DARAJAR YAYANA PART 3

DARAJAR YAYANA PART 3

Darajar Yayana3-03
Posted by ANaM Dorayi on 12:12 AM, 04-Apr-16
Under: DARAJAR ‘YA’YANA
_________________NA ___________HALIMA K/MASHI Assalamu’alaikum,akaro na barkatai gani na dawo domin kawo muku cigaban labarinmu ,fatan kuna sane da inda muka tsaya. Yayi shiru. Na ce Hello, kana jina? Eh, kin fadawa Iya ne? Na ce, nanmuka amshi haihuwar tare, Kasan cewa taso ta gano cewa danka ne? Dan yaron yayi kama da kai fiye da duk yaran gidan nan.Da karfi yace Haba dai! Wlh, yaushe zaka zo? Yayi dan tsaki, gaskiya bani da ranar zuwa, zan turo miki kudi kiyi duk abinda ya dace. Nace, zuwan ka yana da muhimmanci, sabida Mujidat zata iya tana komaifa, inbata gankaba. Ya ce, to zan zo kafin suna inkuma dawo Gurin aikina. Nace to saikazo. Na kira auntyAbida na fada mata, haka ma Aisha kawata.Makota duk suna ta shigowa Barka. Su kausar ma nasa sunje sunga baby,na fada musu cewa kaninsune, suna ta murna har da kausar. Aisha ranar datazo barka tana daukan yaron tace, kai Sadiya yaron nan yana kama da Abban kausar. Nace, haka ake ta cewa, dama kin san mutane sun ce in mai ciki tana yawan kallon mutum ta kan haifi mai kama da shi. Ta yi Yar dariyar yake,tare da cewa, hakane kawata.Mai jego kam ina kallon ta sai harara take watso mana. Muna shiga dakina tace, Sadiya anya kuwa ba kanshin gaskiya a cikin lamarin matar nan? Kin san halin mazannan ko dai Dan sa ne? Ki yi hakuri kamarce naga tayi yawa. Nace, hum! Ke dai bari kawata, tsakanina dake nasan amanace, wlh dansane ciki yayo mata, yanzun data haihu zasuyi aure. Aisha amana na fada maki ko iya bata San wannan ba. Aisha ta zabura tare da fadin, kan uba! Lallai Sadiya ban taba sanin cewa Ke sakarya bace sai yau, yayowa wata ciki sannan ki yarda ta zauna maki a gida? Wallahi da ace nasan haka ne in nazo barka shegiya nake,kin ma daure masa gindi kenan gobe ya kara.Na ce, Aisha ki fahimta, uban ‘ya’yanane,mijina kuma yaya zanyi? Nawa ganin rufin asirinshi Nawa ne, kuma na yara nane. Ta yi tsaki bana Jin zan fahimceki, in tazo gidan ta koreki kin ga ai sai kiji dadin rufa masa asirin. Na ce, nasan dama bazaki fahimceniba, shi yasa tun farko ban sanar da Ke ba, dan na sanki. Ta dauki yarta tasa a baya,ta suri jakarta da hijabinta, Ni kin ga tafiyata. Na bita ina fadin, “Dan Allah Aisha ki saurareni. Ki tayi ta tafi abinta. Na ce to shi Kenan in kin huce za muyi waya ta ce ni kar ki kira ni. Na dawo daki na kwanta kan gado ina hawaye, in na tuno Yaya zasuyi aure da Mujidat Abin na daga hankalina ya kuma sani kuka. Ranarr da suka cika kwana 5, sai ga Yayakusan 10 na dare, Ni ce ma na bude masa kofa, ya janyo ni jikinsa,ni kaina bansan me yasa jikina yayi sanyi ba kuma banyi wani farinciki da ganinsa ba. Ya dago fuskata, sannan yahaskani da wayarsa, lafiya my choice? Na sa hannu na tare hasken,lafuya mana Yaya mai ka gani? Na karbi jakar hnnunsa tare da cewa sannu da zuwa,bai amsa ba sai dai ya ce, na ganki cool ne, kamar ba kiyi farin ciki da gani na ba. Na ce, bacci na fara. Sannan nayi gaba na bude masa daki ya shiga. Ya zauna bakin gado tare da fadin, na gaji yau Sosai,8 ta wuce na baro Abuja, kuma da safe zan wuce na zone Kawai sabida kin nuna zuwan nawa yana da muhimmanci. Na ce, to Kayi wanka zaka warware. Ya ce to. Kafin ya fito wanka na kawo masa tuwo daman shi nayi a daren miyar zogole. Sai da yaci na fitar da kwanukan, sannan na shiga gurin Mujidat tana zaune da waya tana chatting, na ce, ya kamata fa ki dinga bacci. Ta ce, ba zan yi hira da kawayena ba? Na ce, kuyi tayi, akawo yaro babanshi yazo. Ta kalli yaron sannan ta kalleni, ya yi bacci. Na Isa gurin yaron na dauko shi, ban tsaya jiranta ba na kai shi. Aliyu ya mike tsaye zumbur likacin da ya kalli yaron duk yadda Sadiya Ke bashi labarin kamannin shi da dan bai zaci har hakaba. Ya kalli yaron kusan minti 1, sannan ya miko mini tmkr yana tsorace,na maida hannuwana baya. Kayi masa addu’a kamar sauran yaran ka duk dadai baka samar da shi ta hanyar da shari’a ta amince ba, sannan ka yi masa hudu ba,ya daga murya rikeshi mana Sadiya. Na juya na fita. Abin mamaki sai ga Mujidat labe tana lekenmu, na tsaya turus ina kallonta, ita ma ta yi tsuru-tsuru na ce, a’a dama kina min labe? Ta soma Sosa kai, sai kuma ta shiga borin kunya, kin zo kin daukarmin yaro ba dole inbiba? Na ce, kina zargin zan cutar miki da yaro ne? Yaya ya fito ya mika mata yaron “ungo yaron ki kar ku tada min da yara suna bacci. Ta amshi danta ta tafi, ni kam a gurin na tsaya na ma rasa tunanin da zanyi, tun