DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Daddy karami da sai sharce gumi yake ya girgiza Kai yace” likita ka ceto rayuwa ta da Allah, Kar wani abun yasameta, zanje na sanar ma iyeyeta da Allah likita”

Dr Abbas ya girgiza Kai ciki tausayi ya shige daki da aka kaita, tashi hankali sosai ya ziryace shi gani hali da take ciki, ya Raya aranshi Aya ba fyade aka mataba… Ya Kira nurses Nan suka dafa masa, suna kokari tsayar da jini dake fita ta kasanta” ya Allah!! Wani Rashi Imani ne haka? Ya fada ciki tsoro gani hali da yariya ta ke ciki…

Fitowa yayi baya suyi nasara tsayar da jini dake zuba a kasata, Allah yasa ma tana da isashe jini imbahakaba har Kari jini sai amata(Aliyu yayi babba aiki????) su sa mata leda ruwa da allurori ya Kuma Basu umarni da suyi mata dinki a jikita…

A can gidasu Essha kuwa, family din su shiga tashi hankali, na Rashi zuwa su Essha, tayi, Dan tun two suke expecting dawuwarsu, ama gashi har magriba tayi Basu karasoba…

Daddy Essha sai ziriya yakeyi a ciki parlour rike da waya a hannushi, mummy ne gefeshi zaune kan dogo sofa din parlor ita da anty zainab , ta zuba tagumi ita Sam hankali ta bai kwanta ba tafi kowa daga hankali, su amir su na islamiya.

Daddy Yana ta trying duka lambobisu baya shiga, ya Kira Big mum can k.d ta shaida mishi cewa tun safe suka tashi, Killa hold up ne ya rikesu a hanya…

Anty zainab tace” Alhaji ka kwantar da hankali ka za su karaso, kila haka dine, kasa yanayi hanya”

Mummy ta yarfa hannu kamar Mai shiri kuka tace” haba mana, go slow tun safe ace har yanzu Kuma ana trying lambobisu baya shiga, Wana wani iri go slow tun safe haryanzu, Kai ni gaskiya hankali na bai kwanta ba”

Aina’u tace” mummy sha’ani network ne Kar ki daga hankali ki inshallah zasu karaso ciki koshi lafiya” Tana rufe baki suka ji horn din motar , an bude gate, da sauri suka fito har suna rige rige.. Daddy da ya rigesu fita yaga Ashe motar su amir ne sun dawo daga islamiya, suna fitowa daga motar, mufeedat ta nufi daddysu tace” daddy sis Essha ta dawo?

Ya girgiza Kai yace” autar mama don’t worry kinji sis Essha suna zuwa ” ya fada Yana shafa mata kai…

Amir yace” daddy datzu da muka fita break na Kira layi sis Essha Yana ringing Bata daukaba”

mummy ta zabura ta nufeshi tace” layi ya shiga? Kara trying amir”. Ya fida waya daga ciki aljihu ya dialing number Yana ringing ama ba’adaukaba..

Tace” Kara trying na daddy karami ko na hajiya” duka layi in yakira Yana ringing ama ba’adauka..

Anty zainab tace” hmm Allah yasa dai lafiya suke… Bata Gama rufe baki ba sukaji horn din motar, atare duksukayi ajiya zuciya… Daddy yace” gasunna ma su karaso”

Gate man na bude gate, daddy karami ya shigo da motar ko Gama parking baiyiba ya sauko a firgice Yana haweye ya nufi Daddy.. suka binshi da kallo mamaki gabasu na faduwa…

Daddy yace” lafiya ya na gaka a haka Ina saurane? Jini Maine Kuma a jikika?

Daddy karami duk ya firgice sai sharce haweye yakeyi yace” Essha, Essha …. Mummy da Daddy dam sukaji gabasu ya fadi..

Daddy yace” Ina Essha din, maiye samaita? Accident kukayi komai ya jera mishi tamboyoyi a take har jikishi na rawa..

Daddy k. Yace” tana asibiti, ku zomuje, ku yafeni nakasa rike amana, kunyafe nakasa Kare Essha””

Mummy taji kanta na juyawa tace” Wai Mai kake nufi ne? Wani asibiti ? Maiyesameta? Ta fada Tana haweye…

Yace” ku zomuje ku zomuje” mummy ko hijab Bata dauka ba, dogo rigane a jikita sai mayafishi ciki tashi hankali suka dunguma sai asibiti… Hajiya suka samu a baki kofa ba’abunda takeyi sai kuka, har da shesheka da sauri mummy ta nufeta tana hawaye ta dafata murya na rawa tace” Essha na ta mutu ko? Hajiya ta girgiza Kai.. mummy tasa kuwa kamar ta zare tace” ki gayamin gaskiya Kar ki boyemin da Allah hajiya, ta mutu ko? Kamar zautaciya takeyi…

Daddy ya janyeta yace” ya’isa “

” No ka kalleni Ina Essha , Ina take?

