DARAJAR YAYANA PART 3

DARAJAR YAYANA PART 3

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100

Darajar Yayana3-04
Posted by ANaM Dorayi on 07:21 PM, 06-Apr-16
Under: DARAJAR ‘YA’YANA
________________NA ___________HALIMA K/MASHI Tun a falo nasan cewa masu gidan sun jima da tashi,domin ga gurin da aka karya nan ba a kwashe kayanba,na shiga kicin na soyo wayara dankali da kwai, dama ni ban damu in ci wani abuba don bana jin yunwa, na hada musu Tea sannan ni kuma na sha ruwan Lipton, na kwanta ringine ina karanta wani post da Sheik Daurawa yayo a facebook, sai ga shi ya shigo, idanuna basa san kallonshi, ina jin su Kausar suna gaida shi ya amsa tare da sumbatar su a goshinsu su duka, sannan ya zauna bakin gado kusa da ni. My choice,ina ta shigowa kuna bacci da yaranki. Ban tanka masa ba ya ce, An tashi lafiya? A ciki na ce, Lafiya lau. Ya ce, ke kin ci abincin ne? Na ce Um, ya yi shiru yana tunanin me zai ce, ni ko da zai fita ma zan fi so. Sai ya ce, yauwa am, Sadiya jiya namanta ba mu yi magana ba. Ba tare da na dago ba na ce inajinka. Ya ce yanzun wane hukunci zamu dora Mujidat ko in ce ina za mu ajeta? Budurwa ko bazawara? Yana cewa haka na fuskanci nufinshi wato kwana nawa zaiyi, zuciyata ta soma tafasa,amma sai na fara karanta addu’a, na tashi na kalle shi. Mujidat budurwa ce, don haka sati daya za ka yi a dakinta, garabasa ma dazan yi maka ita ce ka gama hutunka kaf a dakinta. Ya ce, a’a ban yarda ba. Na koma na kwanta ba tare da na kara cewa komai ba. Ya amshi wayar hannuna yana cewa. Me ki ke gani ne cikin wayar ki, wanda ya fi ni? Juyowa na yi ina kallon shi,sai da ya gama karantawa,sannan ya ce, Banace kirufe wannan account din ba? Bana son kina hawa facebook fa. Yayi maganar tare da dan hade rai. Nace, To ni menakeyima a facebook din? Daga ganin abin da duniya ke ciki sai post din malamai,sai ko gidajen da akabude dan wayarwa da mata kai. Ya ce, Duk da haka dai na ce ki rufe zan sai miki kasunan wa’azi in namu sun miki kadan, sannan zan baki kudi ki sai littattafai na wayrwa da mata kai din, huldarki da internet din ne ba na so,ban amsaba,shi kuma ya fice. A raina na ce ka zaci abin da kakeyi a internet din haka kowama keyi? Na ajiye wayar batare da na goge ba, sai dai cikin zuciyata na dauki aniyar gogewa,amma ba yanzu ba. Duk zatona da naganta kicin tana girki duka gidan za ta yi, amma sai na ga ta juye kula daya ta nufi dakinta, don haka sai na tashi nayiwa yarana. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Bai shigo gidanba sai Magriba duk da dai ya
kirani ta waya da rana yace menadafa? Na ce
masa taliya, shi dabagwanin taliya ba ne don
haka sai ya ce to bari ya ci tuwon sa gurin Iya.
Ya sameni daki ina karanta littafin Hausa, su
Kausar suna ta wasa, nan suka tashi suna
yimasa oyoyo, na dube shi tare da yi masa
sannu da zuwa. Ya amsa,sannan ya zauna. Kin
ganni sai yanzun? Na ce, Eh, ina zaton wani aiki
ne ma ya taso maka. Ya ce, A’a, wallahi gidan
ne sam baya yi min dadin zama duk jina nake a
takure, shi yasa naso in sayi wancan gidan ga
shi duk na kashe rabin kudin.
Dariya ta subuce min cikin zuciya nace ai ba a
banza aka kashe ba,tunda aure kayi, ko ba nan
kudin suka wuce ba? Shiru ya yi tunda ya san
bai fada min cewa kudinsa sun wuce a gurin
auran Mujidat ba, sai ma ya dauko wani batun.
Yauma baki cemin lesukan nan sunyi kyau ba?
Nace, Na fada maka mana, ka dai manta ne ko
dai anan kakashe kudin? Da sauri ya ce, A’a ni
ban ce ba. Wayar shi ta soma ruri ya dauka, sai
na ji ya ce, Ke ina zuwa nafa shigo gidan. Ina jin
haka na san cewa Mujidat ce, a raina naji zafi
mijina wata ke kira kuma tana da damar yin
hakan, jin hawaye na son zubo min sai na mike
na shige bandaki tare da cewa, Bari in yo
alwalar Isha’i.
A dakin Mujidat Aliyu ya zauna idanun shi yana
kallon Abdul wanda daga jiya zuwa yau ya soma
son dan shi, ita kuma tana kwance rufda ciki
tana chating ya sa hannu ya amshi wayar, ta
tashi zaune. Honey ban waya ta, muna hira a
group dinmune, don Allah.Ya soma danna
wayar yana dubawa,can ya dube ta, Har da
maza fa na ga kuna hirar? Ta ce, Eh, ba za mu
yi hira ba,’yan group din mu ne fa? Ya kashe
wayar, sannan ya sa ta cikin aljihunsa, ta ce,
Ban gane ba, amma kai ka sai min? Ya ce, Zan
sai miki wata da wani sim din yanzun karkashina
kike ba zan yarda ki yi hulda da kowa ba,tace
Kana nufin har da iyayena,da sauran dangina?
Aliyu ya ce, Bance zan hana ki hulda da
danginki ba, amma sai na tantancesu.taja
tsaki,sannan ta zauna cikin fushi, ya isa gabanta
yasa yatsunsa ya damki lebenta, Kar ki sake yi
min tsaki sabida yanzun ni mijinki ne yana da
kyau kisan darajata. Taji zafin yanda yayi mata,
har ta yi ‘yar kara sannan ya saki ya kuma fita.