yanzu kenan kafin a daura Auren? Shi kam bai so yanda ya yi ba kada ma mu tada masa yara suna bacci, maimakon ya gargadeta kan cewa Kar tasake yi min labe, bai yi hakan ba sai ya shige abinsa. Ni kam dakin yarana na nufa amman ko zama ban yi ba sai ga kiranshi, sai da wyrta kusa tsinkewa sannan na daga. Meyene? Yace, zomana,sai da na dan bata lokaci, sannan na je. Kai kawo na samu yana yi a cikin dakin, ina shiga ya nufo ni ya kama hannuwana. Sadiya asirin da muka rufa zai tonu sabida kamannina da yaron nan ya dauko,ina ganin gara mu fadawa Iya Kawai ita kuma Mujidat ta yi tafiyarta tunda dama dan Kar Iya su sani ne zan aure ta, ni wallahi bana son ta, zata iya tarwatsa min iyali,na zame hannuna daga nasa na zauna bakin gado tare da rike kaina na ce, Yaya ba dan Kar asirin ka ya tonu Kadai ba ne na ce ka aureta, don gudun kada kuci gaba da haihuwa a titi babu aure, don nasan bazaku rabuba. Shima ya zauna, sai dai in itace baza ta rabu dani ba Sadiya, amman wallahi ni tuni na barta,na girgiza kai, Yaya yin Aurenku yafi a kan barin shi, don Mujidat ta tabbatarmin da hakan kuma na San zaku iya… hawaye suka soma zubomin cikin rawar murya na ce. kuma duk laifin kane. Ya kwanto ni jikinshi, wallahi Sadiya nayi nadama matuka, kuma naji kunyarki Sosai ki yi hakuri kidaina kuka, Kecefa kike Karfafa min gwiwa,kike bani shawara. Ya dago fuska ta. Hankalina yatashi da yawa ganin kamannin yaron nan,nasan sai dai mutane su ji mu Kawai, ammababu wanda zai yarda cewa ba yaro na bane. Ya share min hawaye. Ki yafe min. Na ce, Yaya ni dai alfarma Kawai zan roka a gurin ka guda biyu. Da sauri ya ce, na miki alkawarin yi miki su fadi inji. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Na ce, na farko duk rintsi kada ka juya min baya
ko ka wulakanta ni. Ya rike kafaduna muna kallon
juna, insha Allahu Sadiya ba zan miki ba ko bisa
kuskure insha Allahu. Nace sai na biyu, izini zaka
yi min in nemi koyarwa a makaranta, ko L.E.A ta
nan unguwar Mu’azu. Ya yi shiru yana nazari, can
ya ce, kin gane Sadiya ba wai ina son hanaki
bane, nafison ki nutsu a gida wallahi bana son
matata tana yawo. Na ce, akwai dalilina, ka ga
Kwanan nan zamu zama mu biyu a Kasan ka,
duk wata bukata da zan nema a wurinka dole ne
ka yi mana mu biyu, inko inada nawa zan yi
bukata ta ba tare da na takuraba. Ya ce, wannan
bai kai dalilin da zan bar ki ba sai dai in bar ki
sbd tun farko na amsa cewa nayi miki alfarmar
da kika nema,da dai tun farko na san wannance
alfarmar da bazan yardaba, sai dai kimarki ta
wuce in amince, sannan in dawo in ce a’a, kije
kiyi koyarwa ki, amma ki tsare mutuncinki da
nawa.Na sauke ajiyar zuciya ‘nagode mijina, Allah
ya saka da Alheri. Ya lumshe ido sannan ya
bude. Yanzu wane suna za’a sa masa?
Na ce, a’a wannan shawarar tsakaninkane da
Mujidat, da safe ka sameta ku tattauna. Bai ce
kalaba sai ya kwanta rigingine.
Da safe falo ya zauna yace in kirata,ta fito tana
yatsina cikin Riga da wnd ta zauna, ya ce, wane
suna kika zaba? Ni kam mikewanayi. Ya ce,zo
mana My choice. Na ce, ina zuwa. Dakina nashiga
na bar su dan zancen na su ne.Ta mike daga
Inda take ta koma kujerar da Ke daf da shi ta
ce,Sweety kaine zaka bashi suna in dai nice nafi
son sunanka don yaron yafi kama da kai. Darling
kabiyani dakabani mai kama da kai. Ya waiwayo
ya daga mata hannu, tsaya!baki dacikakken
hankali ko? Ni ne nake bada haihuwa?Ki sawa
yaron ki duk sunan da kike so amma ban da
nawa kin gane ko? Ta ce, to ina son a samun
Abdul-kareem. Ya ce, ya yi Allah yaraya shi.tace
ameen. Sai maganar auranmu. Ya mike tace, na
zata tun ranar dana haihu zamuyi maganar shine
yanzu na kawo maganar za ka tashi? To bari kaji
daurin auren nan in ya wuce gobe za ka ji
mamakin abinda zai faru.Ya shigo daki, ina jiyo
duk yadda sukayi nace, Yaya ka amince nima ina
son a daura a wuce gurin kawai,ya ce, ba zanyi
yanda takeso ba, tana ganin itafa wata cikakkiyar
marakunyace. Bata San cewa ina daga mata kafa
bane sabida Ke,nace, dan Allah kai dai gara a yi
ko a wuce gurin. Sam ban zaci za a yi wani suna
ba, don haka ban tanadi wani batun sunaba,
kuma da zai tafi yace Usman zai kawo rago shi
ma bai yi min batun suna ba, amma muna da
kayan abinci na ce masa ya siyo mata sababbin
kayan sawa ita maijegon,yace bazai siyoba, ko
dan kyalle.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Washegari tin misalin 8 na safe naji bugun gida,
dama na rufo kofar gidan ina sauri zan kai yara
makaranta don munyi latti, kafin in bude sai ga
Mujidat ta fito da gudu tana cewa, oyoyo Momy!
