DIYAM 9
❤️ DIYAM ❤️
By
Maman Maama
Episode Nine: The Gamer
Tabbas maganar da Diyam ta fada wa Bassam bashi kadai ta taba ba, har ita
. Tana fita daga ajin taji kanta yana wani irin juyawa kamar zata fadi, duk reality din rayuwar ta yana dawo mata. Tun da tazo UK take living in a dream yanzu kuma ta farka, gobe kuma zata kara farkawa tunda gobe zai zo bata san kuma da wacce zai zo ba. As far as he is concerned yayi winning over her dan haka zata bi abinda yace kenan. Ta samu jikin wata bishiya ta jingina tana mayar da numfashi, a nan taji karar shigowar text wayarta, ta dauko a jaka ta bude taga wanda take tunanin ne ya aiko mata da message
“Tell him I say hi, kafin inzo mu gaisa gobe”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ta sake karantawa, ta nanata amma ta kasa making sense of it. “Him?” who is him?. Wata karamar murya a can kasan zuciyarta tace “Bassam” ta zame ta durkushe a gurin, so he knows about Bassam? Abinda take ta gudu kenan gashi nan bata yi escaping ba. Amma ta yaya yasan labarin Bassam? “Murjanatu” muryar ta sake fada mata.
Ta mike and for the first time ta tari cab saboda yadda take ji ba zata iya tafiya a kafa ba. A motar ma dunkule wa tayi dan ba zata iya zama straight ba saboda wannan abin daya dunkule mata a ciki har yanzu bai saki ba, sai da drivern yayi mata magana sannan ta san sunzo, ta bashi kudinsa ta shiga ciki. Tana bude kofa idonta ya sauka akan Murjanatu a zaune tana facing kofa, suna hada ido Diyam tayi realising gaskiya, ba Murjanatu ce ta gaya masa ba. Murjanatu ta mike tana twisting hannunta tace “Diyam, yaya yasan kuna tare da wannan yaron” Diyam ta bita da kallo bata ce komai ba, Murjanatu ta cigaba “wallahi bani na gaya masa ba, I wanted to tell you tun jiya ya kira ni ya tambayeni wai waye kuke yawo tare dashi a school nace masa ni bansan kina yawo da kowa ba, he said in bangaya masa ba in yazo sai na sani. To dazu kuma ya kira yace min nayi masa karya kuma sai na gane kure na” still Diyam bata ce komai ba, kallonta take kawai tana lura da yadda tsoro ya fito baro baro a kyakykyawar fuskarta. Ta taho ta zagaye ta zata shiga corridor Murjanatu ta mike ta rike hannunta tace “Diyam am sorry akan maganar shekaran jiya, wallahi bansan betting kuka yi a kan wani abu ba, ni kawai cewa yayi min zamuyi playing game, yana so in nuna miki da gaske yake zai kori Judith, please Diyam kiyi hakuri bana son alakar mu ta baci a saboda wannan” ba tare da Diyam tace komai ba ta zare hannunta daga na Murjanatu ta shige dakinta ta rufe kofa. Direct toilet ta shiga, ta cire kayanta gaba-daya ta shiga shower ta kunnawa kanta ruwan dumi. Ta lumshe idonta tana jin dadin yadda ruwan yake sauka a kanta, tana jin duminsa yana narkar da daskararriyar zuciyarta, tana jin jijiyoyinta suna warewa suna aikawa da sakonni kwakwalwarta. Ta tuno abinda Murjanatu tace “a game” of course it is all a game, shi komai a gurin sa ai game ne. Ta tuno wata magana daya taba fada mata shekaru da dama da suka wuce
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
“Diyam, life is like a game of chess, the secret to winning is to observe the movements of your opponent, think deeply and make your move”
Amma abinda ya kasa ganewa shine a yanzu bashi da opponent din, shi kadai yake buga game dinsa, kuma ya kasa realizing cewa a haka zai zo yayi hurting others, innocent mutane kamar Bassam. Ya kasa realizing cewa duk abinda take yi tana yi ne for him not against him. Shi kawai burinsa yayi winning, no matter the cost. Ita kuma burinta shine ya ajiye wannan game din ya duba reality, ita bata son wannan game din nasa mai ban tsoro, dan last game din da ya buga didn’t end well, it ended with someone in jail for life, someone very important to her.
