikin. Nan ya rike min hannu,
don Allah ki saki ranki ki aje maganar yarinyar
nan a gefe, ke kiji a rankima an
shafe babin ta a bayan kasa, kinji don Allah. Na
ce hum! Shi ke nan Allah ya saukeka lafiya. Ko da
ya sauka yana ta kokarin yawan kirana da
sauransu. Nakula sosai yana son shikam lallai sai
mun koma tamkar da, nima dai ina ta kokartawa
don ganin anyi hakan duk da ina tsoron mai zai
biyo baya kan batun yarinyar da cikinta.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Aliyu da yake zaune a bayan motar sa ya dubi
Ade wale da ke tuki ya ce masa kasan gidan da
Mujidat take? Ade wale ya ce a a sai dai gidan
yarta yasa ni inda ya taba kaita sai ko asibitin da
ta kwanta. Aliyu ya daga waya ya danna mata
kira, har ta katse bata daga ba. Ya shareta da
farko amma sai kuma ya tuna yana son kwarai su
tattauna abu mai mahman ci. Don haka sai ya
sake daga wayar da nufin kiranta, amma sai ga
kiranta ya shigo, cikin sauri ya daga. Ta ce kamar
kana jiran kira na? Aliyu ya ce ko daya ina dai
yunkurin kiranki ne. Tayi yar dariya. Ashe dai ka
damudani? Yace ke bankiraki don naji salon
zancekiba, inaxan same ki? Ta sake yin yar dariya
da ya tsana a yanzun, ka bari ni nasan indazan
sameka,tunda ka shigo garinnan nasami labarin
zuwanka, sanan ka manta nice na kiraka ba kai
ne ka kirani ba da har zaka ce bakakirani dan kaji
salobane. Ya katse ta, ki fada min inda xan same
ki yanzu nace,tasake yin yar shewa tare da fadin
ashe dai har yanzu kana tare dani, ni nasan
tunda ka shigo dole ka neme ni ko dan cikinka.
Cikin fushi ya ce, kar ki tsamma ci cewa haduwar
mu zata haifa maki da mai ido, ko kusa ganina
bazai farantamaki rai…. Ta katse shi da cewa, in
ji wa? Ai ko zaka kashe ni ganinka ya fiye mun
komai farin ciki ko kasan ina sonka fiye da
mahaifana? tayaya zan kasa farin cikinganinka?
cikinhaushi yace Amma kin yi asara tunda baza ki
fadin in da kike ba bari in koma gida Cikin sauri
tace ina Hotel din Hamada Daki na sahashida,ka
iso lfy masoyina Tsaki yaja sannan ya katse layin
sannan ya kalli direba muje Hotel din Hamada ko
cikin harabar hotel bai shiga ba Aliyu yace ya
tsaya ya sake kiran layin ta ta daga tare da fadin
bude ka shigo mai sona yace ke shashasha fito
ina can bakin gate sannan ya katse bai tsaya jin
me xata ce ba sanye da dogowar bakar jallabiya
da dan kwalinta sai takalmi baki mara tudu sam
yanxun baya ko son ganinta don haka ya daure
fuska tamkar baitaba dariya ba sam,yanxu baya
ko son ganinta don haka ya daure fuska tamkar
in ya bude baki xai fito da wuta don hada rai,
tana isowa saitinsa ta nufa don tasan gurin
xamansa yasauke gilashin tana kallonshi gabata
ya fadi amma sai ta dake saboda iya bariki tace
maigidana ina son in ganka cikin iri kamewar
gaskiya kada kace aikinka kafito mushiga ciki ya yi
mata kallon banxa tamkar yaga kashi sannan
yace shiga mota muje tace ina? tace. sai kinji?
Tace bari in dauko jakata yace (cikin tsawa ) in kin
koma ciki ni kuma zan fi cikin sauri ta zagaya ta
bude mota tana fadin gida zamu je kenan? ko
tanka ta bai yi ba yace Adewale sai da ya harba
motar kan titi sannan yace Oga. gida zamuje?