Kaucewa nayi ta bude, ashe ‘yan uwanta ne daga
Lagos su 4, Mamanta,Babanta, Kawarta da
Kanwarta suka kalleni nima na kallesu, don hauka
har uban suka shige cikin gidan, nasa yarana a
mota na fice cike da takaicin da ya Aliyu ya ja
mana. Har na dawo raina a bace. Mujidat
nasamu a kicin tana ta fasa kwai ita da kanwarta
suna hada abincin karyawa, ban kula su ba, na
shige dakina cike da bakin ciki. Ko da naji bugun
gida ban fito ba a zatona wadansu dangin
nasune, amma sai na ji wayata tana ruri na daga
ashe Usman ne yace Madam ki bude gida ga
Ragonnan,nabude ya shigo da Ragon muka gaisa
yace kuyi hakuri banzo barkaba, wallahi Sadiya
takaici ne ya yi min yawa bana son ko ganin
matar nan, bare Dan, sanann ga kunyarki. Nayi
murmushi tare da cewa, Haba dai, gurina
bakomai ya Usman. Aunty Abida fa? Ya ce, suna
lafiya,naji tana cewa zatazo anjima. Na ce, yauwa
Dan Allah Yaya ina jiranta yanzu, bari in kira
maijegon ka ba ta, dama danginta sun zo. Ya ce,
daga ina, oho bansan garinsu ba. Nace dashi. Na
leka dakin sunyi dirshan a kasa suna tacin abinci
suna zuba yare har da uban, a raina na ce
tabdijan! Hauka. Na ce Mujidat kizo inji Yaya
Usman. Ta ce, in yazo ganin yarone ya shigo
mana, ni bazan fitoba. Na ce, Rago ya kawo
muku, shima sauri yakeyi. Ta mike tana yatsina
ta fito. Ni kam ban koma gurin su ba sai da na ji
yana kirana. Madam na tafi.,na fito nace to Yaya
mungode, amma lallai ina jiran Aunty, yayi dariya
zan fada mata kiyi ta hkr Kinji? Na ce ba komai.
Sati 1 Kawai da suka yi a gidan naga takaici,
gulma gurinsu ga shegiyar kazanta. Babanta wai
ya so ya ga Aliyu saboda a yi daurin aure su zasu
tafi ,kuma ganinsa baza su iya dawowa ba, shi
kuma yaya yace dansu Bazai bar aikinshiba sai
dai na lallabasu da cewa su tafi in Ya zo sai a je
can garin. Haka kuwa sai tafiya suka yi, ya so ma
har Mujidat ta bisu can, amma da yake ta san shi
in har ta sa kafarta tabisu to sam ba zai nemeta
ba, don haka tace aifa sam ina nan na baka lkc
ka gama zaman ka dawo muyi aure.
Yafi wata sannan ya dawo, lokacin Abdul-Hakeem
yayi wayo sai gogewa yake yi, don ma ba ta san
bashi nono sai madara, wai bata san nononta ya
lalace, na ce Allah Sarki wata rana ma ke kanki
sai kin lalace bare wani nononki. Aliyu kam
tuburewa yayi cewa ba zai auri mujidat ba, nima
na tubure cewa ban yardaba, matsalar da ta
janyo rigima har sai da Usman yazo gidan.Usman
ya cewa Aliyu, alkawari Kayi tun farko, kuma
musulmi ne kai ka san muhimmancin alkawari,
sannan matarka tana da gaskiya ba za ku rabu
ba. Mujidat da Ke daki tana jiyo wa kuwa ta
fito,ta ce, ai mutuwa ce Kawai zata raba su,
kuma ta dibarwa kanta lokaci in har ya cika bai
ce komai a kan auran su ba za ta maka shi a
kotu, sanan zata nemi yan jaridu manema labarai
ta ce shine a matsayin wanda yayi mata wayo
yayi mata ciki bisa alkawarin zaiaureta, amma
yanzu yaki cikawa.Take Aliyu ya tashi ya watsa
mata mari, sannan yace bazai auretaba, taje tayi
duk abinda take ganin zai fitar da ita,da kyar
Usman ya tausheshi, ni kam daki na shige ina
kukan takaici mijina wanda nake girmamashi da
daraja shi, amma ga wata banza datti tana
wulakantashi,a fili na ce shi ya jawa kanshi.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Sun yanke za’a kai sadakin ta can lagos, amma
tare zasu har da ita da Usman da kuma su Yaya
Suleiman. Aliyu ya ce amma sai dai ta fadawa
dangin ta kada suyi maganar jariri, duk ina daki
ina jiyo su,lokacin ne na soma sabon kuka
saboda kishin mijina ta dai tabbata lallai mijina
auran zai yi.
Ya same ni a daki bayan tafiyar Usman cikinn
halin kuka, ya tsorata mutuka, ya dagoni yana
tanbayata dalili, ce masa na yi kaina ne kurum ke
mini wani irin ciwo.ya kawo min magani ya bani a
baki, sannan ya kwantar da ni.
Cikin dare na farka naganshi zaune, na dafa
shi,lafiya Yaya?
Ya ce, Sadiya, ina ganin har in mutu ba zan daina
nadamar laifin da na aikataba, ina cikin dana
sanin zinar da na aikata da banyi ba da ban fada
cikin wannan halin ba, yanzu tunanina da wane
yare zan fahimtar da Iya cewar zan auri wannan
yarinyar? Tsoron tunkararta nake da zancen
Aunty wallahi,ban san me yasa a duk lokacin da
mijina ya shiga damuwa hankalina kan tashi
tausayinsa ya cikani,gaskiya da mutane suke
cewa In kana son mutum kana tausayinsa. Sai na
kwantar da kaina a kirjinsa, sannan nace. Don
wannan Yaya Kar Ka damu, in Allah ya kaimu da
safe zan samu Iya, ko kuma muje tare da kai. Ya
ce, Sadiya bana son yadda nake ta saki karya don
ki fitr da ni. Na ce, Allah zai dubani ya yafe min
karyar insha Allah, tunda dan gyara nayi ba don
batawaba,Ya rungumeni yana fadin, Sadiya Ke ce
rayuwata, Ke ce abar alfaharina. Na ce, nima
kaine rayuwata. Muka kwanta cike da damuwa a
zukatanmu.
Goma tagota muka fito zuwa gidan Iya. Yayaya yi
mutukar kyau cikin shadda waganbari mai kalar
sararin samaniya(sky blue), Hula mu hadu a
banki,itama kalar kayan, wanda kyan shi ya tona
tsadar shi, yana ta kamshi. Ni kuwa Atamfa na
sha Purple mai ratsin fari, Takalmi da Hijabina
kuma farare, muka jero tamkar sabon aure muka
nufi gidan Iya.
Tana zaune kan sallaya ta idar da salar walaha
da fara’ar ta dubemu tana cewa. Masha Allah ina
zaku haka tabarakallah amma kunyi kyau. Muka
sa ‘yar dariyar yake dan nayi Imani yadda nake
tsananin fargaba, hakan nanma Yaya yake ciki.
