DIYAM 24
❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Twenty Four : Red Handed
Na juyo na ganshi a tsaye a gaban motarsa yana kallona, na dawo baya a zuciya ta ina karanto duk addu’ar da
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); tazo bakina na durkusa a gabansa nace “gani Alhaji” ya nuna hanyar gate “waye wancan da na ganku tare?” Nayi shiru kaina a kasa “ya sunkuyo yace “ba’a koya miki in manya suna magana ba’a yin shiru a rabu dasu ba?” Na sake yin shiru ina jin hawaye yana taruwa a idona, ya kama kunnena ya murda, nayi kara na mike tsaye yace “waye wancan nace miki” cikin azaba nace “Sadauki ne” ya sake ni ya kwalla wa maigadi kira, baba audu ya taho dagudu ya durkusa a gabansa yace masa “wanene yace kake barin ƴaƴan iska suna shigo min gida?” Dattijon ya kalle ni sannan yace “bansan baka so ya shigo ba Alhaji, da yake naga duk sanda tazo gidan nan yana zuwa gunta ne na dauka dan uwanku ne” Alhaji Babba yace “babu abinda ya hada mu dashi, daga yau in ka sake barinsa ya shigo gidan nan a bakin aikin ka. Ina fatan ka fahimta” yayi saurin gyada kai “na gane Alhaji, insha Allah hakan ba zai kuma faruwa ba, ayi hakuri Alhaji”.
Alhaji Babba ya juyo kaina yace “ke kuma muje gurin Amina ta gaya min idan da saninta kike shigo min da kattin banza cikin gida” na juya da sauri ina tafiya blindly, kafafuwana suna hardewa kamar zan fadi har na shiga dakin Inna na tarar da ita ita kadai da charbi a hannunta tana lazumi, ta dago tana kallona da mamaki “ke kuma lafiya kamar wadda aka koro? Me ya faru” ban bata amsa ba Alhaji Babba ya shigo dakin, ta mike da sauri dan hardly ne ka ganshi ya shigo cikin main gidan saboda part dinsa a waje yake. Yana nuna ni yace “kinsan Sadauki yana zuwa gurinta?” Ta bude baki tana kallona da mamaki sannan ta fara tafa hannu tana salati “Diyam? Yanzu sai da kika jajibo mana yaron nan har gidan nan? Wato duk abinda nake fada ta bayan kunnenki yake bi yake wucewa ko?” Yace “mai gadi yace min dama ya saba zuwa gurinta a duk sanda tazo gidan nan. Wato yar mitsitsiyarta da ita har ta fara jawo mana yaran banza marasa asali da tushe zuwa gida ko?” Inna tace “Alhaji kayi hakuri, anyi an gama insha Allah ba za’a sake ba. Yarinyar nan bata jin magana, babu yadda banyi da ita ba akan yaron nan tun kafin ta kai haka amma taki rabuwa dashi. Yadda kasan yadda Zainabu ta shanye marigayi haka shima yaron nan ya shanye Diyam” Yace “au kice min tafi ƙarfin ki kenan bata jin maganar ki” ya kuma kama kunnena, na saki karar azaba yace “ni in nayi magana ba’a tsallake ta a gidan nan, daga yau sai yau babu ke babu Sadauki” ya sake ni ya juya yana cewa “shi kuma duk sanda ya sake zuwa gidan nan sai ya gane bashi da wayo, sai na rufe shi naga wanda zai fito dashi, sai naga wanda ya tsaya masa a garin nan”.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Bayan ya fita Inna ta bini da kallo ina rike da kunnena ina kuka, ta koma ta zauna a bakin gado tana kallona ina jiran ta dora daga inda Alhaji ya tsaya amma sai naji tayi tsaki tace “ba kya jin magana Diyam. Ke indai akan wannan yaron ne ba kyajin magana wallahi” ta dauke kai ta cigaba da jan charbin ta sai kuma tace “zo inga kunnen” na rarrafo nazo gabanta, ta duba kunne na ta shafa min vaseline.
Ranar haka na karasa ta cikin kuncin rai da kunan zuciya tare da fargaba, ni bawai fadan Alhaji Babba ne ya dame ni ba illa furicin da yayi akan sadauki, cewa da yayi zai sa a kama Sadauki duk sanda ya sake zuwa gidan nan, na kuma san alkawarin da Sadauki yayi min cewa zai dawo yayi updating dina akan duk abinda ake ciki dangane da mahaifinsa kuma nasan Sadauki baya karya alkawari idan yayi kuma bana jin zai fara daga yanzu. Option dina daya ne dole in nemi Sadauki in yi warning dinsa kuma in hana shi zuwa duk da cewa hakan yana nufin zamu kara nisanta da juna, amna gwara hakan akan abinda za’ayi masa in yazo din.
