NOVELSUncategorized

DIYAM 25

❤️ DIYAM ❤️

By

Maman Maama

Episodes Twenty Five : A Day To Remember

Na juya ina kallon kofar palon amma na kasa motsa kafata ballantana in tafi, Inna na gami ta budo kofa a zuciye tana kallona “ba kiranki ake yi ba?” Na taho a hankali ko wacce gaba ta jikina tana rawa, ina shiga Inna ta
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); tunkuda keyata na durkusge a tsakiyar palon kaina a kasa. Kawu Isa yace “Diyam, shekaran jiya da na ganki kin fito daga adaidaita sahu daga ina kike?” Ban amsa ba kuma ban dago ba, Alhaji Babba yace “idan anayi miki magana kina yin banza da mutane sai na kakkarya ki anan gurin, ba zaki ansa ba” na fara rera kuka “dan Allah kuyi hakuri kar ku dake ni, dan Allah” Kawu Isa yace “ba zamu dake ki ba indai kika gaya mana gaskiya. Ina kika je ranar nan?” na cigaba da kuka na “wallahi Kawu na daina bazan sake fita ba”. Na dago kai muka hada ido da Inna ta rafka tahumi tana kallona, nayi sauri na sunkuyar da kaina, tace “ba zata fadi inda taje ba fa, amma ni nasan inda taje, ba zai wuce gurin wannan bakin mayen ba” ta juya tana kallon Alhaji Babba tace “rannan ba kace in ya sake zuwa gidan nan sai ka kama shi ba? To shine ita ta tafi gurinsa tunda shi an hana shi zuwa. Wato dalilin da yasa kika nace sai na saka ku islamiyya kenan ko?” Na girgiza kaina da sauri “wallahi Inna ba haka bane ba, ranar nan ne kawai naje kuma bazan sake zuwa ba” Kawu Isa yace “to me kika je yi ranar? Me ya kaiki gurinsa?” Ina sheshsheka ina kuma wasa da fingers dina nace “ce masa nayi kar ya kuma zuwa gidan nan” Alhaji yace “au saboda nace zan saka a kama shi shine kika je kika gaya masa ko? To in nayi niyyar rufe sadauki kaf garin nan akwai wanda ya isa ya hana ni ne? Yanzun ma kuma zan tura har gidan da yake takama dasu din insa akama shi a dan lallasa min shi yadda nan gaba ko kince masa zaki je shi da kansa zai hana ki” Kawu Isa yace “tashi ki tafi” nayi sauri na mike nayi hanyar waje sai Alhaji Babba ya ce “kar ki fita daga gidan nan. Kin gama zuwa islamiyya ai. Zo ki wuce ciki” na juya na bi inda yake nuna min, muka hada ido da Hajiya Babba wadda tun da aka fara maganar bata ce komai ba tana dai bina da kallo kawai.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Kitchen din gidan na shiga, na rakube a jikin kofa na cusa kaina a tsakanin cinyoyi na, me yasa ni bani da sa’a ne? Me yasa duk sanda nayi wani abu sai an kama ni? Karya sam bata karbe ni ba? Sai kuma na kama addu’ar Allah yasa Sadauki ya tafi dan kar Alhaji Babba ya aikata abinda yace.

A palo bayan na tashi inna tace “na rasa yadda zanyi in raba yarinyar nan da wannan nataccen yaron wallahi. Nayi nayi, Allah ma ta gani nayi iya kokarina amma abin ya faskara, ni farko na dauka soyayyar yarinta suke yi, na dauka in suka fara hankali zasu saki hannun juna amma kamar kara tunzura su ake yi” Alhaji Babba yace “wai soyayya suke yi?. Diyam din yanzu harta isa yin saurayi? Shekarar ta nawa?” Inna tace “sha hudu zata yi nan da wata daya” ya gyada kai yace “ta isa kam. Matanen mu na ruga basu kaita ba ma ake musu aure. Kuma wannan tunda har tasan a raba ta da saurayi ita kuma ta dauki hanya ta bishi to lallai ita ma ta isa auren” inna tayi ƙoƙarin kare ni “ya shanye tane fa, babu maganar wanda Diyam takeji sai tasa” Alhaji Babba yace “anyi daya ai, ba za’a sake biyu ba, mu ba zamu kuma hada jinin mu da mayu ba, yadda bakin cikin Manu ya kashe Inno ba zamu bar bakin cikin Diyam ya kashe Hardo ba dan haka kija mata kunne. Babu ita babu shi, in taki kuma duk abinda ya biyo baya ita ta jawo wa kanta”.

