DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVEL

Tace” nagode sir”

Ya amsa da Don’t mention sanan yace” zo muje na kaiki inda Zaki zauna, sauri nake anjima zan wuce Nigeria”

Tace” okay sir”

Yafara tafiya tana biye dashi janye da manya manya trolley nata, har suka isa gaba motar ya taimaka mata suka sa Kaya a boat, suka shiga ya tada motar, suna tafiya , Essha ta har da sauke glass din motar tana bin Delhi da kallo, sai hayaniya kakeji, city ya burgeta, there busy roads , yanayi shigarsu ya burgeta ta saki murmushi.. Dr ra’uf na kallota shima yayi murmushi yace” The you like the city? Bata waiga ba tana kallo wani babba temple na bauta ta kada Kai..

Shima ya fara mata nasiha dun yadda zata tafiyar da rayuwata..yace” Essha kiriga sai hakaliki a karatu , Kuma kisan condition daki ciki, you are pregnant you have to be careful”

Essha ta sukunyar da Kai kasa nandana mood Nata ya canza, zatayi kuka a ranta tace” shikena daddy ya sanar dashi Ina da ciki”

Dr ra’uf yakalleta yayi murmushi yace” Essha Kar Wanan yadameki, daddy ki ya sanar Dani komai, you don’t have to be worried (kamar yasan abunda take ayanawa a zuciya kena).. Kuma albirshiki na Miki kawa, a gida daya ma zaku zauna, ba time yanzu muna zuwa Zaki ganta , itama student ne, school naku ma daya har course dima, itama this year ta fara, zata nuna Miki komai na school kijiko?

Ta gyada Kai, Allah sarki harta tuna da bestie, haweye zai sauko da sauri ta share, taji Dr ra’uf nacewa” sauko mun iso”
A hankali ta sauka tana bin street din da kallo, quiet area ba wani hayaniya sosai, gefe guda kuwa fili cricket ne yara ke bugawa, sai bin street din take da kallo haryanzu Bata daina mamaki ba, yau itace a India, a hankali ta furta” Alhamdullila, thanks dad”
Taji Dr ra’uf ya ja mata kumatu Yana dariya yace” hey Yar kauye, shiga ciki nariga da na shiga Miki da Kaya, Pooja zata nuna Miki room naki” ya nuni ga wani flat maidaidaici yace” shiga na ne gida naku, school naku bai da nisa Dana, ni zan wuce sai anjima”
Ta daga mishi hannu tace” nagode uncle”

Yace” you re welcome, shiga ciki, Pooja nanan” ya tada motar ya yi gaba..

Essha a hankali take nanata suna Pooja, ta Kama hanya ta shiga da sallamarta, ba amsaba sai bin gida take da kallo, 2 bedroom flat ne, da babba parlor, kitchen da dinning area, gefe guda Kuma study room ne, gabadaya bedrooms din da furnitures iri na student Dan dai dai, parlor ma yasha Ash sofa, sai da table a tsakiyar Mai kyau, babu abunda babu a gida.

Ta nemi guri ta zauna tana share kwalla, tana daga Kai, tayi ido biyu da wata kyakyawa budurwa, da mamaki ta bude baki tana kallota don yariya Kama take da Alia Bhatt, babacisu kawai tafi Alia Bhatt girma jikine, ta fito daure da towel tana busar da gashi kanta da hand drying, tana gani Essha ta saki murmushi tazo ta rugume ta, ta Mike taba Essha hannu suyi musabaha, Essha kam takasa mgn sai binta take da kallo mamaki,

ta shaking hannu Essha tace” Namaste! Essha Ahmad right? Welcome to India, am your new friend, course mate, my name is Pooja Chandra am from pune, nice to meet you too”

Essha ta saki murmushi tace” nice to meet you too”

Pooja tafara zuba da turaci Tace” ni Yar Hindi ce, ke Kuma musulma ko? ai zamuriga zama tare ba matsala ko? Ki na da kyau sosai, Mr Ra’uf ya bani labariki, ki na da aure, Nima nakusa aure,Nanda wata biyu, mijina da zan aura a Dubai yake aiki, sunashi saif Khan shima musulmi ne, ai zakizo ko? Kiga kena ki zama babba kawana, tundama a kauye mu ba Wanda yakeso yayi kawa Dani saboda nayi kiba da yawa, kina so na a haka ko? Ta fada ta marairace ma Essha fuska…

Essha batasan lokaci dariya ya kubce mata ta Soma kyakatawa, gsky Pooja ta shiga ranta, sanda ta natsu tabar dariya sanan ta gyada mata Kai Tana murmushi tace” ta Amince”

