NOVELSUncategorized

DIYAM 17

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episode Seventeen : PS: I Love You

A tsakiyar term su inna suka zo min visiting suma. Sadauki ne ya tuko su amma babu Baffa kuma babu Ummah sai Asma’u Mama da su Rumaisa. Nace “ayyah, Inna da kun sani kun taho da
Ummah, nayi missing dinta” babu wanda yace dani ci kanki a cikin su. Ranar nayi murna har na rasa inda zan saka kaina, su kuma suna ta yimin dariya. Suka zo da abinci kula kula muka hadu muka ci tare ana ta hira, amma Sadauki tunda muka gaisa ya koma mota, sai da muka gama cin abincin sannan na zuba na kai masa, ina mika masa kuwa inna ta kira ni in dawo haka na taho bamuyi magana ba. Sai da zasu tafi ya dauko bakar leda ya miko min yace inji Ummah, garin karba naji ya saka min takarda a hannu na sai nayi sauri na saka ta cikin aljihuna, yayi murmushi kawai ya daga min hannu suka tafi.

Bayan na koma hostel ina jejjera kayan dasu Inna suka kawo min, na duba ledar da sadauki ya bani naga dambun nama ne da yaji attaruhu da tafarnuwa, just the way I liked it. Nayi murmushi na dauko takardar daya bani na bude ina karantawa.

My dearest star.
Am sorry ba mu sami damar magana ba, but ganin kina lafiya kadai ya ishe ni farin ciki. Ga dambun nama nan inji Ummah tana gaishe ki.
PS
I love you.

Na dora takardar a kirjina ina jin wani iri. Na sani cewa akwai wani abu a tsakani na da Sadauki amma bai taba furtawa direct ba sai yau. And it feels great. A hankali nace “I love You too Aliyu”.

Haka rayuwa ta cigaba da kasance wa, har cikin ikon Allah muka shiga third term na js1, a lokacin shi kuma Sadauki suke zana ssce dinsu. Kullum in naga yan ss3 dinmu suna exam sai inta yiwa Sadauki addu’a, Allah ga Sadauki nan, Allah ka bashi sa’ar exam din nan. Wannan term din gaba daya baizo min visiting ba. Sai ranar da mukayi hutu suka zo daukana shida Baffa, ko dan ma kwana biyu ban ganshi ba? Sai naga ya kara girma ya kara kyau. 

Naje na shige gaban mota na barshi da daukan kaya yana sakawa a booth, Baffa kuma ya tafi zaiyi signing dina out. Na dauko powder da lipstick ina shafawa wai duk kyalliyar zuwa gidan ne, sai kawai naji kamar ana kallona, nayi sauri na kalli mirror muka hada ido dashi, ya tsaya da jaka a hannunsa kawai ya zuba min ido ta mirror, muna hada ido sai kuma kunya ta kamashi yayi saurin dauke kai kunya a rubuce a fuskarsa. Dariya kawai nayi wai namiji da kunya.

A cikin hutun ne muna gida na fara period. Ranar ina kwance a dakin Ummah ina tashi kawai naji danshi a kasana, na saka hannu na shafa kawai sai naga jini a hannu na, na kalli Ummah naga itama ni take kallo. A lokacin Sadauki yayi sallama nayi sauri na koma na zauna ina boye hannu na a baya na, ya tsaya daga bakin kofa yana kallona yace “ke kuma lafiya kike rarraba ido kamar bera a buta?” Ummah tace “ina ruwan ka da ita, tsabar sa ido me kazo yi ma gida a yanzu?” Ya shigo yana cewa “babu aiki a garejin, shine nazo gida in huta. Diyam tashi ki bani abinci” na kwabe fuska kamar zanyi kuka Ummah tace tana nuna masa kofa “tashi ka fita” yace “Allah ya baku hakuri, daga tambaya?” Sai ya mike ya fita yana waige na. 