Ta kashe shower din ta fito ta daura dogon towel sannan ta dauki karami tana goge fuskarta da dogon gashinta dashi, a ranta tana kokarin placing kanta in his place daga nan sai taga menene next move dinsa. Amma duk iya kokarinta ta kasa guessing menene zaiyi a next move dinsa. Ta fito ta dauki wayarta data ajiye tana dubawa, sai a lokacin tayi realising cewa for the first time tun zuwanta kasar yau ne rana ta farko da bai kira ta ba, hakan yana nufin yayi fushi da ita, fushi kuwa mai tsanani. Ita dai tasan har ga Allah bata fara kula Bassam saboda wani abu ba, ta fara kula shine saboda maganganu marasa dadi data fada masa a farkon fara maganar su, wannan yasa ta sauko da niyyar ta wanke kanta a gurin sa kuma sai abota ta shiga tsakaninsu. Ita tasan ko da da digon zarra bata jin wani feeling a kan Bassam wanda ya wuce na mutumta juna da aminci.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ta shirya cikin doguwar rigar zaman gida, ta kwanta ta dauki pillow ta dora akan cikinta ta rungume, sai a sannan ta tuna cewa ko breakfast bata yi ba amma kuma yunwa is the last thing a mind dinta. She just want to know wanne mataki zai dauka, she just want to make sure ba zaiyi hurting kowa ba akanta. Tana nan kwance ita ba bacci ba ita ba ido biyu ba har lokacin sallar zuhr yayi, tayi alwala ta sauke farali sannan ta fito parlor, babu kowa dan haka tashiga kitchen ta dafa noodle ta zauna akan stool taci sannan ta wanke plate da tukunyar data bata ta dauki bottled water ta fito parlor ta zauna tana sha. Dai dai nan Murjanatu ta fito itama da shirin tafiya school. Ta dan zauna a gefen Diyam amma bata ce komai ba. Diyam ta mike ta shiga daki ta dauko dogon hijab ta saka tayi hanyar waje, har ta taba kofa taji Murjanatu tace “Diyam” sai ta juyo ta dawo kusa da ita ta zauna ta rike hannayenta a cikin nata tace “don’t worry. He won’t hurt you, not while am here”. Sai kuma ta tashi ta fita da sauri.
Tana fita ta tari cab, since ta kasa sanin wanne mataki zai dauka ita zata dauki nata matakin da kanta. Bata san hotel din da Bassam yake ba dan haka direct mall din da yake aiki ta tafi. Tana kallon irin kallon da mutanen gurin suke yi mata kuma tasan yana da alaka da dogon hijab din da ta saka amma bata kula su ba ta cigaba da harkokin gabanta. Customer care ta tafi ta tambayi matar gurin agame da ma’aikacin su mai suna Sadiq Abubakar Sadiq. Daga farko kin bata wani information tayi a kansa for security reason, sai da tayi mata karyar ita friend dinsa ce ta yi loosing phone dinta ne kuma tana nemansa emergency concerning harkar karatunsu, sai da matar tayi checking taga sunan makarantar da kuma department din da Diyam din ta gaya mata yayi tallying da information din Bassam sannan ta gaya mata cewa bai shigo yau ba, amma ta gaya mata sunan hotel dinsa. Godiya Diyam tayi mata ta fita ta nufi address din da aka bata. A reception ta tsaya tasake yi musu bayani irin yadda tayi wa waccan matar amma suma suka hana ta hawa sama instead sai suka kira dakinsa through intercom, yana dauka Diyam ta karbi phone din tace “Bassam? Diyam ce. Can you come down for a minute? Ina son magana da kai please” daga can barin Bassam bai ce komai ba dan ji yake kamar in yayi maganar ma voice dinsa ba zai fito ba, sai kawai ya ajiye wayar. Diyam ta ajiye itama a ranta tana kissima cewa yayi fushi ne shima. Amma sai ta kasa fita, sai ta samu guri ta zauna tayi folding hannayenta ta zuba idanunta akan kofar lifter da take ta sunturin kai mutane sama da sauko dasu. Tafi minti sha biyar a zaune sannan ta mike cikin sanyin jiki da niyyar fita, a lokacin ne kofar lifter ta bude ya fito. Sweater ce a jikinsa mai hade da hula wacce ya jawo ya rufe kusan rabin fuskarsa dan haka ta kasa karantar emotions dinsa amma sai taga a idonta kamar ya dan rame kadan. Ya tsaya a gabanta ba tare daya ce komai ba, tana jujjuya hannayenta tace “Bassam magana nake so muyi please in babu damuwa” ya danyi gyaran murya sannan direct yace “are you married? A yanzu nake nufi” da sauri ta girgiza kanta tace “of cause am not” ya gingina kai sannan yayi hanyar waje ba tare daya kuma cewa komai ba ita kuma ta bishi a baya.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Baya suka zagaya, suka jera suna tafiya a tare, suna taka kafafuwansu a tare, amma daga ka gansu kasan akwai tension a tsakanin su. Wani garden suka shiga sannan suka je cikin wata rumfa suka zauna, gurin very quite duk da cewa akwai mutane jefi jefi suna hutawa a gurin, can kuma dan nesa dasu kadan swimming pool ne a zagaye ta fitulu mutane suna wanka a ciki. Ta daga ido tana kallonsa taga shima itan yake kallo, suna hada ido yace “uhumm? Ina jin ki, kince kina son magana dani” tayi kasa da nata idon tace “Bassam am so sorry ban gaya maka all these before ba, nayi haka ne saboda banyi tunanin da akwai bukatar in gaya maka din ba, yanzu kuma nace zan gaya maka ne saboda ka fahimci dalilina na daina kula ka, kasan cewa am doing it for you” ya katse ta “for me? How is that so?”