Nace gurinki muka zo. Yaya ya ce daga nan za
mu je kasuwane ne sai muji ko kina son wani
abun?. Ta ce, bana bukatar komai Gadanga. Duk
wani abu da zan nema ka ajiye min, ga firji da ka
sai min ina ta saida ruwan sanyi ina samun na
batarwa, ba abunda nake bukata Allah ya shi
muku albarka yasa yayanku su goyaku.Muka ce
ameen,tace, yan uwnka sun zo sun fada min
cewa ka kai musu kayan abinci su duka ko?yayi
yar’ dariya, ‘Iya wannan aikin Sadiya ne, ta ce
duk wata in dinga sai musu kayan abinci shi ne
muka fara da wannan watan. Iya ta kalle ni da
dariya, ‘Hali Dubu rubutun dutse, halinki dubu
duk na alkhairi, na san sai ke ‘yata. ‘Ta kalli
Aliyu. Dadin auran mace tagari kenan zata dinga
bai wa mijinta shawara ta gari. Aliyu ya dube ni,
sannan ya kalli Iya, ‘Wannan gaskiyane Iya. Nace,
‘Yanzun ma gurin ki muka zo kan wani
batu…..tace, to, ya aka yi? Na kalli Yaya, shi ma
ya kalle ni na ce, ‘Ka fada mata. Ya ce, ‘A’a ban
san ta inda zan fara ba ki fada mata kawai in ta
amince shi kenan. Iya ta ce, ‘Ku fada min mana,
kun daga min hankali. Na sunkuyar da kai, ‘Iya
dama mun yi shawara da Yaya ne a kan cewa zai
….za ya… ‘Sai na yi shiru. Ta ce, ‘Inajin ki. Na
ce, ‘Zai auri bakuwar nan ta gidanmu sabida tana
da hankali kuma…..’ Da tsawa ta katse ni, ‘Ke!
Da kata kin san me ki ke fada kuwa? Waye zai
auri wa?
Na kalle ta ‘In..
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Yaya ne (Na nuna shi) zai auri Mujidat, tana da
hankali Iya sosai. To ya ce yana son kara aure shi
ne na ce ya aure ta. Iya ta rabka salati,sannan ta
ce, ‘Amma ban taba sanin ke mahaukaciya ba ce
sai yau, ni ban taba jin inda aka ce ga wata mace
ta ce mijinta ya yi mata kishiya? Ta sake zabga
salati tare da riqe haba tana kallona. ‘Ko ni nan
da nake tsohuwa bakeba a ce babanku zai dawo
duniya zan amince ya yi min kishiya? Dan haka
ban yarda ba. Muka kalli juna da Yaya, ta ce,
‘Meye matsalar ka da har kake son kara aure? Ko
har yanzu bata son haihuwar ne? Ya ce, ‘A’a
wallahi bata da laipin komai kuma ba inda ta
kasa, dama sabida raya sunnah ne kamar yanda
yake cikin musulunci, yarinyar nan kuma Iya ta
musulunta ne in ta auri wanda ba na kwarai ba
za ta dauka haka halin musulmi yake, amma mu
za mu yi mata mu’amula ta kwarai yanda ba za
ta yi da ta sanin musulunci ba. Iya ta ce, Eh, ai
dama ke Sadiya ba a yada ke gurin magana,ni fa
dan ke nake fadan nan amma ke na lura kamar
zuga ki nake, wai ke ba kya kishin mijinki ne?nayi
‘yar dariyar yake, sannan na ce ‘Ina kishinsa
mana amma hakan ba zai hana shi ya kara aure
ba. Ta yi shiru tana kallon mu can ta ce, ‘Ni fa
ban yarda da yarinyarba, kallonta nake kamar
wata ‘yar bariki ko wadda ta buga duniya. Muka
kalli juna,Ya ce, ‘Ai kin san zaman Lagos, sannan
ba ta dade da Musulunta ba.Nace, ‘Eh, ba ruwan
ta Iya. Ta ce, ‘Oho! In ma da ruwanta ke ki ka
sani tunda kin ji kin gani ai shi kenan, ni me zan
ce, Allah yasa alheri. Yauwa, kwanaki yayanku
kece min ‘yan uwanta sun zo na ce shi ne don
rashin mutunci ai sazo su min godiya. Muka sake
kallon juna ni da Yaya, na ce, ‘Af wannan laifina
ne Iya ni ce ya kamata in rako su kiyi hakuri. Ta
rike baki tare da cewa, ‘Uhum! Abind ya same ki
kar Allah yasa ya samu sauran dangi. ‘Na ce Iya
na gode bari mu tafi. Haka muka bar Iya baki
bude tana mamakina,ni kuma na ce masa mu
tafin dan kar ta canza ra’ayi,duk da ta amince,
amma ba wai ina murna ba, bani da yanda zanyi
da ya wuce in kauda da kai a yi auran, na san
mata da yawa za su ga baike na amma ina san
su sani DA KISHIYAR WAJE GARA TA GIDA.Daga
nan gidansu Anty Abida ya ce mu tafi,,ni dai
muna tafe ne ba kamar yandamuka taho dazu
ba, ba wata hira bare annuri. Mun samu Usman
a gida don haka muna shiga suka fita. Aliyu ya
kalli Usman ‘Aboki, Iya fa ta yarda da batun
Mujidat. Cikin mamaki Usman ya kalle shi tare d
fadin, ‘Kai haba? Aliyu ya ce, ‘Allah da gaske.
Usman ya ce, ‘Banzata ba, ya aka yi ta amince
da sauri haka? Ya ce, Kai bari kawai,yarinyar nan
Sadiya aboki ba ni d abind zan biya ta, ita ce ta
shawo min kan Iya har ta amince da batun,sai na
lura da akwai wasu shakku daga zuciyarta, Allah
yasa ba ta gane cikina Mujidat ta haifa ba.Usman
ya ce, ‘Ka kara rike matarka da kyau,ina fada
maka a wannan zamanin ba za ka samu tamkar
ta ba, ina fada maka ko Abida matata ba za ta yi
wannan jan aikin ba, tana fada min sai dai ta ce
tana karfafawa Sadiyane dan tasan za ta iya
kuma hakanne mafita. Aliyu ya ce, Allah ya ba ni
ikon riqe ta da gaskiya. Usman ya ce, Ameen,
yanzun mu tafi gidan su Yaya Sulaiman mu ji
yanda za a yi. Aliyu ya ce to, Allah ya rufa asiri.
