DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tycoon ya sauke nannauyar ajiya zuciya yace” na Amince maka, ama da sharadin…
Ya zabura yace” daddy shara din daka gindayamin zanbi “
Tycoon yace” akodayaushe in zaka fita, zaka Riga fita da masu tsaro lafiya, sama da ashiri, ka Amince?
Ya sukunyar da Kai kasa gsky baiji dadi wanan sharadin ba, ama ya zainyi, dole zai Amince sbd ya nemi sanyi idanuwanshi, yadaga Kai yace” na Amince dad”
Tycoon yasake cewa” kuma duk abunda ummi zata daura ka akai, Kar kamata musu” Aliyu ya kalli mami yasake kallo daddy shi, fuska shi da alamu tambaya ama sai Bazar dun haushi ummi yake ji, ita tafara Kira Essha da aljana..
Murya ciki sanyi yace” na Amince”
Tycoon yace” yawwa good boy, yanzu Bara na Kira Hafiz su zo su taimaka ma , kayi wanka ka Rama salloli dake kanka “
Yace” zaniya daddy”
Mami tace” a’a boy Karka yi musu, jiki ja ba karfi..
Baya Akira Hafiz, ya taimaka mishi yashiga dashi toilet din ya fito yaja mishi kofa, Baya Hafiz ya fita, ta Dade a tsaye, Essha yake tunawa da iri hali daya barta a ciki, waensu zirori haweye masu zafi suka zubo mishi , ya sa hannu a gashi kanshi ya cakudasu, ji yake kamar yasa ihu ko zaiji sauki yanda zuciyashi ke mishi, ya kunna shower ya Soma wanka, yana gama yayi na tsarki ya dora alwala yafito , Yana dafa bango da sauri ya taimakamishi , yasa jalabiya, Mami ta shimfidar mishi daddurma, ya hau ya tada sallah, duka ya Rama salloli daake binshi, bayan ya idar yadade a zaune ya na roko Allah ya bayyana mishi matarshi, Yana haweye…
Mami ta dagashi tace” boy ya’isa hka, hakuri zakayi, tashi kasa wani abun a cikika, kasha magani, kaji?
” Mami bazaniya ba ” ya girgiza Kai
” A’a boy zaka’iya, daddy shi kasa baki mana”
Tycoon yayi ajiya zuciya yazo ya dafashi yace” haba gadagaa na, nasaka fa da jarumta da juriya, maiyasa bazakayi hakuriba, uhm aliyu, yihakuri please ko kadan ne kaci kaji boy, sai kasha magani… ya dauki fruit salad dake hannu Mami ya deba ya kaimishi baki .. Aliyu ya girgiza Kai Yana yamutsa fuska yasa hannu ya janye spoon din fruit suka zuba yace” daddy kayi hakuri bazaiya ci komai ba, daddy zuciya na zugi takemin.. ya rike saitin zuciyarshi yacigaba”daddy inhar basa Essha idona ba, tona tabbatar muku bazantaba rayuwa ciki walwala ba, daddy rashita zai sa nasha wuya, nazama kullum aciki kunci”
Haydar ya tareshi yace” haba buddy yakake magana iri wana, so kake ka jefa su daddy da ka ka ciki tashi hankali, Essha Essha Essha bamusantaba, wani halaka bai taba hadaka da maisuna ba, tabbas sai yanzu na gasgata magana ummi, Essha Dina aljana ce ta aureka, ta shanye ma zuciya… Ya dafashi yace” look at me, Aliyu yakamata ka farka, mu yaketa, da adduo’i, addu’a makami mummini, kaga mata kala kala ma su kyau, aji dukiya , su so ka ka kisu, shine daga jiya zuwa yau zaka fada so haba buddy impossible……….
Comment &share❤️❤️????????????????????????????????
????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️
DOCTOR ESSHA
????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️????⚕️
WRITING BY
J Hajara
???? MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION ????????️
Kungiya d’aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilmi, Burin kungiyar a ko da yaushe shine ta fad’akar ta kuma Nishad’antar da masoya ta.????????