Na yi hakuri tare da cijewa gami da kau da
kaina game da Yaya da matarsa.Ranar da ya
cika sati dayama nace nakara masa wani
satin,amma ya ce sam ba ya so. Kafin hutun shi
ya kare wani aiki ya taso don haka ya shirya
komawa ya kira mu falo ya ce to ni zan tafi. Ya
kalli Mujidat. Kada ki sake in dawo inji wata
matsala ta faru, sbd in na ga sabon abu daga ke
ne. Na dade dasanin wace ce matata,sannan
duk abin da ki ke bukata ki tambayeta. Sai abu
na gaba bance kitafi ko’ina ba, don baki dakowa
a garin nan, kin fahimta ko? Ta turo baki gami
da bata rai,sannan ta ce yana yi mata gorin
dangi kenan? Ya ce in kin dauka haka to hakan
ne. Ya dube ni, Kici gaba da hakurin da nasan ki
da shi,sannan ki kama girmanki, kamar yanda
kikeyi, inda wata matsala ki sanar da ni,sannan
yau kwanana daya a dakin ki tafiyar nan ta
taso,ina dawowa zan sauka dakinki in yi kwana
dayan da ya rage,sannan in koma gurin ta,nace,
to Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya. Yara ma
ya sallame su, kamar yanda ya saba muka raka
shi har mota,har da Mujidat din sabe da danta
a kafada,duk da ba ta zo kusa da shi ba. Na
ce,baka sallami Abdul ba.nakalli Mujidat, Ki ba
Baban shi su yi sallama. Ya ce, A’a, bar shi
kawai. Ya tada mota, sam ban so yanda ya yi
ba,domin a gabanta ya rungumi sauran yara
tare da sumbatar su, fuu! Ta juya ciki, tun kafin
ya tada motar,nabita da kallo,sannan na
kalleshi. Yaya ka daina haka, yanzun mun zama
daya kuma wannan yaron ka ne kar ka gwada
bambanci ko ka ce za ka yi kara dan ganin
idona na san dai kana son danka,ya tada motar
tare da cewa, Na tafi.Na ce Allah ya tsare.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Gaskiya Mujidat ba ta bukatar muyi zaman
lafiya yadda take mu’amalarta da yarana amma
ni na sawa kaina alwashin sai dai tayi da wani
amma badaniba, duk da cewa na san ban girme
ta ba,amma a gurina zubar da aji ne in tsaya
cacar baki da kishiya,gurin cin abinci dama tun
yana nan bai hana kowa yin na shi ba.Da farko
na so in masa magana kan cewa ya za a ce
muna gida daya karkashin miji daya, amma mu
raba girki,sai kuma na ce bari dai in bar shi
tunda shi ke nemowa.sai kuma ta tsiri fita zuwa
gurin wasu ‘yarbawa yarensu,sai ta kai dare.
Randa ta fita na uku na yi mata magana,tana
shiga dakinta na bita. Maman Abdul. Ta waigo
ta dube ni,sannan ta ci gaba da kwantar da dan
ta a kan gado. Na ce, Amma kin san mijinki ya
cekar ki fita ko? Ta ce, Na fita din zan ta zama a
gida ne? Ya amsar min waya,sannan ya cezai
hana ni fita, ba zan iya zaman takura
ba,nace,zaman aure shi ne zaman takura?
Ta ce, Maman Kausar don Allah ki barni kawai,
kije ki harkar ki.
Jin haka sai na tafi na kyale ta.
Yaya bai zo ba har sati biyu,duk da yana
kiranmuta waya ko yaushe yana tambayata ko
akwai wata matsala a zamanmu da Mujidat,nace
masa babu wata matsala, ina zaton bai
fadamata cewa yana zuwa yau ba, tadaiga na
haukace da aiki,munyo kitso da lallae ni da
yarana. Ina da nacin yin lalle dan na san mijina
yana matukar so, ya ce min shi zan tayi masa a
gida,don haka su Kausar suna dawowa daga
Islamiyya suka cire kayan makaranta na shirya
su cikin sababbin kaya.Allah ya taimake ta tana
shigowa ko minti goma batayiba na ji tsayuwar
motarsa,nafito daga dakinsa inda na kai turaren
wuta nace su Kausar ga Abbanku,da gudu muka
fita ni da su, nan ta fito kallonmu, duk da cewa
ko a da ta saba gani lokacin renon
cikinta.Dukkanmu muka rungume shi,tsaki ta ja
sannan ta juya cikin dakinta. Duk hidimar da
mukeyi bata fito ba, har lokacin da muka shirya
fita zuwa gidan Iya, na ce baka duba su Abdul
bafa.Yace, Uhm! Yaushe nashigo gidan? Ni zan
je in duba su koko suzasuzo duba ni? A nan na
yi Magriba na yi Isha’i,ba ta fito ba,in ma za ta
ce ba ta sanna dawo ba da Kausar ta kai mata
tsarabar su ai ta san na dawo,nace, duk da
haka ka leka,Tsaki yaja,sannan ya fita abinshi.
Na leka dakin, tana zaune bakin gado ta zabga
tagumi ranta a bace, nace, Sai mun dawo za mu
je gidan Iya,ga mamakina sai naga taja wani
uban tsaki tare da banko min harara, sai na ji
dariya ta subucemini, don haka na yi ‘yar dariya
tare da sakin labulan nata, ina jiyowa ta yi wata
kalma da yaransu wadda nake zaton zagi ne.
Iya ta yi murna da ganinmu,sannan ta ce ina
‘yar uwarki? Nace, Tana gida, ta ce a gaishe ki.
Tace,Ina amsawa. Ita bata fitane bakuzo da
itaba?Yaya ya ce, Ba za ta zo ba. Iya ta ce,
Sadiya ke ce zaki dinga janta in zaki fita, don ta
saba d mutane tunda kin ga ba ta san kowa ba.
Nace to Iya. Mun je gidan Yaya Sulaiman, Yaya
Zakari, da kuma Yaya Sani, duk mun ziyarcesu,
inda Yaya ya yi musu alkhairi. Ina jin dadin
yanda Yaya ke kula da danginshi suna shi masa
albarka, sai dai bayamin kara yayi wa
mahaifina.amma na sha alwashin koya
masa.Daga nan muka dawo gida,kai har yanzun
na tabbatar Yaya yana sona.sabida irin soyayyar
da ya gwada min ta dare dayan da yayi a
dakina. Washe gari mun yini gida cikin jin dadi
da annashuwa, amma Mujidat taki fitowa, sai
lokacin bacci sannan ya nufi dakinta.
Kuka ya sameta tanayi wiwi,ya isa kusa da ita
ya ce, Lafiya? Ta watso masa kallon banza da
manyan idanunta da suka kada suka yi jajir, ta
ce, Haka dama aurenku yake? Ka nuna min
cewa matarka kawai kake so, babiba. Ya ce,
Menayi miki? Ta ce, Tunda ka dawo ka ajiye ni
kamar kashi, matarka da yaranka kadai ka sani.
Ya ce, Kece ki ka ja jikinki damu, na dawo kinki
zuwa ki gaisheni.Ta ce, Ka fada min cewa zaka
dawo? Sai na fada miki dole sannan zaki gaishe
ni? To ni ba haka tsarina yakeba. Ta ce, Eh,
amma ka iya fadawa matarka ai, tunda naga
sun shirya,nima in ka fada min ai zan shirya. Ya
ce, To shi kenan next time zan fada miki tunda
dakin ki zan sauka, dan gobe zan tafi. Ta tashi
ta dawo daf da shi tasa hannu a kumatunsa,
Aliyu ina son ka da yawa, nima ka daure ka
soni. Ya yi murmushi, sannan ya ce, Ina son ki
mana, Ya kalli kitson ta. Har yanzu ba ki cire
wannan gashin dokin ba? Bana son shi. Ta ce,
To zan cire gobe. Ta dauko Abdul tasa masa a
cinya.Tunda ka dawo ba ka dauki yaronka ba,ya
kalli yaron cikin kauna, sannan ya soma yi masa
wasa da kumatun,sai dai koyaushe ya rike yaron
gaban shi yana faduwa, kuma yana tuna masa
cewa fa akwai wani asiri da ya boye. Ya kan ji
tausayin Mujidat a irin son da take masa, kuma
yana son ya kyautata mata ko don yanda ta
hakura da rayuwar bariki ta yarda zatayi zaman
aure,har inzata zauna da su lafiya to zai mata
adalci, don haka ita ma ya nuna mata soyayya
daidai gwargwado, wadda ita da kanta ta yarda
cewa ya soma sonta.Haka nan da zai tafi ya
sake tara muya yi mana nasiha,sannan ya tafi.
