DUKKAN TSANANI 8

????????????????????????
*DUKKAN TSANANI*
????????????????????????
*Na*
*Jeeddah Tijjani*
*Adam*
*(Jeeddahtulkhair)*
*8*
A bakin tebur ɗin mai shayin da ke saitin gidanmu ya tsaya yana hangena, kallo mai cike da soyayya da tausayawa yake min idanunsa sun yi jawur kamar zai fashe da kuka, sai da ya gama kallona tsaf sannan ya juya cikin tsananin ɓacin rai da damuwa.
Bai wuce gida ba saboda zafin da yake ji a ransa kai tsaye wajen abokinsa Kabir ya wuce, a Kofar gida ya same shi yana yana karkade machine dinsa da alama shirin tafiya wani wajen yake yi, yana ganinsa ya saki fuska “mutumina yau kuma kaine a dai-dai wannan lokacin, ai kuwa kaxo a dai-dai sai kayi min rakiya wajen madam don yau zuwa na musamman zan yi mata” shirun da yaga Izuddeen yayi masa ne ya tabbatar masa da ba lafiya ce ta kawo shi ba yanayinsa ya canja lokaci daya idonsa ya faɗa gashi yayi ja. Matsawa yayi kusa da shi yana tambayarsa “lafiya kuwa mutumina na ganka a haka, Allah yasa dai ba mutuniyar ce ta haɗa maka xafi ba” ya karasa magana yana dariya tunda dama Kabir gwanin zaulaya ne sun saba tsokanarka juna ya tsokane shi, shima ya tsokane shi haka suke yi.
Shiru yayi ya kasa magana saboda abinda ya cika masa zuciya.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Ganin yadda yake ne yasa yayi saurin gane ba lafiya ba saboda babu yadda za a yi ya tsokani Izuddeen ba tare da ya rama ba, amma yau sai bin sa kawai yake yi da ido.
Zaunar da shi yayi “me yake damunka Izuddeen ni fa ban saba ganinka a irin wannan yanayin ba faɗa min damuwarka mana”
Wani daci yaji ya taso masa daga kasan makoshinsa a hankali ya hadiye miyan takaici, a gintse ya amsa da “ina cikin tashin hankali Kabir mu shiga daga ciki na faɗa maka”
Tashi suka yi suka shiga soro wanda a nan dakin Kabir yake.
Furzar da numfashi yayi mai cike da takaici “ka san yarinyar da nake baka labarin na haɗu da ita kwanaki?” Cikin kulawa Kabir ya amsa masa da “Eh”
Shiru yayi na wasu yan mintuna sannan ya cigaba da magana.
“Tun kafin na furta ina sonta nake ganinta a hanyar xuwanta makaranta, na yaba da hankali da nutsuwar yarinyar wannan dalilin yasa nake matukar sonta har na fara zuwa wajenta hira mun fara fahimtar juna, sai kuma babanta ya bijiro min da wasu abubuwa wanda na kasa gane inda ya dosa, yanzu ma kokarin da yake yi shi ne neman ya raba ni da ita, yanzu haka ma wajenta naje shi ne yayi min korar kare, ban sani ba ko bai shirya aurar da ita bane nayi masa katsalandan”
Cikin nuna damuwa da halin da abokinsa yake ciki ya fara magana.
“Subhanallahi to me yake nufi, Ni dai nasan gaba da baya ba kada wani abin kunya ko makusa abokina, kuma dai-dai gwargwado kana da rufin asirin da xaka iya riƙe yarinyar, sannan iyayenmu mutanen kirki ne ba su da wata matsala, ka cancanci a soka na san duk wani uban da kaje neman auren yarsa xai yi alfahari da hakan, amma bamu sani ba ko kuma miji yayi mata shi yasa ya dakatar da kai”
Saurin girgiza kai Izuddeen yayi, “gaskiya bana zaton an yi mata miji don tun farkon haduwa ta da ita bata faɗa min cewa akwai wata magana a kanta ba, nafi tsammanin akwai abinda yarinyar take boye min”
“Ok ba mamaki amma shawarar da zan baka, ka fadawa Baba kana sonta a aika a nemar maka izinin zuwa zance, ina ganin wannan rashin aikawar ne ya ɗan baka matsala”
Girgiza masa kai kawai Izuddeen yayi sbd yanxu Maganar ma wahala take masa tunanin yadda za a ce an raba shi da Sa’adatu yake yi, ya san har abada baxai taɓa jurewa ba, Kabir ne yake ta yi masa hira don hankalinsa ya kwanta shi dai jin shi kawai yake amma zuciyar shi da hankalinsa yana wani wajen daban, har gida Kabir ya kai shi a machine sbd baxai iya tafiya da kanshi ba kasancewar baya jin karfin jikinshi.