Shikenan kamar magana ta wuce, zuwa washegari na shiga harkokina sosai kamar babu abinda ya faru amma cikin raina kuma cikin sallolina ina yiwa Sadauki addu’ar samun nasara, sai inke tambayar kaina ko ya samu mahaifin nasa? Ko wacce irin karba a samu daga danginsa? Hankalina rabi yana tare dani rabi kuma yana gurin Sadauki har ya kwana uku da tafiya. A ranar da daddare aka aiko Alhaji Babba yana kiran Inna, ta dauki hijab dinta ta fita shiru shiru har na gaji da jiranta mukayi shirin bacci ni da Asma’u muka kwanta, amma sai na kasa baccin kuma nayi ta juyi ina jin wata irin muguwar faduwar gaba. Na rasa me yake yi min dadi kawai na tashi na zauna na rafka tagumi sannan sai gata ta shigo, sai kawai naga idonta kamar wadda tayi kuka amma sai ta maze tace “ke kuma me kike yi har yanzu bakiyi bacci ba?” Nace “bana jin dadi ne kawai Inna. Baffa nake tunowa” sai kuma na fara matsar kwalla, ta dauke kai tace in an tuno mamaci addu’a akeyi masa ba kuka ba” sai ta wuce can karshen gado ta zauna ta jingina kanta da jikin gadon, naso in tambayeta in wani abun yana damunta amma nasan ba lallai ta bani amsa ba dan haka sai nayi shiru na koma na kwanta ina kalllon ceiling, mun jima a haka sannan tace min “Diyam Baffanku ya mutu ya huta, mu da muke duniyar mu mune cikin wahalarta” na runtse idona ina tunanin ma’anar maganar ta ta.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Washegari bayan na tashi da assuba nayi sallah sai na koma baccin safe, cikin bacci na kawai naji muryar mama a dakin na farka ina mamakin me take yi a gidan da sassafe? Sai naji Inna tana cewa “ni wallahi Hafsa kinfi kowa sani, bana son yaron nan sam zuciya ta bata sonsa ballantana har inyi sha’awar ya zama surukina amma duk da haka saghir fa….” Sai kuma suka ga ina kokarin mikewa sukayi shiru. Na tashi na gaishe da Mama, sai naga fuskar Inna still akwai bacin rai idonta kamar batayi bacci sosai ba, sai kawai naji ina son inji maganar da suke yi. Sai na bude toilet na shiga na rufe na kunna pampo kamar zanyi wani abu amma sai na dawo na sakakunne na a jikin keyhole. 

Sai naji Mama tana cewa “wannan gajeriyar matar tasa ce zata kissima masa, shi kuma ya hau ya zauna saboda son kansa, amma suma kansu sunsan ai Diyam ba sa’ar auren Saghir ba ce ba, ya ninka ta a shekaru fa, gashi da budadden ido ita kuma fa? Yarinyar da junior waec kawai ta rubuta? Akwai cutuwa sosai a hadin su” Inna tace “babu fa abinda ban gaya masa ba jiyan, sai yaji haushina ma wai ina so in nuna ni na haifi Diyam basu ba, wai ita suke wa gata, wai baza ta taba samun miji irinsa ba, wai gata suke yi mata albarkacin zumunci albarkacin maraicinta” ta danyi tsaki tace “ni da ace Diyam ta fi haka girma ne, da ace misali ta gama makaranta ne wallahi da bani da dumuwa. Ni yanzu abinda nake so kice masa idan kinje shine, ki roke shi a bar yaran su daidaita kafin ta gama makaranta”.

Na sulale ma zauna a kasa a jikin kofar. Naji dai suna maganar aure, kuma naji sun ambaci sunana sun kuma ambaci sunan Saghir. To tambaya ta anan itace auren wa za’ayi? Aurena za’ayi ko auren saghir za’ayi? Dan kaina ba zai iya daukan aurena da saghir a sentence daya ba ballantana ƙwaƙwalwa ta ta fahimci cewa aure za’a hada ni da saghir. Na wanke fuskata nayi brush na fito ina murmushin yake, suma duk yaken sukayi min har na zauna na fara breakfast sai na lura duk sun zuba min ido suna kallona. Sai na samu kaina da tattauna abincin amma makogwarona yakasa budewa ballantana in iya hadiyewa.