Bayan kwana biyu duk na kara diriricewa, ko yaya naji hayaniya a waje sai inji gaba daya hankalina ya tashi inyi tunanin ko Sadauki ne yazo aka kama shi. Rannan dai sai wata dabara ta fado min. Da daddare muna zaune da Inna nace mata “ni kuwa Inna ina so in tambayeki ko muma za’a saka mu a islamiyya ni da Asma’u. Kinga duk ana wuce mu a karatu muna zaune a gida” Inna tace “Wallahi nima zancen islamiyyar nan yana raina tunda muka zo na dauka za’a saka ku amma har yanzu shiru. Amma bari in hafsa tazo sai insa Mukhtar ya kai ku ko kuma in saghir ya zo gari in roke shi ya saka ku” nace “Inna yanzu islamiyya ma sai mun jira wani yazo ya saka mu? In kin yarda kawai in bi su murja in tambayi malaman abinda ake bukata na sabon dauka” ta danyi tunani tace “shikenan, ki bisu din”. Ai kuwa na samu chance.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Washegari na shirya na kama hannun Asma’u muka je islamiyya na tambayar mana komai aka yi min bill, kamar yadda nayi tunani sai yasaiyadin yace mu shiga aji mu zauna, dai na tura Asma’u ajin su ni kuma nace zan je in dauko Alqur’ani na daga nan sai na kama hanya. Bani da ko kwandala dan haka na dauki hanya a kafa ina ta zabga sauri kamar zan tashi sama amma a raina sam banga nidan tafiyar ba, nasan gidan Alhaji Bukar inda yaya ladi take anan bayan layin mu yake dan haka nan na dosa, a ringa bi ta lunguna in tsallaka wannan titin in shiga wannan lokon bansan cewa na gaji ba sai da na ganni a kofar gidan, na tsaya a gaban mai gadi ina haki shikuma yana kare min kallo, sai da na gama tsaida numfashi na sannan nace “dan Allah baba Sadauki nake nema. Allah yasa yana nan” ya ajiye radiyon hannunsa yace “dazu ya shiga, bara in dubo miki shi” sai naga ya doshi boys quarters ana jima wa sai gasu sun fito a tare Sadauki ya doso ni da sauri fuskarsa cike da damuwa “Diyam? Lfy? Daga ina kike haka?” Na danyi masa murmushi sai naga yayi ajjiyar zuciya, ya kalle ni yace “kar dai kice min a kafa kika taho” na gyada masa kai sai ya jani zuwa kujerar mai gadi na zauna shi kuma yayi kneeling a gaba na yana mammatsamin kafata yace “me yasa kika taho a kafa Diyam? Ko menene ba zaki bari inzo ba sai ki gaya min? Yanzu da wani abin ya same ki kuma fa?” Nace “You don’t understand, gaya maka zanyi kar kazo din ai” sai na bashi labarin abinda Alhaji Babba yace.