*************
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Na fi rabin hour a zaune ina zulumi, ni ban shiga gida ba ni kuma ban tashi daga inda nake ba, tunanin inda zan ajiye wayar da ya bani nake yi saboda bana so a kwace masa wayarsa karshe nasan ba nice xan mora ba, a gabana xa a yi wa su A’isha kyautarta ni kuma a bar ni da kunar zuciya. A bayan kaure na ajiyeta da niyyar idan kowa ya shiga daki na dawo na ɗauka.
Tunda na doso kai bakin kofa naji an cika tsakar gida ana ta maganganu da dukkan alamu zuwana ake jira, komawa soro nayi na zauna a raina nace “sai kun gaji da xama xan shigo dan baxan xo a kusan cinye namana danye ba” komawa nayi na xauna abuna, shirun da suka ji yayi yawa ne yasa Baba xuwa da kansa kirana.
“Kina nufin baxa ki shigo bane Sa’a ko kuma binsa xaki yi ku tafi, ina nan ina jiranki kixo ko kuma ranki ya ɓaci”
Daurewa nayi na miƙe idanuna suna ƙasa na kasa dagowa a hankali nake jan ƙafa har na shiga ciki, idanun kowa ne ya dawo kaina ana yi min wani kallo mai ɗauke da fassarori masu yawa, cikin kakkausar murya Baba ya fara yi min magana.
“Tsugunna nan zan tsaga miki sharudda a gaban yan uwanki saboda ina so su zama shaida ko zuwa gaba” ban yi gardama ba na xauna tare da sunkuyar da kaina ina wasa da yatsun kafata, addu’a na shiga yi Allah ya bani damar daurewa kada makiyana su ga kukana.
“Wannan shi ne maganata ta ƙarshe da ke kada na sake ganin wannan yaron a gidan nan idan ba haka ba kuma zaki haɗu da fushina daga ke har mahaifiyar ki, kin ji abinda na fada miki ko” gyada kaina nayi alamar eh.
Innah salamatu ce ta amsa da “kai kake bata bakinka malam amma ba saurara abinda take yi xata yi ba, sau nawa kasa doka aka karya maka, shawara daya xan baka kaje ka dakatar da yaron nan har gida, ko kuma ka bani dama ni naje da kaina tunda kai naga bori kake yi da sanyin jiki”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Maganar innah ba ƙaramin tokare min xuciyata tayi ba, na san matuƙar taje gidan su Izuddeen Maganar aurenmu ta gama lalacewa har abada, har na gwammace zuwan Baba a kan nata saboda shi idan suka gyara zancen xai iya amincewa da aurenmu.
Cikin gamsuwa da abinda ta faɗa ya jinjina kai
“Kwarai kuwa xuwan naki ma ya fi muhimmanci tunda kin san gidan, kuma ke xaki samu mahaifiyarsa kai tsaye ki fada mata kudurinsa na son lalata mana yarmu. Ni kuwa ba lallai ne na samu babansa ba, don haka gobe da safe kije ki fada musu su katange dansu ni ma zan bawa yata kariya duk abinda ya biyo baya kuma kada su zarge ni su zargi kansu”
Farin ciki ne ya bayyana a fuskarta taji dadin hukuncin da aka yanke min, cikin kissa take magana “Amma malam ina ganin har da rashin abincin nan da ba a bata, shi ne yasa take so ta jefa kanta a rayuwar da ba tata ba, ina roko a dawo musu da kwanon su ita da borar uwarta ko sa ji sassauci, idan aka tsare mata cikinta za a toshe wata kafar barnar tunda dama da yunwa ake fakewa ake wata lalatar”
Shiru yayi na dan lokaci sannan yayi magana “to shikenan tunda kin amince ki cigaba da basu amma ki tabbatar sai kowa ya koshi”
Amsa masa tayi da “To” har ya juya xai tafi ta kira shi.
“Au malam baka ji ba” da rawar jiki ya dawo “Da akwai abinda kika manta ne baki fada ba?”