Aliyu yace babban asibitin garin nan zamuje ta
zaro idoda sauri tace yin me? ku tsaya in sauka
bazanbikuba ,tasoma lalube zata bude kofa Aliyu
yace bazan hanaki ki fita ba amma ki sani in ki
fado kan titin nan ba lallai ne ki rayu ba wanda
hakan ba zai dameniba yan uwanki ne za su yi
rashi,ta dan shiru tana tunanin me zatayi don
kuwa itakam bazata taba yarda a cire mata
cikinnanba Don tasan shi ne kadai abinda ya rage
mata wanda zata rike Aliyu da shi dole ya
saurare ta ta kalleshi nifa bana son ka kai ni a
cire min ciki ya dubeta. ina ruwana da cikinki
bashi ne matsalata ba ta sauke ajiyar zuciya tare
da jingina kanta a jikin kujerar mota ta tabbata
gaske ne ba abinda zai kaisu kenanba ta sake
kallon shi me zamu je yi ya dauki wayarshi yana
naiman wani layi ya karata a kunne tare da fadin
in mun je kyaji,Suna shiga dakin ganin likitan
wanda ya riga ya shaida masa yana tafe, ya
baiwa likitan hannu suka gaisa. ‘Yan sanda sukan
saba da likitoci sbd yanayin ayyukansu, don haka
Aliyu yasan likitoci da dama a Asibitoci daban
daban. Ya nuna Mujidat gata nan, Mujidat ta
soma zare ido, sai dai ganin Likitan ya dauko
kayan gwajin (H.I.V), sai ta kwantar da hankalinta
dan tasan bata da shi din amma Likitan ya ba da
lokaci wata uku nan gaba su dawon a sake
gwadawa, ya umarta shima a gwada shi.
Sakamakon dai duk daya ne, babu, Aliyu
zuciyarshi yanzun ta nutsu d cewa bashi da
(H.I.V) ya yi wa liktan godiya sannan suka yi
sallama. Suna fitowa ya shiga motarshi. Direba
zai tada kenan tazo ta bude zata shiga. Aliyu ya
ce, (cikin tsawa) ‘karki shigo min mota, sannan
banida buqatar sake ganinki a rayuwata.’ Ta ce,
‘Labari kake yi’. Ta dafa cikinta, ‘in kai danka
ina? Kai ba ka san bala’ina ba ko? Za ka sha
mamakin abinda da zai biyo baya in har ka ki
tsayawa mu sasanta, Mujidat kawai ka sani
amma ba ka san halinta ba. ya daka ma Adewale
tsawa, ‘Muje mana, ‘Take ya figi mota suka yi
gaba in da har Mujidat ta ku san faduwa, kofar
motar ta rufe gam! Suka bar ta a nan. Ta bi
motar da kallo cikin kunan rai, a fili ta ce
‘Wannan bai sanni ba, bai san yana cin
albarkacin so bane? Amma zai san ya kirama
kanshi ruwa.’ ta nufi titi don hawa acaba.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tun lokacin d muka samu sabani d Yaya
Aliyu,kusan ko yaushe dakin yarana ni ke kwana
don samun sauqin wasu abubuwan, ko na ce
tunane tunane. Yau ma niyyata kenan inna gama
can zani cikinsu in kwanta, zan fita dakin kenan
wayata ta soma ruri. Na koma kan gado na
kwanta sannan na daga tare da yina sallama. Ya
Aliyu ya amsa,sannan ya ce ‘My choice
Alhamdulillah.’Na ce, ‘Shin ne abin godiya. Ya ce,
‘Ina mana murna gaske yarinyar nan ba ta da
(H.I.V). Na lumshe ido cikin jin dadi,amma sai na
tuno d cikinta, na ce ‘To cikin fa? Ya ce, ‘Ina
ruwana d cikinta, ban bi ta kanshi ba, don ba
matsalata ba ce,’ Nace, ‘Matsalarka ce, tunda
kwanka ne. Babu yadda za’a yi mace ita daya ta
dauki ciki. ‘Raina ya soma zafi, ya ce ‘Ni kadai
nayi hulda d ita?? cikin bacin rai na ce ‘Amma kai
ka ajeta a gida.’ Kuka ya subuce min, sai na
kashewayar nayi jifa da ita na ci gaba da kuka.