Ta bude baki zata yi magana wayar ta tayi kara. Ta dauka tana dubawa wa, “Inna” ta danyi murmushin takaici ta ajite wayar, of cause Inna, of cause gurin Inna zashi ya shirya mata wata dramar kuma, tun dazu abinda take tunani ga amsar ta bayyana yanzu. Tasan wannan ba kiran Inna ba ne ba dan tun da tazo kasar nan Inna bata kiranta dan tace ita bata gane wannan lissafin lokutan dan haka sai dai ita Diyam ta rinka kiransu ko kuma in Asma’u tana gida sai ta kira.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Har wayar ta katse bata dauka ba a take kuma aka sake kira, Bassam ne ya daga wayar ya ga sunan da yake kira yace mata “ain’t this important? Ba innar ki bace?” Ta karbi wayar ta daga kiran, sai kuma ta saka a handsfree yadda Bassam zaiji abinda ake cewa, maybe abinda zai ji ya taimaka masa wajan fahimtar ta. Tayi sallama, daga daya barin inna tace “Haleema ya karatun? Ya ‘yar’uwar taki?” Diyam tace “lfy lau muke inna ya kuke?” Inna tace “uhmm. Ni ina naga lfy kuwa? Kullum hankalina a tashe, ni dai har yanzu zuciyata bata kwanta da wannan karatun naki a kasar turawa ba Diyam” Diyam ta lumshe idonta tace “Inna ba mun gama wannan maganar ba tun kafin in taho? Inna ke da bakinki kika nuna hakan da nayi shine dai dai, yaushe kuma kika chanza ra’ayinki ” Inna tace “zancen lokacin da na chanza ra’ayi duk ba shine mai muhimmanci ba, abu mai muhimmanci shine na chanja ra’ayin nawa. Ni ban yarda da zamanki a kasar waje ke kadai babu miji ba, dan haka cikin biyu zaki zabi daya, ko dai ki hakura da karatun ki dawo gida ki zauna a gaba na ina kallonki har lokacin da kuka shirya auren naku ko kuma a daura auren yanzu in yaso ya taho kuyi ta zaman tare, tunda shima yana da nasa harkokin a nan kasar”. Diyam ta shafa fuskarta ta taji ta dauki zafi kamar mai zazzabi, ta kalli Bassam taga ita yake kallo shima fuskarsa cike da tambayoyi. Inna tace “kina jina shine kika yi shiru ko?” Diyam tace “Inna bashi wayar muyi magana” Inna tace “wa?” Diyam tace “nasan yana nan a gabanki Inna saboda kalmomin da kika fada ba kalmomin ki bane ba, nasa ne, shi yazo ya gaya miki su, to gwara ni ya gaya min a kunne na inji” Inna tace “au, wato abinda Ingilan ta koya miki kenan? Tun yanzu Diyam?” sai kuma suka ji muryar wani a background, can kuma sai ga muryarsa fes ta fito, very deep and very clear, yace “yes, I am here” Diyam ta hadiye wani abu a makogoronta cikin rarrauniyar murya tace “this is not the agreement, ba haka muka yi alkawari ba” yace “ba haka mukayi alkawari ba and yet you broke the promise” da sauri tace “I didn’t, believe me I didn’t” yace “we will see about that, tomorrow” daga nan suka ji shiru ya kashe wayar.