Muna nan zaune babu mai magana sai ga aike aba kiran Mama inji Alhaji Babba, ta tashi ta tafi muka cigaba da zama ni da Inna sai ga wani aiken wai inna taje itama, tana tafiya na rufe abincin gabana na tashi na kwanta a kan gado trying hard not to think, trying hard not to let my brain assess maganar da naji su Inna suna yi. Ba zan iya tuna adadin mintina ko awannin da suka wuce ba sai ga yarinya an aiko wai inzo inji ana kira na a palon Alhaji, na tashi na saka hijab dina still trying not yo think na fara tafiya blindly zuwa part din Alhaji Babba. 
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Na murda kofar na shiga da sallama. Duk suka dago kai suna kallona kamar yadda nima nake bin su da kallo. Alhaji Babba, Hajiya Babba, Inna, Kawu Isa da kuma Mama. Na durkusa na gaishe su da muryar da a kunnena naji kamar ba tawa ba. Suka amsa sannan duk suka zuba min ido suna kallona. Alhaji Babba ne yayi magana “Diyam a matsayin mu na iyayenki wadanda baki da wadanda suka fimu kaf duniyar nan mun yanke shawara a kanki. Zamu hada auren zumunci tsakanin ki da yayanki Saghir”.

“Dama an jima da bani shawarar cewa babban abinda zai saka Saghir ya zauna a guri daya ya nutsu shine in na samu kyakykyawar yarinya na aura masa, tun a lokacin Diyam ce ta fado min a raina na kuma kuduri aniyar hada su aure in ta isa auren, to kuma yanzu ganin har ta fara iya bin saurayi zuwa gidansu na fahimci ta isa auren a yanzu, dan haka za’ayi yanzu. Diyam zaki cigaba da karatu kamar yadda mahaifiyar ki ta bukata, amma ba zaki koma makarantar kwana ba, za’a saka ki a day ki karasa secondary, in kin gama in mijinki ya yarda sai ki cigaba in bai yarda ba kuma shikenan. Bamu saka rana ba tukunna, na kira shi Saghir din nace masa lallai ya hawo jirgi yazo ya gobe ina nemansa, in yazo sai muji tsare tsarensa sai mu samu saka lokacin. Shikenan abinda zan ce miki Diyam, tashi ki tafi”.

Na tashi kamar yadda yace, amma sai kafafuwana suka lankwashe na fadi a gurin, Inna da Mama suka yo kaina a tare amma kafin su karaso na sake mikewa na kama hanyar na fice. Bansan ya akayi nazo ba kawai sai gani na nayi a dakin inna, na durkusa a gaban gado gabaki dayan jikina yana karkarwa kamar ana kada mazari amma idona babu hawaye, lallai wani tashin hankalin yaji gaban kuka. Baffa naji ya fado min arai, na tuna maganar sa sanda yake mana fada ni da sadauki “waye kuke tunanin zaiyi muku aure yanzu? Ba dai ni babanku ba” ashe haka maraici yake? Ashe haka rashin gata yake?

A gefe na naga handbag din Mama, na dauka da sauri na bincike da dauko wayarta, babu tsoro ko kadan a raina nayi dialing number din da Sadauki ya bani. 

Ring biyu ya dauka, muryarsa as clear as yana gabana a tsaye wannan yasa na samu relief na san at least lafiyar sa kalau. Yayi sallama amma ni sai na kasa magana saboda karkarwar da baki na yake yi, sai kuma kuka ya kwace min. Na fara rera wa ba kakkautawa nan take ya rikice “Diyam?? Ya Salam Diyam kiyi min magana menene? Me ya faru Diyam? Please talk to me” shima kamar zaiyi kukan, na tsagaita nace “Sadauki ka taimaka min, Sadauki aure za’ayi min wai” yayi shiru kamar baiji ba sannan yace “what?!!!” Nace “yanzu suka kira ni suka gaya min, aure zasu yi min Sadauki, wai hamma Saghir zasu aura min” yace da sauri “su? Su waye su? Diyam kar kiyi min wannan wasan bana so” na lissafa masa duk wadanda suke gurin sanda akayi maganar nace “da gaske suke Sadauki, wallahi da gaske suke, Sadauki mutuwa zanyi ka taimaka min”. Yace cikin muryar da ban taba jin yayi magana da irinta ba “Diyam listen to me, zan ajiye duk abinda nake yi zan taho kano gobe and I promise you I will not let anything bad happens to you”. 
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Kofa ta bude inna da Mama suka shigo fuskarsu babu yabo babu fallasa, sai kuma suka tsaya suna kallona da waya a hannu ina kuka. Na sauke wayar daga kunne na ina ji a raina bana jin wani tsoro kuma, wanne punishment za’a yi min wanda yafi wannan da aka riga akayi min?

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button