Inaji yana ta sake kira amma na qi dagawa, inna
tuno wai Aliyu shi ne ya yi ma wata ciki, abin nan
yana soya min rai. Duk ranar d aka kawo mana
dan me zai fada ma duniya? Mezai fada ma
zuri’arshi? Musamman yaranshi masu wayon
tsiya? Banji bude kofa ba, sai dai muryar kausar
naji tana cewa, ‘Momi wanene? Da sauri na share
hawayena ta ce, ‘Momi Abbanmu ba ya ce kun
daina fada ba? ‘Na ce, ‘Jeki dauko min magani,
kaina ke ciwo na kasa tashi ne. Da gudu ta fita,
saiga ta da shi har da ruwa. Ina sha ne naji
sakonni suna ta shigowa cikin wayata,na bata
kofin na ce ‘Kije ku kwanta, kiyi muku addu’a zan
yi waya da Abbanku. Ta ce, ‘Momi kin fasa yi
mana tarihin d ki ka ce za ki yi mana na rayuwar
Manzon Allah? Na ce,’kin ga kaina na ciwo,sai
gobe.
My choice ki bari mu sake daidaita kanmu, ki bari
mu saita rayuwarmu, ki amince da ban hakurina.
Tsaki naja sannan na duba dayan sakon.
Kin yi alkawarin cewa kin yafe min, kamata yayi
ki mance kmai,ina sonki my choice, kece
rayuwata.
Na sake jan tsaki a fili na ce, ‘Kamar gaske. Wani
sakon ya sake shigowa.
Don darajar Allah da girmansa d darajar lokacind
muka kasance a baya, d martabar soyayyarmu,ki
amice da ban haqurina. Amicewarki kurum shine
daga wayata , xan kira ki yanxun . Dagawarki
itace zata tabbatar min cewa kin hkr.
Na ajiye wayar tare da yin rigingine na
kumaruntse idona, matsalata ina da rauni da
sanyin zuciya, bugu da kari ina son mijina.Bana
jure in wulakantahi, tausayinshi na daga cikin
abinda ke sa in kauda kai ga abubuwan da yake
min…ringing din wayarsane ya dawo dani
tunanina. Na dauki wayar tare da yin sallama
cikin makoshi , yace”ngd da daga wayata, yanxun
na yarda kin yafe min.Inason mu koma kamar
da, yanxun ki fada min abinda kikeson muyi.
Nace kamar me? Yace wlh bana son bacin ranki
ne, shine nake son ki tsara mana yanda zamu
shimfida sabuwar rayuwa, wadda baza ta katse
ba.”Nace kamar gaske, kila sai kasa na soma
farin ciki daga baya ka canza min. Allah sarki
Sadiya sarkin son soyayya, sai gani ina ‘yar
dariya, nace duk lkcn da ka so. Shima yayi ‘yar
dariya.Inzo gobe? Nace koh yanxu ma ka zo.
Yace insha Allahu ranar jumma’a xan taho, roko
nike ma Allah yasa suyi min transfer zuwa
arewa.Nace amin yace ina yarana? Nace suna
dakinsu sunyi bacci. Yace, to bari in amsa waya
xan sake kiranki.Ba’a fi minti dayaba ya sake
kirana yace zan fita barayi ne a cikin wani kauye,
shi ne aka kira ni yanxun. Nace Allah ya tsare.
Nayi birgima a kan gado, zuciyata fes. Wata
zuciyar tace lallai ke dai sakara ce, duk irin
abinda mutumin nan ya kunsa miki shinecikin
mintin da bai kai 10 ba har kin manta?Nadan yi
tsai ina son inyi tunani, tabbas xuciyata
shagalalliya ce ma’abociyar son a sota, da zaran
abin son ta ya fuskance ta sai ta bude da yawa
ta shiga cikin farinciki.Idan abin sonta ya juya
mata baya sai ta shiga kunci ta tsuke , ta dinga
zafi. Nayi murmushi tare da rungume filo, a fili
na furta.Allah kakauda shedan tsakanina da
mijina. kullum yanxn ina cikin farinciki sbd xan
kira yaya a lkcn dana so, kuma shima yana
kirana, sannn ga hirar kwantar da hankali tare da
ban baki da yake min kullum.Tun ranar Alhamis
naje gidan kitso na kuma biya gurin mai zana
fulawr dayis tayi mana har da Kausar da Mama.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tun safiya Jumua’a na hana kaina sakat da
ayyuka. Funkasau na kwaba sai kuma farar
shinkafa, nayi kunun zaki na sayo fura.Duk
abinda nasan yanaso haka na tanade shi, a
wayarmu ta karshe baifi saura minti hamsin ya
isoba don haka na feshe yara nima na saka kayan