Abida ta dube ni ina kuka, kallo na kawai take yi
bata hana ni ba kuma bata bani hakuri ba. Sai da
nayi mai isa ta. Sanan na share hawaye na,
sanan ta dafa kafada ta. Sadiya kada kiga cewa
ban baki hakuri na barki ne ki rage radadin dake
zuciyarki, gaskiya ne in ka zubar da hawaye yana
rage bakin ciki, amma in tambaye ki mana? Na
kalle ta da jajayen idanuna, ta ce kukan nan na
menene kike yi? Murya ta a dishe tana rawa na
ce, anty… Abida ina da matukar kishin Yaya
Aliyu,Dan ban san irin son da nake yi mashi ba,
kukaba yakunshi abubuwa dadama, amma kishin
mijina shine a gaba, wai mijina zamu raba da
wata, inna tuna haka hanjina na kaduwa, da na
sani ban amince ya aure taba…. Sabon kuka ya
kubuce mun.Tace kijure, Allah yasan nufinki,
karki bari yaga karaya daga gareki, domin ba
mijinkiba har mijina ya ce kin burge shi kullum
cikin yabonki yake tare daba mijinki shawarar
cewa yayi maki kyakkyawar ruko, dan haka ki
cigaba da dannewa. Na ce, to anty zan kula,
yanzu na sha kanshi ya amince in nemi koyarwa,
sai dai ban san ta ina zan fara ba. Ta ce kada ki
damu shugabar makarantar firamare ta L.E.A
unguwar Mu’azu kawar yaya ta ce zanyi mata
magana sanan karamar hukumar Kaduna ta kudu
ma babban wan su Usman yana gurin ne kuma
nasan zai tai maka. Na ce, to, aikuwa nagode
Anty Abida Allah yabar kauna. Tace amin. Haba ai
ba komai wallahi. Nan muka wuni nakasa cin
komai, Anty Abida har Dan wake tayi min wai
taga inaso, amma da kyar naci uku ina taunawa
tamkar ina tauna magani, ko ruwa na sha sai
inga tamkar magani . Anty kanta ta shiga
damuwa tana min fadan kan in kashe kai na a
banxa. Na ce mata. Anty kiyi hakuri cikin
kwanakin nan ko gida na bana iya cin abinci in na
dauki littafin marubutan nan in dan duba sai
komai ya tsaya min inkasa fahimtar me nake
karantawa mai makon in karanta litafi sai dai shi
littafin ya dinga neman karantani da ko ina da
yar matsala inna karanta sai ya dan rinka debe
min kewa. Ta ce ai duk ki ajiye batun littafi
kirumgumi mai kankat wato, ALKUR’ANIR
KAREEM. Na sauke ajiyar zuciya,, tabbas Anty
Alkur’ani yana sanyaya zuciya mu kan musalmi
bamu da kaico sai godiya ga ubangijin da yayo
mu a musulmi. Ta ce haka ne Allah kasa mu
mutu a cikin musulumci muna a musulmai. Na ce
amin.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Kafin su dawo ta sani na wanke fuskata nayi yar
kwalliya, duk da fara’ar da nadingayi sai da yaya
ya gane nayi kuka, duk lokacinda na kalle shi sai
in ga idanunsa na kan fuskata har dai ya kare ya
ce Sadiya kukan me kikeyi? Muka kalli juna da
Anty abida ta ce, sam bata yi kuka ba me kagani?
Yayi dan yake shi dole murmushi, ko ba jami’in
tsaro bane ni, kun san daini ba yaro bane. Na
share zan cen da cewa, yaya mu tashi dan yara
na jira na in daukosu. Ya ce madan saurareni.
Abida ta kalle shi ya ce, nifa bana son abin da
zata shiga matsala, in auren nan zai kawo mata
damuwa wallahi sai a fasa duk abin da zai faru
ya dade bai faruba kowa ya ji cewa nayi wa wata
ciki ta haihu, daga nan fa? Na runtse ido, don
Allah yaya mu bar maganan nan, nace maka ba
damuwa nake ciki ba, ka yarda dani. Usman ya
ce aboki ina ga dai na dawowa da hannun agogo
baya din nan a bar shi. Abida ta ce ai sadiya
jaruma ce bata cikin wata damuwa, kuma
malamai sun sha fada muna cawa in Allah ya
rufa maka asiri yayin da ka aikata wani laifi to kai
kada kayi kokarin tonawa kan ka don haka barin
batuna haka shine mafi a a’ala. Haka dai muka
baro gidan nasu bayan sun yi mana rakiya.
Saty daya bayan nan suka shirya tafiya lagos, sai
dai ban da ya Sulaiman saboda suna son yan da
haduwar su da dangin mujidat zai kasan ce, haka
nan basa son yanda ya Sulaiman ya san cewa dan
da ta haifa na shi ne. Sun tafi da Usman da shi
Aliyun da kuma Mujidat da Danta. Sai dai lissafin
da aka yi masa ya same wuce hankali, domin ko
auren Sadiya bai kashe wannan kudin ba, sannan
kudin sa da ke accout yayi shirin siyan wani gida
ne da aka yi masa tallansa can kasan su a
sabuwar unguwa da ke nan unguwar Mu’azun. Ya
kalli Usman ya ce aboki ni fa ba zan iya biyan
wayan nan kudinba. Usman ya ce, to ka kirata ta
fada musu baza ka iya yin al’ada ba. Ya kalli
waliyin ya ce a kirata. Sai suka ce ai su al’adar su
ba a magana da amarya sai su waliyanta. Usman
ya ce to su basa yin wanan al’adar sadaki kawai
zasu biya. Sauran suka ce sam ai tunda ta haihu
a tasu al’adar yin biki dolene, kuma abubuwan
al’ada dole ne, domin ita mai albarka ce mai
haihuwa ce, sannan ba dama ya ce ya fasa tunda
ta haihu.
Shi da Usman suka kalli juna a ran shi ya ce lallai
ya debowa kanshi ruwan dafa kanshi. Usman ya
ce kawai ka basu inya so sai ka sai fili bana son a
samu matsala. Nan dai ba da son ran shi ba ya
amince bayan sun fita suka tafi banki in da ya
ciro kudi suka dinga yi masa lissafi yana ba su,
nan fa suka ce jibi za su yi hutu, suka amince a
haka. Ni kam ko da suka dawo bai fada min ba
gurin Anty Abida na samu labarid Usman ke fada
mata, na ce shi dai ya sani can da yawarsa.