Hajiya bataiya cewa komai ba tayi daki da aka kwantar da Essha da hanzari suka bi bayata, suna shiga suka tarda Essha kwance hannu da drip, da mugu sauri mummy ta karasa wajenta tana girgiza ta da dukkani karfita, ama Essha ko gezau, Kara tasaki Mai karfi Wanda amonsa yacika daki da suke.. “ESSHA” ta fada Tana Kara girgiza ta, ciki tashi hankali idon ta ya sauka aka kafata , taga layi jini nabin kafata, ta Kara kallo da kyau, na kafa damata har yasoma bushewa, tasa Kara a karo na biyu, ta Mike ta nufi saiti kafa ta daga dogo riga ta leka,Nan take ta runtse ido, kirjita ne ya shiga bugawa da Karfi gaske, saitin zuciyarta na fat-fat Kamar zata yi tsalle ta fito , ta Soma furta ” inalilahi waina ilaihi raju’un, inalilahi waina ilaihi raju’un” a hankali ta sulale a wajen ta zauna ta rike kai.. tana kallo Essha tana hawaye…

Daki yayi tsit bakiji komai sai sautin kuka mummy da hajiya.. Daddy yagamy rudewa yakasan fahimtar komai dake faruwa,.

Ya kalli daddy karami bakishi na rawa yace” Wai mai ke faruwa ne? Ku gayamin ku barni a duhu. Maiyesameta?

Mummy Dakar ta ‘ iya bude baki tace” Abba Essha, Essha was raped, fyade aka mata ” ta sake fashewa da kuka…

Daddy kansa ya dafa, ji yake kamar zai balle daga madaukarsa, bugun zuciyarsa ya tsanata wajan bugawa.. ya nufi hajiya da kanta na kasa sai shesheka takeyi yace” hajiya ki gayamin zance na Dana keji karya ne, ki gayamin gaskiya “

Hajiya na kuka ta kwashe duk abunda ya faru tundaga farko haduwarsu da kungiya har zuwa su asibiti …
Daddy da mummy su matukar firgita daji wanan labari … Haweye ke sauka a idon daddy kamar an balle famfo yace” inalilahi waina ilaihi raju’un Allahum arjini fi musibati*2….

Tunda hajiya ke bada labari anty zainab ke haweye take haweye, Bata taba jin labari iri haka Mai firgirtawa da abun al’ajabi ya taba faruwa ba ko da a film ne ko littafi ….

Daddy ya rike saitin zuciyarshi Yana girgiza Kai yace ” Essha Dina ne aka aurar da ita, ga yaro da ba’asanshiba , ba’asan asalinsa ba, Allah Mai iko ya share haweye ” alhamdullila tun da har aka daura aure, ba fasikaci suka aikata ba, haka ma yazo da sauki, aure alkhari ne, toh maiyasa kuka bar shi a can baku daukoshi ba?

Daddy karami yace” mun rikece ne da gani hali da Essha take ciki, shiyasa na Manta da batun yaro” dai dai lokaci Doctor Abbas ya shigo daki ya tardasu fuskokisu cike yake da haweye…ya Mika ma daddy Essha hannu sukayi musabaha..

Doctor Abbas yace” kuyi hakuri zata farka, firgice da tsoro ne ya hadasa mata Suma,ya kalli daddy” inason gani ka a office na..

Daddy yakasa magana ya bin baya Doctor Abbas zuwa office nashi , baya su zauna .. Dr .Abbas ya kalli daddy ynda ya shiga damuwa, ya kadan kai” Yaya ku ka Bari haka ya faru da ita? Dr. Abbas ya Mike a fusace yanuna daddy da yatsa yace” ga abunda na ke fadama kenan akullum inmu hadu, kadaina sake ma yaraka da yawa, kullum Kai burika ka, ka farata musu ne baka tsawata musu ba, baya kuma kasa hali yaran zamani na, Wana ya’isa ya zama ishara a gareka, yawa bama yaraka freedom shi ya janyo aka ma Essha fyade . A matsayi na na makwabcika nake gayama gaskiya ” Daddy ya bude baki sheke Yana kallosa har yagama magana , mamaki zance sa ya hanashi bashi amsa.. bai San asali magana shine har ya ke hukuci yake Daura minshi laifi.. toh Wai ma shin maiye aibu wanan duk ka sake ma yaraka, wanan ai sunnah ne na Ma’aiki (S.A.W.) ka riga farata ma iyalaka, ka Dora musu da tarbiya nagari, takura, matsi ko iyaye suriga hade ma yarasu gira shine zai sa yaro ya natsu no yawaici ma shine ke cefa yara ciki wani hali( kaluballe agaremu iyaye).

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button