Dama makarantar da aka dauke ni koyarwa
sunce sai andawo hutu, tunda tuni sun min duk
wani abini da ya dace kafin a dauki duk wani
malami, don haka ana komawa hutu na soma
koyarwa a matsayin sabuwar malama, aji biyu
na nake dauka, wato ‘yan safe. Don haka tun
Asubahi inna tashi nake kammala yarana ina
sauke su in wuce tawa makarantar, sai dai
matsala daya aikin gidana dole sai na nemi ‘yar
aiki kenan. Kodanayi wa Aliyu wannan batun sai
ya ce dalili kenan da baya san aiki ga matarsa,
ba danbazai iya biyan ‘yar aiki ba, a’a sai dan
ba za a tsaya a duba masa gida da kuma yara
ba. Na ce ni dai zan biya mai aikin cikin
albashina, ya ce ai ba wai ba zai iya biya ba ne
ya fi son ya ganni a gida.Iya na fadawa a samo
min ‘yar aiki,tace in kuna da wadatar gurin
kwanane sai ku dauko Nasiba ‘yar gidan Yaya
Zakari. Na ce ai matsalar gurin kwanan ne, na fi
son wadda ke kusa da gida,in ta yi aikin ta ta je
gida. Iya ta ce haka ne. Ansamo min wata
yarinya ‘yar matashiya, kullum zatazo ta yi min
wanke wanke da shara,haka muka ci gaba da
tafiyar da rayuwa da dadi ba dadi, ina kuma
yabawa Yaya yanda yake kwatanta adalci
tsakaninmu, amma kullum Mujidat gani take yi
Yaya ya fi sona da ita. Albashina na farko naje
na sayo kayan abinci da zannuwa turmi biyu.
Ranar Yaya ya dawo ya tsaya yana kallon kayan
abincin.Wanna fa? Na ce, Babana zan
kaiwa,tunda na yi aure ban taba yi masa wani
abu ba. Ina kallon Yaya ya yi shiru yana
nazari,sannan ya ce, Nawa ne kayan nan? Na
fada masa ya ce to kafin in tafi zan baki.Nace
ayi haka Yaya daka barshi. Ya ce, Nima ai ‘dan
shi neko? Na yi shiru, ya ce, To zan ba ki ba zan
so ba a ce kin riga ni kaiwa mahaifinki wannan
alheirin. Na ce, To shikenan Allah ya saka da
alkhairi. Ya ce ameen. Na ce, Ni dama ko da na
kai da sunanka zan kai.ya ce, Yanzun ma duk
ba haka ba,wai ke za ki je Zariyan?
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
na ce, Eh, wai da. Ya ce, ‘A’a gobe zan je in kai
musu. Na ce don Allah ka je da ni. Ya ce a’a,ina
ce ke ce na ji Iya tana fada miki bikin kannanki
guda biyu? Na ce cikin shagwaba, Allah Sarki
Yaya bikin fa sai daf da Azumi akwai saura. Ya
ce, Eh, ki hakura sai lokacin. Na ce, Shi kenan.
To yanzun in kabani kudin nan me ya kamata in
siya? Yace, Oho! Miki, ki bude account mana. Na
ce eh, tozan bude.
Cikin wannan lokacin na soma rasa gane kaina,
ba sai an fada min ba na san cewa ciki gare ni,
ban taba irin wannan cikin ba mai masifar
laulayi. Binta yarinyar da ke min aiki ita ce ke ta
dawainiyar aikinta, har ma jinyata. Mujidat
kuwa ba ta zama,bata taba yimin sannu ba, sai
dai in jiyo tana ta yi wa yara wasa.Su Khausar
su ne suka sanar da Iya cewa ba ni da lafiya sai
ga ta. Ranar ita ce ta gyara min gida,sannan ta
kira Mujidat tana ta yi mata fadan cewa. Me
yasa ‘yar uwar kina ciwo amma ba za ki taya ta
aiki ba? Sai ta ce wai ita ba ta sani ba, ko da
Iyan ta shigo tana fada na ce mata kar ta damu
Mujidat ba mai son aiki ba ce, don ko dakinta
ba kullum take gyarawa ba,Iya ta ce Allah ya
kayuta, ni sai in gakamar ba kwa zaman lafiya?
Nace, Lau muke ni da ban cika zaman gidan ba,
don dai ciwon nanne. Iya ta ce, To kin sanar a
makarantar? Na ce, Har malamai sun zo duba
ni. Ta ce, Allah ya kara sauki, ga shi kinki zuwa
Asibiti. Na ce to ko na je ba wani abu da za su
yi min sai magani, to ko maganin ba zan iya
shaba, ko fa ruwa na sha sai ya dawo. Nan Iya
ta yini kafin ta tafi..
Cikin dare kuma tamkar ba zan kwana ba,
Kausar da Binta mai aikina sune a kaina. Kausar
nata kuka,ta je ta fadawa Antynsu amma ta ki
zuwa, tama ki bude kofa, duk da irin
kwankwasawar da Kausar take yi, na ce su dau
waya ta kira Babansu,sabida gani nake tamkar
ba zan tashi ba. Ya daga kiran farko, Kausar ta
ce, Abba, Momy fa ba ta da lafiya. Cikin muryar
kuka ta yi maganar. Ya ce, tabani na amsa
sannan nace sufita,suna fita cikin muryar wadda
ke cikin matsananciyar jinya na ce, Aliyu ka
yafemin bana zaton ciwon nan na tashi ne. Cikin
daga murya na ji ya kirani da karfi, SADIYAA me
ke damunki? Cikin rauni na ce ka yafe min? Bai
amsa ba ya kashe wayar. Can jimawa sai ga
Mujidat ta shigo, na san cewa shi ne ya kirata,ni
dai daga karshe bansan me ke faruwa ba ma,
ashe wai suma nayi.Ihun Mujidat shi ne ya sa
su Kausar tashi daga bacci.ta kira shi tana ihu
wai bana motsi,kila na mutu ne,ya kidime sosai
da jin hakan kuma nan take ya kira Usman,
yasanar dashi duk abin da yake faruwa, cikin
daren Usman ya zo yana buga gida Mujidat sai
tace da Binta mai aiki taje ta bude, cikin tsoro
yarinyar ta ce waye? Ya ce nine Usman bude, ta
bude. Har dakina Usman ya shigo, Mujidat tana
ta ihu ya ce takama su sani a mota, ta ce ba
mutuwa ta yi ba? Usman ya ce sai na ji daga
likita.