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Cike da makirci tace “Maganar bawan Allahn nan ya kamata a taso da ita tunda da kanka kaje ka same shi ka faɗa masa damuwarka, kuma ya yarda ya amince, amma kuma har yanzu baka sake cewa komai ba kamar wanda aka daurewa baki, kaga wannan ma wata hanya ce da xata sa a toshe kafar barna tunda dai ta nuna aure take so, kuma hakkinka ne dama ka aurar da ita don haka tunda akwai miji a kasa me ake jira sai magana kawai”
Sauke ajiyar zuciya yayi “ina sane da wannan maganar akwai abinda nake jira ne shi yasa kika ji nayi shiru amma ba mantawa nayi ba”
Juyowa yayi kaina “Au dama tun daxu kina nan munafuka, kin sa mutane a gaba kina zare mana ido wato duk maganar da za a yi sai kin ji ko, tashi maza ki bace min da gani kafin na karya munafukar kafar taki”
Tashi nayi na shiga daki a xaune na tarar da innah tana karanta littafin addu’o’i babu wani alamar damuwa a tare da ita, duk da cewa na san duk abinda aka taji tattauna a kunnenta, sannan ta san da dukkan abinda ake kulla min, gefenta na samu na zauna nima ƙoƙarin kin nuna mata damuwata nayi, sai da naga alamar ba tada niyyar ce min komai sannan nayi magana.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
“Innah wai duk abin nan da ya faru baki ji bane naga kina ta karatu kamar baki san anyi wani abu ba, naga ma kamar baki damu ba”.
Fuskarta mai cike da kamala ta dago “to me zan ce Sa’adatu, wanda yake da Allah me xai dame shi, ina ganin addu’a ce kawai maganin abinda yake faruwa a gidan nan, ni da Allah na dogara kuma nasan xai isar min, duk abinda suke yi na barsu da Allah idan ba yau akwai gobe, kema abin ya daina damunki idan mijinki ne duk makircin da zasu shirya sai ya rushe kin aure shi, shi yasa abin nasu ma ya daina damuna”
Tawakkali da nutsuwar innata da yadda take samun nutsuwa a duk lokacin da masifa ta same ta ba ƙaramin karfafa min gwiwa yake yi ba, wannan Dalilin ya sanya na daina saka kaina a damuwa, kallon duk abinda suke mana nake yi a matsayin film wata rana dole zai kare.
Ban sake yin magana ba sai da naga ta idar da addu’ar da take yi saboda bana so na katse mata abinda take yi, cike da ladabi nace “innah waya fa ya bani shi ne abinda ya janyo wannan kace nace din, wai Baba da kansa yake cewa lalatani yayi sannan ya bani” Ban san lokacin da na fashe da kuka ba, rarrashina innah take yi
“Duk naji abinda suke faɗa Allah ya fi mu sanin halinmu, kuma zai mana hisabi a kan abinda suke fada shi yasa ban fito na kare ki ba, saboda nasan ko na faɗa a banxa ba yarda xasu yi ba, cewa zasu yi ni na yarda kiyi, don haka ki kyale su Allah baya bacci, yanzu ina wayar”
Cikin kukan na amsa mata da tana bayan kyauren soro.
Da sauri ta dube ni, “kika ajiye masa waya a soro salon a je a sace, yi maza kije ki dakko” tashi nayi na tafi naje na bude bayan kyauren abin mamaki banga waya ba, hankalina ne ya tashi na rika duba lungu da sako amma babu waya babu dalilinta.
Da gudu na shigo gida na karbi touch light na haska ko idona ne bai ga dai-dai ba nan ma dai shiru babu waya, da kuka naxo nake sanarwa innah ban ga waya ba.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({}); Ita ma hankalinta ne ya tashi sosai saboda kada mu je Izuddeen yace bai san xance ba sai mun biya shi waya, ga shi ba wani na bawa ajiya ba ballantana na tunkare shi nace ya bani.
Mun fi 2hours muna neman waya ba labarinta, mu ba abin mu yiwa jama’ar gida cigiya ba mu janyowa kanmu gori.
Bayan Asubah ma sai da na sake dubawa ban ganta ba, kuka sosai na riƙa yi ina addu’ar Allah ya bayyana wanda ya sace ta, innah ma taya ni ta riƙa yi.
Ina godiya gare ku mutanena na DUKKAN TSANANI FANS Ina godiya da comment dinku kuma kuna karfafa min gwiwa.
Kada a manta da sharing
*Jeeddahtulkhair????*