da bai sanni dasu ba, a sunan Aisha na dinka su,
atamfa ce blue mai ratsin yellow. Ina jin
kwankwasa gida nace su Kausar Abbanku,
maimakon su biyo ni kamar yanda da can
mukeyi, sai naga duk sun tsaya.Kausar ma hade
rai tayi, na kamo hannunta,kuzo muje mu taro
shi. Biyo ni sukayi , na bude gida jan gwarzo na
yau cikin kakinsa yake, ya aje jaka muka rungume
juna cikin murna da doki.Muka kalli yaranmu
lamarin ya zame musu tamkar sabon abu.Kausar
ma rufe fuska tayia lamun kunya.Al’ameen ne
ma naga yana tadariya. Muka kalli juna ni dashi ,
ya sakeni yaje ya rungumi Kausar, sannan
Al’ameen da ya aje shi ne ya dauki Maama ni
kuma na kwashi kayansa muka nufi ciki.Tamkar
da ya basu leda dauke da kayan ciye ciye tasu
tsarabar, nan muka barsu faloya shiga wanka,
kamar da nice na taimaka masa yayi wanka.Tsaf
ya shirya muka fito gurin cin abinci, yanda yaran
suka ganmu har sun soma sakin jiki, abinci kam
ya rasa da wanne xai soma.Ya kamo hannuna
yana yabon lallena, kausar dake can gefe tace
Abba nima kaga nawa, harda Mama akayi mana .
Yace , iye! ‘Yan gata kunyi kyau yarana, nayi kasa
da murya ina cewa Kausar fa hankalinta yana
kanmu. Yace, duk zatonta yau ma rigimar
zamuyi? Nace wannan ya zama tarihi. Muka sa
dariya, daya kammala ya mike.Dauko hijabinki
kuzo mu fita. Yara suka hau tsalle muna gaba ni
da yaya, su kam suna baya.Gidan iya muka soma
zuwa, muka bata tsarabarta. Sai gidan Usman
nan ne ma muka dan dade.Sun kama hirar siyasa
ni kuma muka kulle da Anty Abida cikin daki,
shawarwari tayi ta bani kan cewa kada in sake
inyi fushi ko in dauki gaba da mijina don yana
bin mata.Yin haka zaisa ya kara zakewa.tace kin
ba shi dama kenan, amma in kika jawo shi kika
ninka abinda kike masa ada, kika hada da addu’a
sai kiga komai ya daidata. Nace bakisan wani
abuba Anty, yanzun yarinyar tana da ciki, ko
Usman bai fadawaba, abinda ke batamin rai
kenan, kuma tasha alwashin sai ta haife dan
cikinta ta kawo shi.Anty Abida tayi salati tare da
rike baki tace lallai akwai matsala. Nace nayi nayi
ya tsayamuyi shawara ni da shi amma yaki yace
in bar zancen. Tace shikenan tunda baya son
zancen ki kyale shi, Allah ya rufa asiri, nace amin.
Daga nan yayi ta yawo damu supermarket da
stores kalakala. Mun kwaso kayan ciye,ne da
suturu da takalma, ni kama har da mayafai da
jaka. Gsky ranar ya kashe mana kudi, haka muka
shigo gida nikiniki da kaya, yarana nadade sosai
bangan su cikin farin ciki kamar yau ba. Lallai
rashin jituwar iyaye ba karamin shafar rayuwar
yara takeyiba. Don Allah iyaye in wata matsala ta
gifto muku ku daina sa’insa gaban ‘ya’yanku, don
gudun lalacewar tarbiyyarsu, tare da jefa rayuwar
su cikin rudani,Tun daga ranar dayace min yana
tafe nayi ta hada abubuwana ina sha , yanxun
ma zumata na samu na kada kwaina na hada na
shanye.Sabon wanka nayi na saka sabuwar rigar
baccin daya zaba in a fitar da mukayi, yanxun na
kama gashina shi kam yana falo yana kallon
labarai a tashar Aljazeera,Yara tuni sunyi bacci,
ban fito ba nima sai nabi kan gadona na fada
tsakiyar gadon nayi kwanciyata.Da zai yiwu in
bada labarin daran ranar kila da nan zan kare,
domin ya shiga sahun tarihin da ba zai gogu ba a
zukatanmu.A cewar yaya, daran ya dara na
farkonmu.Da safe mun tashi tamkar sabon aure,
cikin kwalliya muke aiki tare dashi a kicin.
kwanaki biyun da Yaya ya yi sai da na rubuta su
cikin dan kundin adana mahimman sirrikana. Da
zai tafi har kuka nayi. Allah sarki rayuwa,mun
koma tamkar da har mun fi da kyau,rayuwar
aure d zaman lafiya gami d soyayya akwai dadi.