Asbahin fari na farka na ganni a gadon
Asibiti,an samin ruwa. Usman da Mujidat na
gani tana zaune shi kuma yana jingine da
bango,ya zo kaina yana min sannu, na kalli
ruwan na gane ina Asibiti ne. Ya dubi Mujidat ta
farfado. Mujidat wadda bacci yake fizgarta,ta ce
uhm,uhum, tare da tabe baki,ta soma jijjiga
danta, sannan ta ce, sannu Maman Kausar.
Idona yana lumshe kai kurum na daga,ina ji
lokacin da Usman ya kira yaya fada masa cewa
na farfado. Yace shi ma yanzun haka ya wuce
Nasaraw daf yake da Unguwar Ma’zu , Usman
ya ce muna asibitin Biba ne. Aliyu ya ce ka fada
min. Yaya ya rude da ganin yanda na dawo,ya
kama hannuna ya zauna bakin gadon, Sadiya
me ya same ki? Na bude idanuna ina kallon shi
ya rusuno ya sumbaci kumatuna. Sannu kin ji?
Ya kalli Usman. Sannu Aboki, na gode Allah ya
saka da mafificin alkhairi.
Usman yace , Haba dai sai ka ce wani abu? Allah
dai ya ba ta lafiya. Aliyu ya ce ameen, na gode.
Da ya samu labarin cewa ciki gare ni sai na ga
Yaya ya soma murna,tamkar cikin fari. Usman
neya taho da Mujidat wacce ke ta yin gyangyadi
a zaune. Tunda duku duku sai ga Iya wai da
Asuba Binta da Kausar suka je suka fada mata,
ita ce ma ta tashe mu daga bacci, domin bacci
ya sace mu Yaya na kan kujera ya dora kansa a
gadon, hannuna yana kan nasa kawunan mu a
hade, motsinsa shi ne ya tashe ni, suka gaisa ya
fita sallah. Sai lokacin na tuna da ‘yan yarana
su kadai kenan su ka kwana.
Kafin yamma naji karfi sosai sakamakon ruwan
da aka yi ta dura min mai dauke da sinadarin
abinci,likitan ya sallamemu tare da ba mu
magunguna. Tunda muka dawo gida yaya ke
jinyata,Sallah kurum yake fita har abin da zanci
shi ne ke girka min,, ya min wanka,abin ya
kunna Mujidat har ta kai su ga fada ya mareta,
tun daga lokacin ta yi wa kanta alkawarin kawo
karshen zaman shi da matarshi ko ta halin
kaka. Yayan da zai yi kwana biyu sai da yayi
biyar ya ga nadan murmure,sannan ya tafi..
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Duk abin da nake so sai da ya tanadar min
isasshe sannan ya tafi. Kullum gidan ba ya
rabuwa da ‘yan dubiya. Aisha ta yi ta yi min
iskanci wai na narke sai ka ce cikin fari, Yaya shi
kuma ya daure min gindi tun da tazo ta ga yana
ba ni abinci a baki shi kenan fa,nace na ji dai ai
ko wane ciki na fari ne tunda wuyar dana ke ciki
da wannan na fari ban sha ta ba.
Na rarrafa kicin ina dafa taliyar Hausa, sai ga
Mujidat daga yawonta an zugo ta ta shigo da
fushi, Mama tana wasa da abin kama shanyar
ta da ya fado daga igiyar yaronta, ban ma lura
da shi a gurin ta ba sai na ga ta kwace tare da
rankwashin ta a kai tana zagin ta da Turanci.
Maama ta yanka ihu raina kuma bace na ce
mata. Ke! Na nuna ta da yatsa. Ki shiga
hankalin ki, wannan ‘yar yarinyar zaki doka?
Wallahi ba zan dauka ba. Ta harareni tare da ce
min ta doketa, kuma kada in ga wai nayiwa
mijina asiri yana mata wulaqanci in dauka za ta
tafi ta bar shi, to in sani ita fa ba inda za ta,
domin shi kadai ta gani miji,sannan in shirya
barin gidan bada jimawa ba. Na yi dariya. ‘Ke
ko Agumin ku yayi kadan bare ke, ba da tsafi ku
ke takama ba? Mu zuba ni na riqe Allah.Ta
shiga daki fuu! Na yi mutuwar tsaye ina
mamakin lamarin,wannan ai ke ce kwarkwasa
fidda mai gida a gidansa,iInshaAllahu ta Allah
ba ta ki ba.
Haka muka ci gaba da zama cikin husuma
kullum sai ta tsokaneni,in na yi kamar in hada
ta da mijinmu sai in kyaleta. Ashe ita kullum aka
yi saita kirashi a waya. Sai da ya yi wani zuwa
yake min zancen wai me ya hada mu da Mujidat
ne?nace me akayi, tace anyi wani abune? Ya ce,
Eh tace kin canza yanzun kintsaneta, kiyi ta
zaginta kina mata gorin bana sonta,in ko har
hakane bazanji dadiba, domin batun ina sonta
ko bana sonta tunda yanzun ita ma matatace
bai kamataba. Yafa bata rai wai dole sai ya kare
mutuncin matarsa,inzaiyi adalci ai nasan ya fi
nuna so da kauna gare ni. Nayi ‘yar dariyar
takaici, sannan na ce, Tunda ka mance halina
har ka yarda da batunta shikenan. Amma in har
adalcin zakayi kamataya yi ka tara mu,dama
‘yan sanda da bangare daya suke aiki in sun ji
ta bakin me kara ya isar musu hukunci? Ya yi
shiru sannan ya ce, To muje falo a kirata, Na ce
a’a a barshi ni nayarda na dauki nauyin
zunubin.ya ce ni dai na ce ku fito falo.
A gabanta na maida komai kuma ba ta musa
ba,baisan tana fita ba sai lokacin danace ina
taje aka zugota. Nan fa ya zaro ido ina take
zuwa? Na ce ga ta nan ita ta sani, hankalinshi
ya tashi ya ce mata gurin wani take zuwa? Ta
zaro ido wai a’a gurin yaren su ne, dama shi
irin wannan auren haka kullum a yi ta zargin
juna, nan na tashi na bar su suna ta masifarsu.