Yana fita Ummah tace “tashi in gani” na mike, tace “kin san menene?” Na gyada mata kai. Tabbas nasan jinin haila da hukunce hukuncen sa tun a islamiyya, na kuma kara sani a kansa a makarantar boarding. Akwai yan ajin mu da suke yi, kuma seniors din mu ma sunayi dan sukan aike ni wajen wata matron in siyo musu pad, amma ban taba tsammanin zaizo gare ni ba ni Diyam, at least not now, ni ban shirya girma ba gaskiya. Ummah ta saka ni naje drawers dinta na dauko wasu undies data siyamin da niyyar in zan koma makaranta zata bani, ta saka na dauko pad itama a dakinta takoya min yadda ake sakawa sannan tace min inje toilet in gyara kaina. Ina dawowa na tarar ta gyara inda na bata a kujerar ta, sai kuma ta zaunar dani ta sake yi min bitar wankan tsarki da sauran abubuwa da suke shafi haila, ta kama kunnena tace “babu wasa da maza daga yanzu, babu wasa da Sadauki” nayi kyar kara sannan ta cika min kunne na. A lokacin Sadauki ya shigo yace “ya naji ana ambatar sunana?” Sai kuma ya kalli irin zaman da mukayi yace “hirar me kuke yi ne haka?” Na tabe baki zan saka masa kuka ya juya yace “na fita, in tayi tsami zanji”. 

Sai da muka gama maganganun duk da zamuyi da Ummah sannan tace min in tashi inje in gayawa Inna. Na zaro ido nace “Inna? Ni bazan iya gaya mata ba” tayi dariya tace “ai kuwa sai kin gaya mata. In baki gaya mata ba ke da ba’a gida kike zaune ba ta yaya zata sani?” Nace “dan Allah Ummah kije ki gaya mata” tarike baki tace “ni? Babu ruwana, ke zaki gaya mata da bakin ki” naji duk hankalina ya tashi, sai tace “bara in baki shawara. Kinga, yanzu ki tafi dakin ta, ki saka pad a jikin pant ki ajiye akan gado inda tana shigowa zata gani. Da kinji ta taho sai kiyi sauri ki shiga toilet ki buya”. 

Haka nayi kuwa, na ajiye akan gado sai da naji ta taba kofa sai nayi sauri na shige toilet. Na jima aciki,a tunani na ta fita sai na fito ai kuwa sai gata azaune a kan gado ta tasa pant dina a gaba, nayi sauri zan koma toilet tace “ke! Zo nan” na dawo ina karkarwar jiki na tsaya. Ta nuna pant din tace “wannan na waye?” A hankali nace “nawa ne” sai kuma tayi shiru tana kallona sannan tace “yaushe kika fara?” Nace “dazu” sai ta zaunar dani itama ta dora daga inda Ummah ta tsaya a nasiha da bayanan sabon yanayin dana samu kaina a ciki. Sai data gama sannan tace “saura kuma in sake ganin kun rike hannu ke da wancan bakin munafikin”.

Muna gab da komawa hutu exam din su Sadauki ta fito. Alhamdulillah, ya samu nasara sosai. Duk da dai ba distinction ya samu ba amma ya samu credits a duk subjects din daya kamata. Mukayi murna sosai. Sai da jamb ta fito sannan murnar mu ta koma ciki, yayi kokari nan ma, sai dai bai samu points din ake bukata ba a mechanical engineering wanda shine abinda yake so ya karanta. Ranar haka ya wuni ransa babu dadi, ni kuma harda kuka na zauna inayi masa, Ummah kuwa dariya tayi tace “wa kuka taba ganin ya samu abinda yake so lokaci daya? Kuje jami’ar ku tambayi daliban kuji wadansu da yadda suka samu admission din. Ko kuma ku samu mutumin daya ke da daukaka ya baku labarin yadda ya samu daukakar tasa. Babu wani abu mai kyau da ake samun sa cikin sauki”.

Baffa yana duba takardar yace “babu komai Sadauki, kar ka damu, akwai next year ai insha Allah sai ka sake gwadawa. In the meantime kuma zan nema maka computer school kayi diploma kafin ka sake jamb din”.

Ayi hakuri da wannan.
One love ????

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button