Tuni Aliyu ya mantar da ni abinda ya faru a baya.
Kuma ko na tuna bana jin haushi,don na dauke
shi matsayin jarabta. Sai dai fa duk lokacin da na
tuna cewa wata tana can dauke d cikinsa ina
tsorata da abinda zai biyo baya. Kwatsam sai ga
shi anyo ma Yaya transfer zuwa Abuja.mun yi
murna don ganin Abuja ni ke tamkar kaduna,
tunda ya koma nan ba ya jimawa bai zo ba. Wata
rana har can Abujar ya kan tafi da mu muyi
hutun karshen mako. Rayuwa dai ta jin dadi
muna ciki. Kwatsam wani yammacin ranar Talata
ina tsakar gida ina kwashe shanyar kayan
makarantar yara da na wanke. A jikina ina sanye
da doguwar riga mai hade da hula blue da ratsin
fari,sai naji ana buga min gida, na nufi kofar ina
tambayr kaina ko wa ye?? Ina budewa muka
hada ido da ita, gabana yayi mummunar faduwa.
Ina zaton ko cikin duhu na ganta zan gane ta,
bare a haske,domin na sha ganin hotunanta cikin
facebook, tana sanye d doguwar riga ja hade d
mayafinta. Sannan tana janye d akwatinta, ga
wata ta rataya a kafada. Na dake na sake
dubanta. ‘Malama daga ina? Kuma wa ki ke
nema? Ta ce, ‘Nan ne gidan Aliyu Tukur jami’in
dan sanda? Na ce, eh nan ne. ‘Sai naga ta turo
kai, na ce ‘Ba ki minbayani ba kina kokarin shige
min gida. Tayi min wani kallo sama da kasa, ‘Ni
bakuwarshi ce, Allah yasa yana gari? Na maida
kofar na rufe,tare d cewa ‘Bayanan yana Abuja,
lafiya? Ta nufi ciki. Zo ki nuna min inda zan
zauna, a gajiye nike, don na wahala kafin na
gano gidan. Falo na sauketa duk da tafasar da
zuciyata ke yi, amma na danne har ruwa na
bata. Sannan na zauna na kalle ta. ‘Baiwar Allah
daga ina ki ka zo neman Maigidana? Ta gyara
zama ‘Ciki ya yimin,ta fada a gadarance ba tare
d jin wani nauyi ko shakka ba, ni kuwa duk da
cewa nasan batun sai da gabana ya fadi da jin
furucinta. nace, ‘Ciki? Ta ce ‘Eh, shi ne don
wulaqanci ya ci moriyar ganga zai yada
kwauronta? Bai isa ba. Sai yasan ya taba annoba.
Raina ya soma daukan zafi a gurin,na daga waya
na kira shi,ringing din farko ya daga tamkar yana
zaman jiran kirana ne. Ya ce,’Ya ya dai my
choice? Don in nuna ma Mujidat ban damu ba,
na ce ‘Sweety kayi baquwane,da sauri ya ce,
Daga ina? Na kalleta tamkar ban san ds batunta
da shiba, na ce ya ce daga ina? Ta miqo hannu
‘Ba ni wayar. ‘Nayi ‘Yar dariya. Ke ba ki d wayar
ne? Fadi kawai daga inda kike in sanar dashi.
Cikin son ta tura min haushi ta ce, fada masa
wadda yayi ma ciki ce. Kalmar tana dukan kirjina
in ta furta, amma na dake na ce ‘Wai wadda ka
yi ma ciki ce. Na karasa zance da dariyar bakin
ciki. Da sauri ya ce, ‘Mujidat? Subhnllhi! Lallai
wannan ‘yar iskar tana son jaza min bala’i ne. Ta
ya ya ta gano gidana? Na tabe baki tare da cewa,
‘Oho’ ya ce, ‘Kai wannan akwai ‘Yar iskar yarinya.
Sadiya don Allah kiyi hakuri kinji? Zan taho yau
din nan kmai dare, amma yanzun ya ya za’a yi?
Na ce, kaika san yanda za ka yi da ita. ‘Ya dan yi
shiru yana nazari, duk a rude yake,ya ce, ‘Sadiya.