Kafin ya tafi sai da ya kafa mata dokoki har da
na fita, amma yana tafiya ta sa kafa ta shure
dokar,sabida jarabarta ma ni na lallaba na soma
zuwa aikina, yara ko na kwaso su sai in kai su
gidan Iya in bana gida bana barin su a gida.
sai dai wani abu da na lura da shi shi ne wata
dinkewa tsakanin Yaya da matar shi Mujidat,
duk da cewa bai canza min ba, amma ina
mamakin sabuwar shakuwar in yana dakinta har
wani zumudi yake yi,sannnan ya kan dauki
danta ya fita da shi wani dare ma har saloon ya
kai ta, ko da dai ya min tayin zuwa na ce a’a,
sannan ya kan dauke ta da yara su fita shopping
duk da dai ya kan min tayin zuwa,ce masa nake
a’a sai sun dawo. Haka nan zasu zomin da
tsaraba,abin yana ta damuna hatta abincin ta
da yake cewa ba zai ci ba yanzun nadeshi yake
yi. Wani zuwa da ya yi sai na yi niyar gwada shi
ranar da ya dawo dakin Mujidat zai sauka sai na
yi tuwon shinkafa da miyar Ogun, bakwai da
wani abu ya iso gidan. Taliya ta dafa dama
girkinta bai wucetaliya da shinkafa da miya ba,
ga shi ta zabga uban attaruhu, ta saka wando
da riga an je an wanko kai, dan ma ba wani
gashi neda ita ba da na doki ake gayun, kuma
ya hana sawa,da in ya dawo ni yake fara nema
a ko yana dakinta, yanzun kum in dakinta yake
can yake yada zangoi,sai daga baya sannan ya
zo. Ina sallar Isha’i ya leko, sai kuma ya shigo
ciki ya zauna,sannan na gaida shi ya amsa tare
da tambayar jikina na ce da sauki sosai, na kalle
shi. In kawo maka tuwon shinkafa miyar ugun
ce? Kafin ya yi magana sai wayar shi ta soma
kara, da ya daga sai ya ce, Ya? Ina jin haka na
san Mujidat ce, ko me ta ce sai na ji ya ce’O.k,
gani nan, Ya kalle ni.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Mujidat ce take jirana muci abinci, na so cin
tuwon amma yaya zan yi tunda girkin ta ne zai
fi kyau mu ba ta hakkin ta ko? Raina ya sosu
matuka, amma sai na danne na ce, Haka ne, na
ga ai kuna ta dasawa. Ya kalleni, Kamar yaya?
Na ce,gani na yi kana ji da ita. Ya ce, Lallai
Sadiya,harma zakice haka yanda na fifita ki a
kanta kuma ta hakura? Nayi guntun murmushi,
Ni ba ni san ka fifita ni a kanta, na fi son ka yi
adalci, ni na san dama duk zance ne da ka ke
cewa ba ka sonta. Ya hade rai, ‘Wannan wace
irin magana ce? Kin san ai matata ce, batun ina
son ta ko ba na son ta ki aje shi. Ya mike tare
da fadin. Banason irin zantukan nan kowacce ta
zauna a matsayinta. Ya fice abin shi. Na jima
ban iyatashi ba, eh na san ba laifi ba ne dan ya
nuna kulawa ga matarsa,amma abin da ke ban
tsoro yanda na ga yana son hada matsayin da a
da ya ce ni kadai ke da shi ya raba mana. Anya
nan gaba Yaya ba zai bijiremin ba? Wata zuciyar
ta ce haka wane shi, zai manta asirin da Allah
ya rufa masa kuma ke ma ki ka rufa masa.
Da safe muka shirya da yara zan aje su a
makaranta nima in wuce gurin nawa aikin,sai
lokacin suka bude kofa muka gaida shi, sannan
muka wuce. Ko a makaranta a ranar tunani
nake ta yi in zan lura da kyau yanzun ma bai
cika nema na ba sosai, ga zatona don ba ni da
lafiya ne, amma yanzun na gane ba haka bane.
Da muka tashi na kira shi na ce zan biya gidan
Anty Abida,sai cewa ya yi shi fa ya tsani wannan
yawon,daga can bai ce in je koina ba, na ce to.
Cikin kuka nake fadwa Anty Abida matsalata,
dariya ta yi tare da cewa, ‘KISHI ke damun ki
Sadiya ga shi kin fada kin ce mijinki bai canza
miki ba,dan ya nuna kulawa ga matar shi ya ci
abincinta sun fita tare laifi ne? Na yi shiru. Ta
ce, ko yana miki sababbin dabi’u? Na ce, Eh, to
jiya dai da na yi masa korafin cewa yanzun yana
sonta kinga yanda ya bata rai,yana ta fada. Ta
ce, Kar kikara yi masa zancenta, ba ruwanki da
harkarsa. Na ce to shi kenan,amma fa bai cika
son Taliyaba ko na dafa sai na yi masa abin da
zai ci,amma ita sai ta yi masa yayi taci. Anty
Abida ta ce, Na ce miki babu ruwanki. Nace,
Yanzun duk ba shi da laifi? Ta ce, Babu. Na ce,
shi kenan. Tace ki kauda kai ga tunanin zai
canza kiyi ta kanki da lafiyarki. Na ce to Anty shi
kenan. Na nufi gida ina zaton sam Anty ba ta
hasashi abin da nake hasashe ba.
Tsakiyar falo muka same su ya dora Abdul
saman kafadar shi yana yi masa wasa, yara
suka yimasa sannu da gida,su ka nufi dakin
su,nima dai sannun nayi masa zan wuce yace,
Abdul yana ta kallonki MY CHOICE. Na dawo na
daga masa hannu tare da yin dan yake,nawuce
dakina.Ina kwance kan gadona ya shigo baifi
minti biyar da shigowa ba, Sadiya! Ya kira
sunana,bayan ya zauna bakin gado, na amsa da
na’am ba tare da na taso ba. Ya ce, Ni na ga
kamar kin canza min? Na ce, Kamar yaya? Sai in
ga kamar idanunki suna tuhumata a duk lokacin
dana kalleki? Na ce, A’a kai ne dai ka ke zargin
kanka. Yace,shikenan, ya jikin naki? Alhmdllh.
Ya ce, To haka akeso.Yakai hannunsa ya shafi
cikina,ya babyna? Ban tanka ba dan ni fa
yanzun abu kadan ke bani haushi, ya juya zai
fita kenan sai karar shigowar sakonni cikin
wayata, ina ji na san daga facebook ne,na kai
hannu zan dauka shi ma ya kai, saiya riga ni
dauka, gabana ya fadi dan na san cewa ya ce na
goge,ban goge ba. Ya dawo ya zauna, ‘Sadiya.