Pooja ta rugume ta, tana murna ta mikar da ita ta Soma zangaya da ita gida tana ta zuba tana Bata labari school, har waje ta kaita ta nuna nata gida su landlord nasu, Essha duk ta gaji, Pooja ta Bata hakuri, ta nuna nata dakita, Essha na shiga baya Pooja ta wuce ta fada gado ta fashe da kuka, ita kanta ta rasa dalili kuka, sanda tayi Mai isarta tukun ta Mike ta share hawaye ta fada bathroom tayi wanka, Tana Gama ta daura alwala ta fito tayi sallah, Tana idarwa ta fara jera kayata a ciki wardrobe, Pooja ta shigo ta taimaka mata suka jera foodstuffs a kitchen tana gamawa ta fito da dambu kaza da mummy ta hada mata taci sosai ta bin da ruwa ta kwanta da kewa gida…

Monday

Tare suke tafiya school da pooja, su tashi Tare, tana fahimta karatun sosai… Tun safe in suka fitai lecture sai 7 wani lokaci har 9 suna kaiwa, su dawo duk a gajiya..a kullum sai tayi waya dasu daddy ta, harda su hajiya suna kirata su gaisa..

Baya three months

Essha ciki ta ya girma har ya Soma fitowa, tana samu kulawa sosai guri Pooja da mummy, Dan ko wani karshe wata mummy take zuwa dubata, su Saba sosai da Pooja, da Pooja Bata da matsala, inkagasu kamar amine juna da sukayi shekaru a tare,a bangare karatun kuwa, karatun take sosai ba Kama hannu yaro, ta mayar da hankali ta sosai ba wasa, har ayi biki Pooja two months dasuka wuce, suyi shagali biki sosai, baya biki miji ya dauketa sukaje honeymoon a Dubai, Essha tayi kewata sosai, sati daya Pooja ta yi ta dawo saboda school, ta koma gida mijita , tayi da Essha ta dawo, Essha taki amincewa, haka ta hakura itama ta park ta sake dawowa gidanasu suka cigaba da zama…

Duk abunda Essha ke bukatar Pooja ne kayi mata,ta hanata to komai sai dai taci ta sh tayi karatun, gashi tana samu kulawa sosai guri mummy da Daddy ta.
tun Pooja baiya girki naija ba har ta kwaya ta kwairai sanadiyar Essha, baza ta iya cewa ma Pooja komaiba dun ta mata abubuwa da ko yanuwata barasa su mata ba, shiyasa a kullum take kara shiga ranta..

Ciki na 6months sukaje scanning, scanning ya nuna namiji zata Haifa, Pooja tagaya ma mummy, su ka fara sayayar Kaya haihuwa, kafi wani lokaci suga ma sayayar komai…

Baya wata tara da Yan kwanaki, Da safe, Essha na zaune , tana tsifa, takkadu ne birjik a gabata, mummy na gefe ta, tana bare ma ta gayda , Pooja na ka gado tana barci, Essha sai mutsu mutsu takeyi ta kasa sukuni, mummy ta kalleta tace” yadai ?

Ta yatsine fuska tace” bakomai mummy”

Mummy ta Mika ma ta gayda ta amsa zata Kai baki taji kamar wani Abu ya tsarga mata mara, ta dakata da sauri, a hankali ciwo ta takeji ya fara tsanata, Essha ta kasa Koda motsi sai cije lebe take, can azaba ya ya tsanata tafara murkusawa, Nan ta fashe da wani kuka Mai Kara, mummy da hankali ta baya kanta tanaji kukata da daga Kai da sauri ta Mike Tace” Essha lafiya?

Tana kuka Tace” Wayoo mummy zan mutu marana”

Mummy tace” subhanallahi” na ta fara Kira suna Pooja.. Pooja na barci ji yanda mummy ke kira sunata tasan ba lafiya ta farka a zabure ta diro daga gado gani Essha a durkushe yasa ta karasawa gareta da sauri, daga ita har mummy dukasu a rude suke, Dan Essha ta Soma fita daga hayacita, azaba takeji sosai, gashi kanta duk ya mutse , duk ta jike gabadaya.

Pooja da sauri ta shiga bedroom nata ta zari car key da mijita ya Bata gift a lkc bikisu, ta koma daki da gudu, tana zuwa da turanci tayi magana tace” mummy dagata mukaita asibiti”
Mummy ta dagata a rike suka fito da’ita, Pooja tayi sauri ta bude back sit ta aka Kwantar da Essha, mummy ta zauna a baya ta Dora kan Essha a ciyarta tana shafa Kai Tana tofa mata duk addu’a da yazo bakita.. Pooja ta figi motar sai asibiti …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button