DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ciki tashi hankali da razana tasake tace” Aliyu din, inalilahi wayyyooo nashi ga uku na Ina gada gana yashiga ” ta fashe da kuka ta sake walking stick din Kamar zata fadi, Tycoon da sauri shi ya rike ta..

Yace” Ummi Kar ki tada hankali ki za’agashi insha Allah nayi waya da commissioner yansanda, ya tura yarashi a bazama nemeshi, Kar kidamu Ummi” Yana magana muryashi na rawa”..

Ummi ta share hawaye tace” toh naji, Umaru nasa kawai dauriya kake yi , wuce ciki kasamu ka huta”.

Ya girgiza Kai yace” Ummi bazataba samu wani kwanciya hankali ba har sai Naga Aliyu, kiyi hakuri Ummi”..

Ummi tace” Aya Umaru Kar kadaga hankali da yawa fa, Ina zuwa”… Sai gata ta fito,Yan aiki maza ne biyeda ita suna rike da babba daddurma da plastic chair, Uncle Bello nabinsu a baya hannushi rike da bottle water…

Ummi tace” Kai ku shimfida a gabanshi”… Suka shimfida, taje kusa da je kusa da Tycoon da sai safa da marwa yake, wayoyyishi sai Kira akeyi yahanasu amsawa.. jikishi sai Bari yake…

Ummi tace” Umaru zauna ka huta “..

Yace” Ummi kiyi hakuri, baza iya zama ko samu sukuni ba har sai Naga Aliyu “..

Ta kada Kai Tana hawaye tace” haba Umaru da wane zamuji , dubi fa Bari kakeyi a tsaye, Dana shiga ciki maihaifiyarshi ta Kiran, tana kuka Wai kaki daga wayoyisu, Alama dai kenan kana fushi dasu, haba dawane zamuji” ta fada Tana share hawaye…

Yace” ya’isa Ummi daina kuka, bayi fushi dasuba, gashi zan zauna… Ya zauna.. ” Abba Salma mu zauna”..

Ummi ta gyara zama tace” inba fushi kakeyi dasu ba, gayamun Maiye dalilika na ki daga musu waya, Aliyu ko da masu Kama da gunki na(guards ????) ya fita in Allah ya rubuta wani abun zai samaishi toh fa bazai tsalake ba saiya faru, saboda haka ka kwantar da hankali ka insha Allah za’agashi ciki koshi lafiya kuwa, ba abunda zai samaishi, Kuma ai Aliyu ba yaro bane”..

Uncle Bello yace” gaskiya ne Ummi, insha Allah za’agashi”.

Yace” Allah yasa” ya Mike tsaye

” Ina zakaje? Ummi ta tambayeshi

Yace” masalaci zanje Ummi, ankira sallah la’asar”..

Baigama rufe baki ba bodyguards Mai rike da wayoyyisa yazo da sauri yace”Sir, commissioner ne ke kira”..

Ya amsa da sauri yasa a kunne yace” hello kungashi?”..

Daya bangare commissioner yace” Sir lungu da sako, ciki gari da baya ta, hanyoyi titituna ba inda bamu duba ba, yallabai ka Kara hakuri, dakaina nayi jagora , ama Kar kadamu yallabai zamu Kara himma, sai aganshi yau Dina ba gobe ba”..

Tycoon duk ya firgita baiya magana sai bin waya yake da kallo… Karshe ma katse Kira yayi …Ummi sai kuka..

Yasa hannu a baya yaje ya dawo*2 iyayi sai furza da iska..

Can yace” Abban Salma kashiga da Ummi ciki ni zanje sallah “..

Ummi tace” Umaru zaka iya fita jiki ja fa yannuna bakada lafiya ?”..

Yace” Kar kidamu Ummi sallah zanyi”..

Ya wuce bodyguards na binshi a baya hagu da dama, fuskar na ya hadashi tam kamar baitaba dariya ba, har yakarasa baki masalaci, dakanshi ya dura ruwa a tap yayi zauna yayi alwala hannushi na rawa saboda baci rai, mutani masalaci kam sai mamaki sukeyi yau tycoon ne a gabasu, mutumi da suke gani a tv yau ganshi su ganshi a zahiri…. Yana idar da alwala ya wuce zuwa ciki masalaci guards zasu bimshi ya dakatar dasu da hannu, baya an tada jam’i suyi sallah su idar, ya zauna yadade a zauna Yana roko Allah yabayana mishi Aliyu shi …sai misali karfe biyar ya fiti, jiki shi duk yayi lagwas, guards ne a baki kofa masalaci suna jira fitowa shi, da Uncle Bello hardasu commissioner, hannu kawai ya daga musu bai yi maganaba, ya tsaya shiru sai bi anguwa kawai yake da kallo….