‘Na waiwayo na dube shi. Bana ce ki rufe
wannan account din ba? Na ce, ‘Zan rufe ai. Ya
ce, ba kida niyya. Ya soma fada. Ni fa bana son
taurin kai,wata nawa da cewa ki rufe,mekikeyi a
internet?na ce ‘Karuwa! Nima cikin zafin rai na
fada,ya ce in ban da shashanci dubi yadda
maza suke requesting dinki. Na ce, sai ka duba
ka gani na yi accepting? Ya ce, Ina ruwana, na
dai ce ki rufe kuma kin ki don haka yaune
karshe, in ba ki rufe ba sai kin daina rike
babbar waya. Zuciyata ta tunzuro na ce, O.K,
sabida nice zakace ma haka, amma matarka da
yake ita kana shakkarta ba yini take yi chatting
ba? Ya ce, Ita ma tunina hana,ita da har wayar
na amshe na ba ta karama me ta ce? Na dago
na kalle shi, Har yanzun chatting take yi. Ga
mamakina sai na ji ya ce, Karya ki ke, ‘yar Nokia
ce a hannunta,ina ruwanki ma in me take yi? Ke
dai ki hanu mana da abin da na hana ki? Ke
yanzun kin kama taurin kai,nema kike ki canza
hali ko? Kinfi son a yi ta fitina? Fuu! Yafice
abinsa. Sai na samu kaina da jin zafin
kalamansa,kuma na dauke su a matsayin
wulaqanci da tozarci,wata zuciyar tace me yasa
tuni da ya ce ki rufe account din kika qi? Ina
kokarin amsa laifi na ne sai wata zuciyar daga
gefen hagu tace shi ne zai fadamiki kalaman
batanci har da kiran ki shashasha? Bayan ita
waccan tana yin chatting ma bai hana ta ba har
da cewa karya ki ke mata, to kema kar ki rufe
duk abin da zaiyi yayi. A fili na ce, Ni da nake
karanta abubuwan karuwa a ciki ma ba zan rufe
ba.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Har ya tafi sama sama muke, amma duk da
haka yana kiran wayata sai dai ba na iya yi
masa hira dan haushisa. Tabbas in ma ya hana
Mujidat hawa internet to tana yi a boye dan
tana yi a gabana, sannan ba ta daina zuwa
gurin yarensu ba. Ni kam yanzun ba abin da zai
fi min illa in yi watsi da su in yi ta kaina. Kwanci
tashi cikina ya shiga wata na biyar,na dan
gyagije daga laulayi,kuma na soma siyayyar
kayan babyna. Tabbas Mujidat tana jin haushin
cikina,don ina lura da irin yanda take yawan
zabga min harara, sannan in ba ni ce na yi
mata magana ba itabata yi mini. Haushin da
take ji nawa a yanzun ko da da yayan bai damu
da ita ba ba ta ji kamar yanzun. Wata Litinin na
dawo daga aikina tare da yarana, na kai minti
biyar ina buga gida ba a bude min ba, har
nasoma zaton ko ba kowane a ciki, sannan aka
zo aka bude, sai dai wani rainin wayo ashe suna
zaune a harabar gidan ita da wadanda take
zuwa gurinsu su ma yau sunzo gurinta. Cikin
fushi na kalleta. Maman Abdul kina nufin
zamanku a nan bajuji duk bugun gidan da
nayiba? Ta yatsina fuska, Na ji mana ba gashi
na bude mikiba? Na yi kwafa tare da juyawa na
nufi ciki,sai na ji sun yi wata magana cikin
yarensu,sai kuma suka kwashe da dariya, na
dawo baya cikin zafin rai na ce Maman Abdul ki
ce da mutanen nan su fita,tace yazakice su
fita,wurin ki suka zo? Na shiga kicin na dauko
muciya nanufe su. Ku fita daga gidan nan maza
maza.Cikin sauri suka fita suna yare, itama
tabisu, na maida gida na rufe, na koma ciki, ina
ta huci. Hatta su Kausar sai kallona sukeyi
tamkar na zamar musu sabuwa. Kusan awa
daya na ji tana buga gidan, banza na yi da ita
har Al’ameen sai da ya zo ya ce Momy ana
buga gida, shi ma na kore shi, kusan minti
goma waya ta ta soma ruri na gane Aliyu ne,
dan ringing din shi daban ne, na daga raina a
cushe,ban raini shi yasa dukwanda ya yi min
raini nake jin zafi. Ya ce, Sadiya yaya za ki rufe
mata kofa, ki bar ta a waje? Na ce, Wa? Ya ce,
Au! Ba ki ma san kowace ce ba? Bari ki ji
Mujidat fa matata ce kuma ina son ta kamar
yadda nake sonki tayaya zaki hana ta shigowa
gidana, duk rigimar da kukayi dai ai kin san ba
ta da inda za ta. Zantukan shi suka zafafa
zuciyaa,sai kawai na kashe wayar, yayi ta kira
na ki dagawa,can sai ga kiran Anty Abida, ta
soma min fada wai me yasa na canza, mijina da
ke yabona ya koma korafi akaina. Na ce, Allah,
Anty ba zan bude ba, ni za ta maida ‘yar iska?
Shi kuma dayaji ta bakinta baya tuntuba ta, sai
kurum ya kira niya fara masifa, nagaji, shi
kanshi fa ya’isheni ke! Anty Abida ta katse ni
‘Kina hauka ne za ki ce mijinki ya ishe ki? Shi
kuma wannan cikin da masifa ya zo miki? Ki
bude mata gidan ta kira shi ta mafada masa, ya
kira ki kin ki sauraron shi shi yasa ya kira ni,
nima ba ki saurare ni ba? Shiru na yi mata tace,
Shi kenan. Ta kashe wayar, ni kaina ina
mamakin kaina yanda zuciyata ke ta
tafasa.Kamar daga sama su Kausar suka ce
Momy ga Iya fa. Na buga kafa,ashe shi ya kira
Iyan ya fada mata, jikina na rawa na je na
bude, ta kalleni ranta a bace. Sadiya lafiyar ki
kuwa? Yaya za ki koro abokiyar zaman ki waje ki
kulle gida? Na kalli Mujidat wadda saboda
makirci har da yin hawaye, na ce,Iya akwai abin
da ya faru. Iya ta kalleta jeki dakinki kinji? Na
soma kuka. Yaya za a ce kowa ba zai tambayi
ba’asi ba sai kawai a yita ganin laifina? Iya ta
ce, An gani, sakarya, a gaban kishiya za ki yi
kuka ‘ya’yanki suna kallon ki. Fuu! Na juya na
nufi daki raina a bace, ina gunjin kuka, Iya ta
biyo ni cikin daki tace, Sadiya yaushe ki ka zama
haka? Na ce, To, ni Iya shi kenan ba wanda zai
tsaya ya ji dalilina? Ta ce, Eh, ba wanda zai ji ke
bake ce babba ba? Ko me ta yi miki sai ki tura
ta waje? Me mutanen unguwa za su dauke ki?
Na ce, Wallahi Iya ni ban tura ta waje ba, ki
fada mata ita ma in na buga kofata ringa bude
mini. Na kai minti biyar ina buga kofa suna
wurin sunki bude min, da ta ga dama ta bude
na yi mata magana nace meyasa ta barni tsaye
ina ta buga kofa ga yara ni kaina na gaji fa, sai
ta ce min wai batajiba. Na tafi kuma suka yi min
dariya suna yare, ni ko na cewa wadancan su
fita shi ne ta bi su ni ko na rufe kofa. Iya ta ce,
shi kenan zanyi mata magana,amma kema ki
dinga tausan ranki dan naga kina fama dazafin
rai,ina zaton kuma ciki ne ke saki saurin fushi.
Na ce ko ba ciki dole inji haushi,Shima yaya ba
bincike ya kira ni yana ta min ihu shiga mai
mata,har da fadin cewa wai gidan shine, to ina
ruwana da gidan shi? Na soma sabon kuka, Iya
ta ce ki yi hakuri zan yi masa bayani, na san
cewa har da ciki wannan saurin fushin ki dinga
yawan salati kin ji? Na turo baki nawa ganin sun
dai ki fahimtata ne, na ce ita ma ki gaya mata
fa? Shi ma ki gaya masa. Ta ce zan fada musu.