Sai naga fuskarsa ta chanja gaba-daya yace “Diyam mai nayi wa mutanen nan ne wai? Su kansu ba zasu taba iya fadar abinda nayi musu ba haka nan kawai suke ji a ransu basa sona” ya dago kai yana kallona yace “Diyam ni nasan ba zasu bani ke ba” nayi saurin girgiza kaina nace “da sauran lokaci ai Sadauki, ka tuno abinda Baffa yace? Sai na gama makaranta na shiga jami’a tukunna? Kafin nan zasu chanja ra’ayinsu zasu fahimci ko kai waye ne. Yanzu ka yarda Alhaji Bukar ya kai ka gurin abbanka tunda wannan zai kara sassauta zuciyarsu tunda suna cewa baka da asali” ya gyada kai yace “you are right. Gobe dama nayi niyyar zanje in gaya miki cewa jibi zamu tafi. Maiduguri yace zamu je” na bude ido ina mamaki, sai kuma na fara sharar hawaye, yace “sarkin kuka, kukan menene kuma kike yi?” Nace “Maiduguri fa da nisa” yace “kuma ce miki akayi a can zanyi ta zama. Nima ai bazan iya zama a can ba zanje in gansu ne kawai in dawo nan ko dan makaranta ta ma” sai kuma ya bani labarin wani abokin Baffa da Baffan ya hada su dan yayi masa hanyar admission, yace “ranan nan bayan nayi welcome back din layina sai ya kirani yayi min gaisuwar Baffa yace min insha Allah wannan admission din dani a ciki. Kinga zan dawo ko dan makaranta ta, besides, ni bazan iya rayuwa nesa dake ba”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Na makale kafada nace “Allah yasa dai kar Borno tayi dadi ka manta da Diyam” yayi murmushi yace “maganar kike so, sau nawa zan gaya miki cewa babu rayuwa a tare da Sadauki in babu Diyam ba. Life without you will not be just unbearable it is unimaginable. I can’t imagine me without you”. Sai kuma muka shiga hira kamar bamu da wani problem, yana ta tsara min yadda yake yana planning din rayuwar mu tare, hatta fasalin yadda zai gina mana gidan mu a filin da Baffa ya siya masa sai da yayi min. Ga iskar gurin tana yi mana dadi. Jin mu muke a saman gajimare, tamkar together zamu iya facing duk mutanen duniya
Mun jima tare sannan ya duba agogon hannunsa yace “Diyam, tashi maza in raka ki ki hau daidaita ki tafi, ashe lokaci ya tura bamu sani ba”. Sai naji kuma kamar bazan iya tafiya ba kamar inyi zamana a gurinsa mu tafi Maidugurin tare amma nasan hakan ba zai yiwu ba, shima ganin yadda na damu sai duk jikinsa yayi sanyi. Ya dauko biro ya kama hannuna ya rubuta min number dinsa yace “ga numberta nan, ba wai rubutawa zakiyi a wani wajen ki boye ba a’a haddacewa zakiyi a kanki, if anything happens kafin in dawo, if you need anything ko menene ki samu aron waya ki kira ni. Kafin ki koma makaranta insha Allah zan dawo. Ki ringa yi mana addu’a” na gyada kai ina karajin jikina yana kara sanyi.
Ya raka ni waje ya tarar min adaidaita ya bashi address ya biya kudin, sai kuma ya tambaye ni in inason kudi. Na girgiza masa kai, kamar ba zai matsa ba yana kallon fuskata sai da mai adaidaitan yayi masa magana tukunna sannan ya ja baya muka tafi. Na waiga ina kallonsa sai yayi murmushi ya daga min hannu.
Daga dan nesa da gidan Alhaji Babba nace a sauke ni, ina sauka na juya da niyyar in karasa sai naji daga bayana ance “Diyam daga ina kike?” Na juya muka hada ido da kawu Isa shida wani mutum suna tafiya a kasa, na durkusa na gaishe su fuskata cike da rashin gaskiya, ya sake maimaita min tambayar, cikin in ina nace “Inna ce ta aike ni gidan Mama” ya gyada kai yace “to ki gaisheta, amma dan sahun ai daya karasa dake ciki” sai nace “zan biya ne ai ta islamiyya in tafi da Asma’u”.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Nayi sa’a ina zuwa gida na tarar an taso yan makaranta na shiga cikin su muka shiga cikin gida. Bana jin dadi kuma bana so Inna ta gane dan haka nace da Asma’u ta tafi ta gaya mata mun dawo ni kuma na bi Murja muka tafi part din Hajiya Yalwati. Muna zuwa na kwanta a kujera ina jin kamar zanyi zazzaɓi, Hajiya Yalwati ta tambayeni “lafiya?” Sai na gyada mata kai inajin kamar zanyi kuka, sai kawai ta rabu dani tana tunanin ko Baffa na tuno.
Kwana biyu bayan nan, ranar da nake lissafin su sadauki sun tafi Maiduguri, mun fito zamu tafi islamiyya sai muka tarar da Alhaji Babba, kawu Isa, Inna da Hajiya Babba suna zaune a babban palo da alama magana mai muhimmanci suke yi. Muka gaishe su har zamu wuce sai ji nayi kawu Isa yace “Amina ki daina aiken Diyam ita kadai gwara kiyi wa Hafsan waya ta bawa Mukhtar ko menene ya kawo miki” na kara sauri kamar zan tashi sama, na kusa gate kenan naji an kwalla min kira, na runtse idona na kasa motsi, “Diyam ki zo ana kiranki” murja ta dafa ni tace “number dinki ta fito, good luck, ni nayi gaba”