Na ce, ‘Na’am, ‘Ya ce, ‘Kuna tare ne yanzun
haka? Na ce,’Eh. Ya ce, shiga daki muyi magana.
Na ce, To. Na miqe na nufi daki. Na shige Toilet
na rufe, sannan na ce ‘Ina jin ka. Ya ce, ‘Sadiya
don Allah kiyi hakuri kwakwalwata ta toshe, ki
buda min ita ya ya za a yi yanzun? Raina bace
yake matuka, na ce ‘Lokacin da za ka yi sabonka
ka nemi shawarata? Don haka sai ka nemi
shedanin daya hure maka kunne ya sa ka a
hanyar da za ka warware matsalar. Ya ce, Sadiya
duk ba wannan zancen ba, yara na gida tayi
magana? Na ce, ‘A’a suna islamiyya. Ya ce, ‘Ok,
yanzu yaya za ayi? Na ce, ‘Wallahi ban sani ba, ni
dai bani da dakin da zata kwana sai dai in
dakinka. Ya ce, ‘Zan taho yanzun nan zansa
jami’an tsaro su kulle min ita. Na ce, ‘Kana ganin
wannan mafita ce? Yarinyar nan irin ‘yan iskan
nan ne ma su tutiya da iskancinsu. A shirye take
d ta shelanta ma duniya ita farkarka ce, kuma
tana da cikinka.ka shirya zubewar mutuncinka? In
ka shirya ka zo ka bi ta d zafii in ko kana son
tsira d dan ragowar mutuncinka,to koka tabbata
za ka bi ta ne da lalama ka kuma yi mata adalci
tunda lokacin daza ku yi shedanar ba ka
juyamata baya ba. Na kashe wayar tamkar in yi
kuka, amma sai na fasa don bana son wannan
Mujidat din ta fahimci abinda ta zo dashi ya daga
hankalina. Ko kuwa ya dadani da kasa,don na
lura ‘Yar bariki ce.nasame ta inda na barta sai
dai yanzun ta dan kwanta akan kujerar. Na dube
ta ‘ya ce ki jira shi yanzun zai baro Abuja,kina
buqatar wani abu yanzun? Ta ce, ‘A’a bana jin
yunwa na ci abinci a gidan cin abinci. Na wuce na
ci gabad aikina sai dai kunci da takaici a zuciyata
ba a magana.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Shida daidai yara suka dawo Islamiya kallonta
suka dinga yi sannan suka gaishe ta. Ta ce yara
masu kyau,ina kausar?Ta ce, ‘Gani. Mujidat ta
ce, Yar lelen Babanta duk ya fi ambatar ta cikin
yaran. Kai ne Al’ameen? Ya ce, ‘Eh. Ta ce, ‘Ka yi
min kyau, kana kama da babanka sai ka shiga
raina. Ta dubi Mama ta yatsina fuska, ‘Ke ce mai
kama d mamnki ko? Sunfi ki kyau, Allah yasa
babyna ya yi kama da…………..” Da karfi na
daka mata tsawa ‘Ke! Mahaukaciyace? ‘Na kalli
su kausar, ku je dakin ku ku cire kaya ina zuwa.
Na dubeta bayan shigarsu daki,mekike shirin
fadawa yarana? Kina so ki fada musu kina da ciki
da babansu? Ta ‘Eh ai dole su sani ko da ban
fada musuba, domin a gidan nan zan haife shi.
Na runtse ido don baqin ciki na bude tare da
furzar da takaicina ta baki, na ce ba zan hanaki
ki haihu a gidan nan b, sai dai zan gargade ki kar
ki sake ki fadawa yarana maganar data fi karfin
tunaninsu, kin gane? Ta yi ‘Yar dariya,sannan ta
ce, Bani da magana dake bare ki sa min doka,
mijinki nake jira. Haushi ya turnikeni har na kasa
tsaida shi na ce, ‘Mijina fa nawa ne kar ki ga na
miki tarbar mutunci ki za ta shakka ce, in na ga
dama ba ki ganin mijinnawa, sannan dole ki bar
min gidana. Ta saka dariya, sannan ta debi
kafafunta ta zuba kan kujerata kuma kallona
sama d kasa,sannan ta ce………zandakata anan,
zakuji zarar Allah yanufa..
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347

1 2 3 4 5Next page

Leave a Reply

Back to top button