https://www.facebook.com/107980946102? referrer=whatsa
3️⃣7️⃣&3️⃣8️⃣
Aliyu ya sauke hannu haydar daga dafashi da yayi yace” haydar, Essha ba aljana bace mutum ce kamar kowa. Tabbas da basan so ba, na kasa yarda da wata kalama Wai ita so tsakani ya mace da namiji, in aka cire na iyaye, duk Mai soyaya Ina daukar shine kamar Mara aiki yi, gashi yanzu na fada tarko so. Wlh aka Essha zan iya sadaukar da komai nawa inhar zan ganta” ya rufe fuskashi da taffuka hannuwashi Yana kuka yace” basan a wani hali take ciki ba, tana matukar bukatar a tare da ita, Wai Maiyasa ma ku dauko ni ba tare da ita ba why? Yadaka tsawa ya Mike ya na buga kanshi a bango, da sauri haydar da Suleiman suka rikeshi duk yabasu tausayi. Ya kwace kanshi daga rukosu ya zo gaban tycoon Yana tangadi, tycoon da saurishi ya tallafoshi ya rugumeshi Yana rarrashi shi. Ya kalli mami da duk fuskata ya baci da hawaye, Abu mamaki ya ke Bata, Wai yau Aliyu ne ke kuka, kuka ma aka mace. Taji murya Aliyu nacewa” Daddy maiyasa kuka barta acan, why why ?
” Aliyu kuka ya’isa haka, tun jiya da safe ake ta nemanka lungu da sako ama ba inda bamu duba ba, karshe a gefe gate din gidasu ummi muga, bamusan waye ya ajekaba” Tycoon ya fada Yana share mishi hawaye.
Mami ta share hawaye tace” sai yanzu na Kara yarda da maganar ummi gaskiya ne, aljannace ta shafi boy”
Aliyu ya rike Kai da Karfi kamar zai cire Yana girgizawa yace” no Mami Essha mutum ce, ba aljana bace, Mami kubar kirata da aljana.. ya rike hannu daddyshi yace” daddy Kar yardadani, da Allah ka taimakeni wlh zuciya ta zata iya feshewa”
Tycoon yace” Aliyu take it easy mana, be strong, in har kanaci abinci, kana Sha maguguna ka, har ka warke toh zamu nementa Kar kadamu”
“No daddy baza taba warkewa daga ciwo danakeji a zuciya ta ba inhar bagantaba” Aliyu ya fada kamar zai zauce.
” Hmmmmm” Mami ta ja dogo numfashi… Tace” Hafiz, haydar ku tatara mubar asibiti na mukoma gida Naga kamar Kara rudewa yakeyi”
“Toh mami” suka amsa..
Fawaz ya ya Hado mishi maguguna aka Kira babba likita suka bashi sallama, Aciki motar ya ki kulla kowa titi kawai yakebin da kallo, harsuka isa gida, suna isa parking lot , kafi angama parking yasa hannu ya bude motar ya fito, ya wuce side nashi Yana tangadi, fawaz da Suleiman da gudu suka bi bayashi, suka taimaka mishi ya karasa ciki.
Suna bude kofar parlour sukaci karo da manya manya malamai su takwas ga Al’qurani a gebasu, su zagaye parlour suna karatu, ummi da Ammi suna zaune akan couch gabasu kasko ne ga Kaya hayaki lodi Lodi a gabasu, Aliyu ya binsu da kallo al’ajabi, sukayi sallama, suka amsa.
Ummi tace” yawwa malamai ku dagata gashi ma ya dawo, Suleiman ku kawoshi tana ya zauna a tsakiyar su”
Aliyu ya Bata fuska Yana hararata yace” Ammi ki gayamata ba’abunda zanyi”
Tycoon da Mami da shigowar su kenan yace” kamata sharadin da mukayi da Kai a asibiti ko?
Yace” Daddy wlh mutum ce, ku fahimce ni”
” Ssshh bansaji komai kayi yadan tace, je ka zauna”
Ya nufosu jiki a sanyaye ya zauna a tsakiyar malamai.
Fawaz ya kalli Ammi yace” Ammi abanshi wani, Abu yasa acikishi yasha magani Naga kamar za’a jima”
Ummi tace” eh ku kawomishi abinci yaci yasha magani kafi a fara”
Ya Galla mata harara yace” ni na koshi banzaiya ci komai ba”
Ammi tace” baka isa ba, Hafiz jeka kawo magani, ni baza naje na hadomai wani abun da zai ci”
Yace” Ammi ni na koshi banzaiya ci komai ba”
Ta harareshi tace” mun shiru, banasan nakara ji murya ka ana, abinci sai ka ci shi, sana afara” tayi hanya kitchen dake side din, sharp sharp ta hada mishi pototo with kidney sauce, da coffee, tasa mutumishi ne. Ta fito ta jera a dinning table, takira su fawaz, zu zo suyi breakfast tasan tun jiya rabuwasu da abinci ga idanusu yanuna, baya su zauna tayi serving nasu, ta debo na Aliyu ta dire mishi agabashi ya kauda fuska, ta tsuguna agabashi tace” Aliyu Allah ka ci abinci na, ko na sabba ma”
Ya marairace murya yace” Allah Ammi bazan iya ci komai ba”