Ta dinga tausa ta har zuciyata ta sauko sannan
ta tashi na raka ta,ta shiga dakin Mujidat ni
kam na yi bakin gate jiran ta.ta iso ta ce na yi
mata fada ita ma,don haka a zauna lafiya. Na
ce to Iya na gode, da na rufe gidan na dawo sai
naga Mujidat ta shiga kicin tana kumburi,nima
na yi cikin dakina. Iya tana isa gida Aliyu ya
soma kiranta,sai da ta zauna, sannan ta daga
wayar ta ce, Na dawo ai ta bude mata,dama
ashe ba ita ce ta koro ta ba. Ya ce, Ita din ma
za ta iya saboda yanzun Sadiya ban da neman
fitina ba abinda take yi, shi yasani yanzun ko
son zuwa Kaduna banayi. Iya ta ce, Ita ma
Sadiya ba laifinta ba ne kowane da irinsa,kuma
ba sabon abu ba ne kowa ya san mai ciki da
saurin fushi. Ya ce Iya ba ruwan ciki kada ku
goyi da bayanta, na soma tunanin damar dana
bata ne take zuwa koyarwa,can ake zugo ta, don
haka in na zo zan soke. Iya ta ce, Kull Ban yarda
ba,ba abin da ya shafe ka da batun aikinta, ka
dai yi hakuri har ta haihu,kuma wannan rikicin
tsokanar ta Maman Abdul din suka yi ita da
yaransu, shi ne ta kori wadancan ita kuma ta bi
su. Aliyu ya ce, Amma da na kira ta ba sai ta
fahimtar da ni ba, shi ne zata tsaya yi min
taurin kai? Iya ta ce, Na dai kashe wannan
wutar zancan kuma ya mutu.Ya ce shi kenan.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Goman dare ya kira ni na daga ciki ciki muka
gaisa, ya ce ranar Litinin zai turo da kudin
abinci, na ce muna da abinci mai ne da su
maggi ya kare, sai Indomie.
ya ce to bayan nan ba wata natsala? Na ce
babu, sai kudin asibiti zan soma zuwa
awo,sannan sai kudin siyan kayan baby. Ya ce
to na ji nawa zan bada? Na ce to ka san dai
komai sai na siya sabida bakamar na Mama ba
da na yi amfani da wasu abubuwa na Al’ameen.
Ya ce, Ni dai kudin na tambaye ki, Na hade
fuska kamar yana gabana. Na ce, Dubu Hamsin.
Ya ce,hamsin? Na ce, Eh, kila ma ba za su isa
ba,in kuma in bari sai ka zo mu je to. Ga
mamakina sai na ji ya ce, Me yasa haihuwar
Abdul ba a kashe wannan kudin ba? Wani bakin
ciki da takaici da ya zo min wuya, kawai sai na
kashe wayar, Ina jefar da wayar yana sake kira,
na daga ya ce, Lallai na yi kuskuren barin ki ki
fara koyarwa, daman can kika koyo sababbin
dabi’u kin rainani, ba ki da buri sai ganin nuna
husuma, to zaki dai na koyarwar in ga tsiya. Duk
da qoqarin da nai in danne maganar,ashe ta
fito,sai kawai na ji na ce, Sai me in daina mana?
Ya ce, Iye! Lallai kin rika ba laifin ki ba ne
nawaa ne da na kira ki. Sai ya kashe wayar.
Sororo na tsaya ina kallon wayar zuciyata tana
ta yi min fadan cewa ban kyauta ba, mijiki yana
son kyautata miki amma na kasa yin abin da ya
dace.Hawaye ya soma zuba a idona,na dauki
wayar da nufin in ba shi hakuri,amma sai wata
zuciyar ta ce da Allah bar shi ya karata. Sai ko
na yi tsaki na share.
Allah sarki ranar Litinin ina zaune tare da
Malamai kawaye na muna hira,sai ko na ji
shigowar sako,ina dubawa sai na ga alert ne
dubu sittin kamar minti goma sai sakon shi ya
shigo kurum cewa ya yi goma na asibiti,tausayin
shi ya kama ni. Tun ranar damuka wannan
husumar ba mu sake yin waya ba,don ya ki
kirana,take na soma kiran layin shi amma har ta
katse bai daga ba,sai na ji haushi tare da jan
tsaki. Da na koma gida ban samu Mujidat ba
duk zatona tana can gurin yawan gulmarta,sai
na ga har dare bata dawo ba, duk da cewa ba
ma shiri sai naji na damu,na kira Iya na fada
mata,ta ce ina ta je? Nace na dawo bata nan.
Ta ce to duk inda ta je ta dawo,tun da ba
yarinya ba ce. Wasa wasa har washe gari nakasa
hakura na kira shi ya ki dauka,sai na tura masa
sako cewa Mujidat fa ba ta kwana a gida ba,don
Allah ya kira ta ya ji in da take, dan ba ni da
lambar ta. Kamar mintibiyar sai ga amsa. Kar ki
damu muna tare. Shiru na zauna ina nazari, har
mun zo lokacin da Yaya zai min haka? Nan na
kira Anty Abida da kuka ina karanto mata
komai,tun daga wancan rigimar da muka yi ta
kudi zuwa yau. Ta ce abin da yayi shine daidai
ya barki kici masifarki. Cikin kuka nace, Kunki
fahimtata. Tayi tsaki sannan tace, Tunda kin rika
har kina rigima da mijinki sai ki yi ta yi. Ta
kashe wayarta. Na yi dogon tunani don in gano
laifina,amma kwanyata ta toshe,don haka sai na
watsar.
Kwanan su goma sai ga su ta zo tana ta isa da
bunkasa,ita ga ‘yar gaban goshi. Allah ya
taimaka ranar zuciya ta sumul, na musu sannu
da zuwa har da ba su abinci, su Kausar suka
soma rige rigen daukar yaronta,don in bana nan
ya kan basu shi, duk da cewa ita bata so,daga
nan na koma dakina na kwanta. Shi kan shi bai
zaci zai gan ni wasai har in kalle su ba. Ya shigo,
Ya jiki? Na ce ba inda ke min ciwo, ya ce kin je
Asibitin? Na ce eh, Na nuna masa kayan da na
siyo na baby na ce ga kayan can, ya kalla. Allah
ya raba ki lafiya. Na ce amin. Ya ce,saura wata
nawa? Na ce, Eh to, EDD dinasunce watan sha
biyu ne, yanzu kuma muna watan tara,saura
wata uku. Ya ce, An kusa, ina san nema in
canza gadajen gidan da kujeru,tunda na samu
na sai filin can.
Na ce, Au har an siya bamu da labari? To Allah
ya sanya alheri. Da sauri ya ce ta waya muka yi
komai na tura kudin ta banki ko Iya bata sani
ba tukunna. Na ce, Allah yasa alheri. Ya ce
ameen. Can kuma sai me? Ya ce, Nasan na miki
laifi na kira Mujidat bada sanin ki ba……. Da
sauri na daga masa hannu, Yaya dan Allah duk
abinda ya shafi batun matarka bana son ji
sabida bana buqatar bacin rai, don bana son in
yi wata magana ka yaba min baka Matarka ce
ku karata.sai na mike na bar dakin zuwa falo na
zauna. Aikuwa washe gari ya tafi..