Idanu na zuba ina kallonsa yau da na ga yanzun
yana dan zakewa tare da rawar kai, sam ban zata
ba, ya sa a yi gyaran gida. An yi fenti na kwashe
kayan yarana daga dakin da ta zauna tunda nan
za’a sa ta, ya ce da ya so canza min gado,amma
in yi hakuri ko daga baya ne. Yaba ni dubu
talatin,na yara ashirin na karba na aje tare da
cewa mun gode. Na dauki waya ta ina dannawa
ya ce, Wai Sadiya akwai wani laifi da nayi
makine?na kalleshi’ Me ka gani? Ya ce, Na ga tun
jiya da na zo ba wata fuska a gurinki?Na maida
kaina ga kallon wayata,sannan na ce, Akwai abin
da ban makaba daga cikin wanda na saba
yimaka?Yace, A’a,kin min komai MY CHOICE, sai
dai ni na gane kamar ba ki da walwala. Na ce, Ba
ka yi min komai ba. Ya ce, To anjima zan tafi, Na
ce, Allah ya kai mu. Har ya kai bakin kofa na ce,
Au! Na manta in fada maka an dauke ni amma
ba aprimary ta nan unguqar Ma’azu ba, ta can
Tudun wada. Ya tsaya yana kallona, nima shi
nake kallo don son jin ta bakin shi,a zuciyata ina
cewa yanzun dai a ce ya hana ni, tabdijan! Da sai
ya ji magana. Tamkar ya sani sai ya ce na san
kina zaton zan hana kineko? Ai ba ni da yanda
zan yi tunda na rigana yi miki alkawari,amma ki
sani raina baya so. Ban ce kala ba na ci gaba da
danna wayata shi kuma ya fita.
Ban tabbatar da cewa ina da kishi ba sai da
lokacin auran ya gabato,wallahi ko abinci kasa ci
nayi duk datausar da Aisha ke min da kuma Anty
Abida dan ganin na kwantar da hankalina, amma
na kasa, bana bacci sosai duk da cewa bana
nunawa Yaya damuwata sai dai shi duk lokacin
da muka yi waya sai ya yi min korafin in daina
damuwa in kwantar da hankali,To kurum nake ce
masa, amma zahirin gaskiya zantukansa ma soya
min rai suke yi.
Ana gobe daurin aure zasu tafi can Lagos din ina
kallo shi yana ta shige da fice yana shiri,an zuba
sababbin dinkuna an sai Huluna da Takalma sai
ina mamakin mutumin da na dinga shan kan shi
da kyar shi ne yake zumudi. A fili na ce Allah
yasa abin ya tsaya nan. Ya fito cikin shiri ina
kwance kan gadon yara ya ce ‘My Choice mun
shirya,na dago na kalle shi, yayi matuqar kyau
cikin Shadda Wagambari Blue shar kaladaya da
hularsa mu hadu a banki, kamshinsa ya cika
gidan, kishi ya kama ni mai tsanani,na kau da kai
gefe. Ya ce, ‘My choice yaya ne? Ban tanka masa
ba sai zuciyata ta ce gwada shi ki gani da yake
cewa in na ce ya fasa zai fasa,in ya so duk ma
abin da zai faru to ya faru. Ya tallabo fuskata.
‘My Choice, yaya ne? Na ce, ‘Ni fa gsky na sake
tunani a kan wannan auran, gaskiay ina tsoron
abin da zai biyo baya. Zai fi kyau a barshi.
Zumbur ya mike tsaye daga russunawar da ya yi,
na kalle shi ga mamakina fuskarshi daure, ya ce,
‘Me ki ke nufin maidani? Karamin mutum? Kin sa
mun yi magana yanzun kuma kizo ki ce ke kina
jin tsoro, ya kamata ki fadi haka ne tun kafin
yau, sai dai ki yi hakuri,mamakida tsoro suka sa
na kasa daina kallonsa sannnan ga hawaye yana
ta zuba tamkar an bude famfo, na girgiza kai
tare da sauke ajiyar zuciya,sai kuma ya zauna
kusa da ni tare da dafa kafadata. My choice bana
nufin cutar da ke kece kika karfafani kika nuna
min yin auran nan shine mafita, to me zai sa
yanzun ki bijiro min da wani sabon batu bayan
aski ya zo gaban goshi? Kuka ya kwace min na
shiga rera shi, tsam ya makaleni jikinsa yana
lallashina. Sadiya in kin ce baki so wallahi abar
shi. Ya ciro wayar shi yasoma dannawa. Bari na
fadawa Usman ya kira Yaya Sulaiman ya fada
masa cewa nafasa.ina jiyo shigar wayar ta soma
ringing a can,da sauri na dago na amshi wayar
da sauri na katse. Ya ce, yaya kuma za ki katseki
bani in dakatar dasu su daina shiri. Na cecikin
shagwabar kuka, Ni fa ban ce ka fasa ba.yasa
hannunsa ya dago fuskata,To me kika ce?Na kalli
cikin idon shi ‘In ka aure ta zaka daina sona? Sai
kurum naji bakin shi cikin nawa, minti1muka
dauka, sai wayarshi ta shiga ruri,ya sakeni tare
da daukar Wayar. Usman ina zuwa. Ya katse ya
kalleni. My Choice in na yi rantsuwa bazan yi
kaffaraba Ke ce 1 tak nake so, kum na soma son
ki ne tun lkcn da kika soma zama mace. Da farko
ban fahimci ina sonki bane sai da Usman ya
kwadaita mini da nazo iya ta ki sai na samu kaina
da kasa hakura, wannan ya tabbatar min cewa
ina mutukar sonki,Ke ce zabina, kada ki damu da
Mujidat sam ba na son ki hada son ta da naki, Ke
ba ita ba in miki ta mahaukaci duk duniya ba
wata mace da nake so ko kuma zan sota sama da
ke, ki rike wannan a cikin zuciyarki,so 1 tak Ke na
ke yiwa shi.,lumshe ido na yi inma karya Yayaya
fada min to na yarda don gaskiya maza da ace
zasu gane furta son ka ga matar ka komai
dadewar aurenku yana susutar da mace komai
shekarunta ta ji ta tamkar sabuwa,amma
matsalar maza musamman irin na yankinmu ba
sa iya cewa matar su suna sonta, ko wasu
kalamai na soyayya irin wanda suke yi mata yayin
yakin neman aurenta da zarar sunga cewa sun
aurenta shi Kenan ta tsufa Nima haka na ji
tamkar farkon aurenmu duk damuwar dake cikin
zuciyata sai ta gushe, sabida ina son a so ni,ina
son a nuna min soyayya, ina son a fada min
kalaman so. Nasa hannu a kumatun shi na shafa
ina kallon cikin idon shi, Yaya na gamsu da
kalamanka, Allah ya tsare hanya gobe zaku
dawo? Ya ce, insha Allah ko jibi, tunda da nisa in
mun taso da yamma ko da dare sai safe zamu
iso. Na ce shi Kenan. Ya mike tsaye, me zan sayo
miki a can? Na ce, gdnsu lesuka, in ka siya min
zanyi murna. Ya ce insha Allah zan zabo miki
masu kyau. Na ce to nagode. Har waje na raka
shi. Sai dai duk da haka kasa bacci nayi daren
ranar sai damuwa da sake saken zuci.