Shiru shiru bakaji motsi, yakai dubanshi ga gate dinsu Ummi.. kawai idonshi ya sauka a wata motar kirar range Rover, can Parker nisa da gate din, ya tsaya shiru Yana kallon motar.

sai ga commissioner ya karaso gefe shi” Sir munkarasa ciki ko, yamma nayi Sir,Naga alamu sunu na kamar bakaji dadi”..

bai amsaba,shidai hankalishi kawai na kan motar na.. ” Abba Salmah waye da motar na a anguwar na daya Parker shi a gefe gidaka? Ya jefa ma uncle bello tambaya..

Uncle bello yace” yallabai wata motar kenan ni bagantaba?”..

Yayi nuni da motar dake can a Parker a gefe gate… Inbaka lura ba bara kasan da wani motar aguriba..

Uncle Bello yace” Kai gaskiya babu, ama basan dai ko wani bako bane mukayi..”

Dai dai lokaci da suke magana aka motar, iska ya kada, kofa ya bude dayake ba rufewa akayiba, an jigina ne, Tycoon yaji gabanshi ya fadi, dun kamar ya hangi mutum a ciki, ama baigani sosai saboda akwai Dan tazara a tsakani su…

Ya Soma tafiya yanu fi guri motar….

Commissioner yace” sir Ina zakaje kuma?”..

Hannu kawai yadaga minshi(Ashe Aliyu yayi gadone)…. Yayi Tata ki har guri motar ama baikaba yaga ko waye ba..

Comment &share????????????????

????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️
DOCTOR ESSHA
????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️????‍⚕️

Writing by J Hajara

????MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION????????️

Kungiya d’aya tamkar da dubu.masu Nazari da Aiki da ilmi, burin ‘kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoya ta.????????
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa


2️⃣9️⃣&3️⃣0️⃣

Har zai juya kawai ya hangi hannu mutum ya fito, da sauri yakarasa guri motar, gabanshi na faduwa , Yana karasawa wa zai gani Aliyu ne, kwance shabe*2 kamar baya numfashi, ya yake salati da Karfi sanda su commissioner suka firgita, da sauri su su ka karasa wajan, Tycoon yakara bude kofar backsit din yashiga ya talafoshi, abunda yakara razana shi gani jini da ke jikishi yasa yakara rikecewa, ya talafo fuska Aliyu yace” Aliyu bude idoka nine Aliyu, nace ka bude idonka daddy ne”

Su commissioner da karaswasu kenan suka taimaka mishi aka fitar da Aliyu daka ciki motar,, Tycoon duk ya rikece dagani hali da Aliyu keciki..

Commissioner yace” yallabai ka kwantar da hankali ka tun da aganshi….

Tycoon ya katse shi da cewa” maza ku Kira min ambulance “…… Ciki hanzari uncle bello ya Dana kira number ambulance din hospital dayake zuwa, bada jimawa ba suka karaso….. tycoon dakashi ya sukuce Aliyu yasashi a motar ambulance.

Dai dai Ammi na Kira waya uncle bello, ya amsa, yaji duk murya yaji duk murya a shake Alama Tasha kuka tace” Yaya haryanzu fa bw Aliyu ba labarishi gashi har magriba ta gabatoh”

Uncle Bello yace” Hajara, alhamdullila Zaki ce don aganshi, yanzu haka asibiti za’ayi dashi, ki kwantar da hankali ki”

Ammi ta rude da taji cewa” za’akaishi asibiti tace” subhanallahi, maiyesameshi? Aina aka gashi? Aciki wani hali? Ta jero tamboyoyi duk lokaci daya….

Uncle Bello yace” hajara wa na tamboyoyi haka nace ki kwantar da hankali ki”

Ciki tashi hankali tace” a’a Yaya gamuna zuwa” ta kashe..

Aliyu kam tuni aka wuce dashi wani babba private hospital dake ciki gari kaduna, likitoci ciki gagawa suka karbeshi, ana bashi taimako gagawa .. .

Tycoon ya kasa tsaye ya kasa zaune, sai ziriya kawai yake a baki daki, addu’a kawai Allah yasa Aliyu ya farka, ya fi hour daya, haka ma guards duk inda yabi sai su binshi da sorry sir”.. commissioner da uncle Bello su na ta rokeshi ya zauna ya huta, ko kulasu baiyiba, harsu Ammi suka karaso, duka family din, hardasu Suleiman..

Likitan ya fito daga daki, da sauri Tycoon ya nufeshi, Ammi da Mami ma haka, don dagani alamu shine likitan

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button