Yadda akai Mujidat ta tafi Abuja kuwa, tsohon
saurayinta mai nacin sonta wanda ko yaushe
suke yin waya, shi ne ya fada mata zai shigo
Abuja tayi kokari su hadu mana. Aminiyar ta
Murfat ta dinga yi mata famfo ta je ta shirya
mata yanda zasu hadu.Don haka ta kira Aliyu
cikin kukan ta wiwi, yatambayeta dalili sai ta
fada masa kewarsa ce ta dameta, yaushe zai zo?
Yace bashi da rana domin yawan rikicin su ya
isheshi. Ya ce, Kin cika tsokana da mata ta ba
ruwanta amma zuwan ki kin maida min mata
mafadaciya. Ta ce, ba ruwa na kishin matar ka
yayi yawa, alhalin kuma ba ta kaini son kaba. To
yanzun ya zan yi don bazan iya riqe kaina har
zuwa wani lokacin ba. Ya ce, to ki taho gobe zan
zo in dauke ki,za muyi tayin waya har ki iso.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ranar da ta cika kwana hudu a can ne suna cin
abinci wayar ta ta soma ruri, ya fi kusa da
wayar don haka sai ya dauka, Uncle ya gani an
rubuta, ya ba ta ta dauka da murna ta ce,
Uncle yaushe za ka shigo Nigeria? Ya ce, Bakiga
lambar da na kira ki ba? Ina Nigeria ai, ina
Abuja. Ta fara ihu ai ita ma tana Abuja gurin
maigidanta, ga shi ma su gaisa. Aliyu ya amsa
suka gaisa,amma shi sam bai ji abin ya shige shi
ba, yana jin su har ya yi mata kwatancen inda
suka sauka, Aliyu ba inda bai sani ba, don haka
ya ce ya gane gurin,sai dai ba za ta ba, ta dinga
rokon shi wai kanin Mamantane da ke zaune a
Germany,sun dade ba su hadu ba. Da kyar ya
yarda gobe zai kaita. Washegari ya kai ta dakin
shi har suka gaisa da shi da wata da ya gabatar
masa wai iyalinsa ce, nan Mujidat ta rungumeta
tana fadin, Anty. Shi kuma ya dauki Abdul yana
nuna murna da ganin jikanshi a cewar shi, har
ya kara da cewa yaron ya biyo jinin babanshi.
Aliyu ya ce to za su tafi,sai wanda yake amsa
Uncle din ya yi rokon shi kan cewa ya bar su su
yini. Da kyar ya yarda. Mujidat sun lalace da
saurayin ta yini guda, hankalin Aliyu ya kasa
kwanciya don haka uku daidai ya bar komai ya
nufo gurinsu,sam ba su zata ba sai dai an yi
sa’a sun fito falo suna hira,ya diro ya ce su
fito.sun fito, nan ya shaka mata kudi masu
yawa,sai dai dubu goma ta cewa Aliyu ya bata.
Bayan dawowarsu ne ta yi ta siye siyenta har ta
sai wayar da ta siya a boye tana chatting, ta ji
dadin zaman Abuja rayuwar da suka yi ta kwana
goma da mijinta, da ma ta fi so daga ita sai shi
da dansu. Don haka ta sha alwashin duk
yandaza ta yi ta raba ma’auratan dan ganin
cewa ita kadai ce ta mallaki mijinta. Lokacin ni
kuma na shiga zargin cewa shi ne ya ba ta
kudade,ta je gidansu Anty Ramatu gidan da
kullum take zuwa, da yake sun fi shiri da
Ramatu, sabida ita ce mai zuga ta a kan
kishiyarta, ta ce mata Hausawa mugaye ne in ba
ta yi wani abu ta kare ta ba, to ita za takoreki.
Mujidat ta ce ina Yusufu? Kanin AntyRamatu
kenan. Ramatu ta ce, Yana dakin shi. Mujidat ta
je gurin shi ta ce, Yusuf ya maganar mu? Yusufu
ya ce, Anty ai ke nake jira mun gama magana
da yaron Bahaushene, kudi kawai yake so. Tace,
Ko nawa ne zan ba shi. Ya daga waya ‘Bari in
kira shi. Yaron ya zo, jamilu sunan shi ya san
kan computer sosai, hatsabibi ne. Mujidat ta ce
ina son a hadawa wata mata sharri ne ta hanyar
internet, yanda mijinta zai rabu da ita. Jamilu ya
ce ita ma tana hawa internet din ne? Mujidat ta
ce tana hawa,kuma mijin ya hana ta amma har
yanzun ina ganin ta.Ya ce tana saka hoto?
Mujidat ta cea’a, ya ce kina da hoton ta?
Mujidat ta ce a’a. Ya ce, To ba matsala nawa za
ki biya ni?Zan baka dubu uku. Ya ce, A’a ki ba
ni biyar, cikin sati daya zan ba ki mamaki. Ta
ciro dubu uku cikin ‘yar jakarta ta hannu (post)
ta ce, Rike wannan zan cika maka in har ka yi
min wannan aikin da kyau,sannan duk lokacin
da irin haka ta taso zan yi maka magana. Ya ce,
An gama. Nan take ya bukaci ta fada masa
sunan da matar ta bude account din ta, ya
kuma ce ko ta san wani da matar ta sani?
Mujidat ta ce a’a,sai dai tana koyarwa a
primary. Ta yi ta yi masa bayanai a kan Sadiya,
sun rabu a kan cewa zai turo mata duk abin da
ya hada a nata account din ta gani.
Kamar an jeho shi ina kwance a tsakar dakina,
sabida kowa ya san mace mai ciki da jin zufa,
har bare ana cikin yanayin zafi. Ya tsallaka ni na
dago kai cikin faduwar gaba na ce, Lafiya Yaya?
Wayar da ke gefena yasa hannu ya dauka,sai
huci yake kamar kumurcin maciji na yunkura na
tashi zaune, ina sake cewa. Lafiya Yaya? Ya
dubeni idanunsa jajir ‘Dama duk tsawon lokacin
da na ce ki rufe account dinki na facebook baki
rufe ba? Gabana ya yi mummunar faduwa,sam
na manta da shi, banama hawa. Na kalle shi.
Kawo in rufe wallahi ba na ma hawa kuma na
manta ne. Ya soma sintirin kai kawo a
dakin,sannan ya ce, ‘Kin ba ni mamaki Sadiya in
wani ya fada min ba zan yarda ba…………..
Abin tsoro sai na ga hawaye sun soma zuba
daga fuskarsa. ‘KINA BIN WANI SADIYA, DA ME
NA RAGE KI, KI KE BIN MAZA??? KASH! Kash
amadadin HALIMA ABDULLAHI K/MASHI. Ni
ANaM Dorayi nake cewa dan jin yaddaza ta kaya
mu hadu kashi hudu wanda ya fito tare da na
ukun nagode,dan Allah inna barar addu’inku
Allah yayemin damuwar dake cina,kwarrai inna
cikin damu.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Leave a Reply

Back to top button