Washe gari kuwa data kasance ranar daurin aure
ba zan iya lissafa tashin hanklin da na shiga ba.
Da safe kasa zama na yi a gidan na tafi gidan Iya
wai don in manta da batun auren amma duk da
haka na kasa sukuni, har Iya ta fahimta, sai
kurum naji ta ce. Sadiya, hakika kishi wani abu ne
mai rai, amma yana da sauki in kin saukakashi,
ina son ki nutsu ki rike girmanki. Shawarar da zan
baki ki kara zage damtse gurin kyautatawa mijinki
kada ki dauki halayen wasu matan masu cewa in
miji ya kara aure zasu daina yi masa komai suce
ya je can matar da ya auro tayi masa, wannan
kuskure ne, don in aka samu wadda ta san
hannunta kafin ki samo mijinki sai wani ikon
Allah,ki zama a gidanki Ke ce uwar kowa. Ina
nufin duk abinda ya taso na kudi ko matsalar
lalacewar wani abu a gida Kar ki tsaya jiransa kiyi
da kudinki in yaso in yazo kya karba ko yaturo
miki, sannan ba’a fata in har sabani ya shiga
tsakaninki da ita tunda an ce zo mu zauna zo mu
saba, to kada ki sake ki fara kai kara Kinji ko? Na
ce, to. Yauwwa sabida in kinyi nazari cikin
ya’yanki mai yawan kawo kara duk gaskiyarshi sai
kinji haushinsa. Na ce, haka ne. To ki rike hakuri
da addu’a ki dinga yawaita karatun Alkur’ani mai
girma, ki zauna da ita zuciya1, sannan ga aikin ki
ma, ai ni naji dadin barin ki da yayi wannan
koyarwar, na ce, nima naji dadi iya, don ina da
yara gara dai yanzu da muke mu 2 aikin ya dauke
masa matsalolina in ina samu ba sai na jira shi
ba, kudin da ya bani ma nawa da yara wai muyi
siyayya su dai na Dan sai musu wani abu, so
nake in hada jari in dinga saye da siyarwa. Iya
tayi dariya tare da cewa, da kyau Sadiyayyena.
Haka nayini Iya tana kwantar min da hankali tare
da bani shawarwari sai kusan 10 na dare na debi
ya’yana ta raka mu har gida, nima na sake rako
ta hanya.ina sa hakarkarina a kan gado na dauko
wayata nakunna dama yinin ranar kashe ta na yi.
Nan fa sakonni suka soma shigowa na yaya sai
na Aisha da Anty Abida, na su na soma dubawa.
Tanbayata suke ina naje sun zo ba nanan? Na yi
dan murmushi, a fili na ce da kun zo gidan Iya ni
kam ba zan yi wani taro ba, sai na soma duba
nashi,duk kusan yana nuna damuwane akan ya
kira bai sameni ba. Sai na karshe da yake cewa
sun taso 9 suna hanya, akwai yiwuwar su iso
kafin 9 na safe, kuma suna tare da wasu daga
danginta dan Allah ta tanadar musu abinci. Kiran
Abida ya katse karatun sakon da na keyi, na daga
muka gaisa, ta ce min, ina na shige yau? Na ce
ina gidan Iya,tace to, ki yi sammakon tashi don
mijinki zasuyi shigowar safe ne, nace Anty me
zanyimusu?tace karin kumallo mana kiyi zuciya1
kada ki sa kishi ciki, bakin kine, kin kuma san
darajar baki a musulunci. Na ce to Aunty zanyi.
Tin 4 na tashi na fara firar dankali da nayi sallah
kuma na hau suya, har kaji biyu nayi musu
farfesu, kwai ma isasshena yi musu kwai da kwai
na dafa ruwan tea mai yawa, sannan na gyara
gidana nayi wa yara wanka na zabo musu
sababbin kaya nima na sheka nawa adon.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Takwas daida na ji tsayawar motoci,gabana ya
yanke ya yi wata muguwar faduwa,sai na hau
karanta Hasbunallahu wa ni’imal wakil. Na mike
na je na bude musu kofa gabana yana ta
faduwa,zuciyata tana maimaita addu’a.suka shigo
suna yi min sannu, wasun su suna kallona wani
iri,amma duk da haka na saki raina ina yi musu
sannu da harshen Turanci.Najee na bude musu
dakin suka yi sororo a tsakar daki don ga
al’adarsu miji ke shiryawa mace daki ya zuba
komai, ita kuma iyayenta su yi mata kayan sawa,
nan fa suka soma yare, duk da bana ji amma
ganin yanda suke magana suna tabe baki na
fahimci zancen nasu bana dadi ba ne, naje
nasoma fito musu d kuloli. Sai gasu Yaya sun
shigo, na kirkiro fara’a ina yi musu sannu da
zuwa. Falo suka je suka zauna na gabatar musu
suma da abin kari, na kula yaya ya ji dadin
yanda na saki jikina na kuma yi musu abin
kari.Nan nabarsu nayi daki,bayan Mujidat da
danginta sun gama karyawa sai suka samu su
Aliyu da Usman suna yi musu korafin ba su ga
kmai a dakin ba.Usman ya ce, Mu a nan da kaya
amarya take zuwa. Suka ce su kam ba haka ba
ne, nan suka fito masa da akwatunan amarya
har da na mijin da na Maman shi da kuma na
danginsa. Aliyu ya ce shi kenan zai siya daga
baya, amma yanzun a kwaso na dakinsa a sa
mata,sukace bakomai. Ina dakin nashi ya shigo
wanda zuwa yanzun ya zama nawa,ya zauna.
Sadiya kin ji wata sabuwa. Na kalle shi, ya ce,
Wai ni zan sai mata gado. Na ce, ina zaton haka
al’adar su take don mun taba yin zancen da wata
‘yar ajinmu da muka yi N.C.E take ba mu labarin
al’adunsu, miji ke yin kayan daki kuma sadakin
su yana da tsada, amma mace za ta ja jari da su
ita ce za ta rike gida,wasu kuma jarin daban miji
zaibada, wadanda ba Musulmi ba sun fiyi,
Musulminsu kamsai sunyi aure suke tarewa gidan
mazajensu,yace,nidai yanzun ya za’a yi? Na ce su
zo su dauki wannan gadon. Na tsura masa ido
cikin mamaki,sai ya ce, ko ya ki ka gani? Na mike
na nufi dakina bayan na ce, Me zan ce kai da
abinka. Na shiga dakina na soma kallon dakin ina
lissafa yanda zan gyara shi ni da yarana da na
bar musu gadona tunda dama katifu gare su. Sai
ga shi ya shigo.Haba Sadiya,me zai sa ki
yankemin wannan hukuncin? Nazo miki da
shawara amma sai ki yi watsi da ni kitaho abin
ki? Na ce, Yaya kainefa da abinka kuma ka ba
matarka, mene ne laifina dan na taho? Yace, Ok,
kije amma ki sani kada nan gaba ki ce na daina
kawo miki Shawara,kin sani dai ke ce kurum nake
tunkara da duk matsala ta. Shiru na yi dan nasan
in hakan ta faru lallai ba zan zama uwar gidaba.
Ya mike zai fita na ce, Yaya” ya dawo,Mene ne?
Na ce, Shi kenan ka yi hakuri. Ya zauna tare da
kamo hannuna, Nagode da ki ka fahimce ni,
yanzun ya ki ke ganin za’ayi? Na ce, Ka ba ta,ni
kawai sai naringa kwana a nan da yarana. Ya
tsura min ido, To nifa? Na ce, Ba komai ka yi ta
kwana dakinta. Ya yi dan murmushi, Har yanzun
baki huce ba.Na yi ‘yar dariyar yake, Bana fushi
da kai. Yace, Zan siyo katifu yau a sa can dakin in
komai ya warware zan canza gadajen gidan.Na ce
to maimakon ka ba ta tsohon gadon ba gara ka
sai mata katifar ba? Amma yanda ka gani, Ya ce
na riga na fada musu ne na ce to su dauka bari.
In zo in kwashe kayan na wardrobe din. Ya ce,
A’a, gado kawai da katifa za ta dauka. Na ce, Shi
kenan, Allah ya rufa asiri. Ashe tashin hankali
yana gaba,sai lokacin bacci, Mujidat ta kira shi a
waya wai tana jin bacci, ya kalle ni muna zaune
kan gado,sannan yaci gaba da magana. To ki
kwanta mana. Ta ce, Ba dakin ka zan kwana ba?
Ya ce, A’a yanzun bani da daki in danginki sun
tafi na kwana adakinki. Mamaki da haushi suka
cika ni, ga kishi kamar in hade raina, na ce, Kuje
dakin naka mana? Yaja tsaki tare da cewa, Don
Allah ki bar wannan maganar. Na kwanta tare da
juya bayana na rungume yarana bankara
sauraron shi ba, shi ma ya kwanta a daya gefen
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Washe gari tun Asbahi suka soma shiri,suna
karyawa suka tafi, wata daya ce daga cikinsu
kadai ta yi min sallama da godiya, suna kama ina
zaton yarta ce dake illorin din, domin nayi
dawainiya dasu sosai ta fannin abinci. Ya tsaya
da su sun shiga gurin Iya sun gaisa duk da cewa
ba sa jin yaren juna, sannan ya wuce dasu zuwa
gareji. Ranar ne matan Yaya Sulaiman da su Anty
Abida sukayi ta zuwa ganin Amarya. Anty Abida
ta yi ta yi min fada wai ya zan sa abu a cikin
raina ga shi nan duk na rame, na ce Anty dole in
sa a raina, ba za ki fahimci zafinkishi ba, duk irin
bayanin da zan yi miki, kuma bana fatan a yi miki
ki ji.Anty Abida tace, Ameen,don Allah ina son ki
saki ranki. Amarya dai tana daki bata fito ba, da
za su tafi na raka su ganin amarya ta ci rigarta
da wando na bakin Jeans, danta yana cikin gadon
shi ta yi ruf daciki kan gadon da suka kafa tana
chatting, a yatsine ta amsa sallamar,sannan aka
gaisa,suka yi fatan alkhairi suka fita.
Daran ranar ne ya hada mu a falo yana yi mana
nasihar zama lafiya, sam ban san me yake cewa
ba, ina can gurin tunani. Yau ga shi abin da nake
karantawa cikin littattafai ya zo kaina, ji nake
tamkar cikin mafarki, ashe dai nima za a min
kishiya. Girgiza nin da yayine ya sa na dawo cikin
hayyacina,cikin damuwa ya ce, Menebe? Na
girgiza kai ba komai. Ya ce, ina tambayar ki game
da kwana,na ce, Nawa nawa? Nayi hamma
kirkirarra, sannan duk yadda kace. Ya ce, To a
bar shi bibbiyu kamar yanda aka fi yi. Na ce shi
kenan. Ita dai tana ta jijjiga danta,na sake kirkiro
hamma, zanje in kwanta bacci. Ya kalli agogon
bango; Da wuri? Na ce, Na gaji ne. Na kalli
amarya wadda ta sha leshi kai ya ji gashin doki
ya zubo har kafada, na ce, Sai da safe,ta dube ni
da ‘yar yatsina eh, dama ban jira amsar ta ba na
yi tafiyata. TABDI! Daran ranar kasa bacci na yi
har zuga ni zuciyata ta dinga yi wai inje in labe
inji me suke yi, amma sai na fi karfinta inda na
yo alwala na yi ta sallah in nagaji in dauki
Alkur’ani nayita karantawa,sai da na yi sallar
Asubahi sannan na kwanat. Allah ya taimake ni
yarana suna cikin hutun makaranta ne, don haka
da na tashesu muka yi sallah sai muka koma.
Ban farka basai tara, ina tashi Mama ta tashi, sai
da na yimusu wanka sannan muka
fito…..zandakata anan zuwa lokaci na gaba,fatan
zaku kasance tare dani
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Leave a Reply

Back to top button