DOCTOR ESSHA COMPLETE HAUSA NOVEL
Mummy kam kala batace ba tayi gaba abinta.
Hajiya tace” kuzo munshiga ciki, matar Yayaki na na zuwa su gaida ki”
“Allah sarki hajiya da so kuwa nagasu kisan ayi biki ba na Nan” cewar Essha
Aina’u tace” Kar kidamu Zaki gansu har ki gaji”
Suka shiga ciki sashe Daddy, Hajiya sai matsifa take” Sadik yazo bai huta ba shaidanu yara harsu shiga dashi gari”
Essha tayi kewa sosai yau ganta ciki family ana hira sai taji sanyi a ranta, Delicious food kala kala aka tanadar mata kowa a guri nasan ta ci nashi tazama Yar lele, Big mum ta Kira sukasha hira sosai, suna Gama waya da big mum ta Kira Pooja, abun tausayi Arundh haryanzu kuka take, karshe ma Pooja kashe waya tayi hira da ba’ayi kenan ba.
Wurare la’asar duk kowa ya watse, masu aure kowa yayi hanya gida mijishi, aka barta dasu mummy dasu amir, sai a lokaci ma ta lura da canzawa mummy, gashi ta damu na Rashi dawowarsu khairat, tunda suka fita Basu dawo ba har ana neman magrib, hajiya dakata ta kirasu su dawo, sai da Isha suka shigo, su Sha fada sosai kuwa aguri Hajiya.
Amir dakashi ya bashi abinci, yamishi wanka ya shiryashi suka wuce masalaci. Har lokaci mummy Bata saki fuskar ba.
Essha na idar da sallah Isha ta shigo daki mummy da sallamata, ta samaita a daddurma tana ja carbi mummy ta amsa sallama, Essha ta karaso shigowar ta zauna a gefe mummy, mummy ta shafa Addu’a ta kalli Essha fuska, Essha ta gaida ta, ta amsa ba yadda ta saba amsa gaisuwarta ba, Essha Bata ji dadi haka ba murya a hankali tace” mummy ko dai laifi na Miki ne Naga tunda munka shigo ki ka canza?
Mummy ta kalleta shiru Bata Bata amsa tambaya ta ba can Tace” ina da magana dake ama ba yau ba sai gobe inda ki ka huta”
Essha taji gabanta ya fadi tace” mummy dafata dai lafiya ko?
Mummy zatai magana, sukaji an bude kofa an shigo da sallama duk suka amsa, Sadik ne Yana sanye da jalabiya fari fat, yamishi kyau, ya shigo da murmushi shi as usual hannu shi rike da iPad da packet din Laddu( alewa ne na kasa India)
ya nufi mummy yace” Granny I bought this for you, open your mouth, it’s sweet it won’t hurt your tooth”
Mummy batayi niyya murmushi ba sanda tayi taji tana matsifa son yaro.
Sadik ya bude baki yace” Granny Haaa?
Ya dauki laddu daya yakai saiti bakita, Mummy ta bude baki a hankali yasa mata, tana taunawa Tace
” Wai waga abun zaki shi yayi yawa ama akwai dadi” tanayi ta na lumshe Ido..
Sadik bai daiji abunda ta fada ba gani yadda takeyi da fuskar ne yabashi dariya.. Essha ta Mike jiki a sanyaye zata fita mummy ta dakatar da’ita
“Ki kaishi guri Daddy ku karami tun safe yake yake tambaya shi, yanaso ganishi”
Murya a sanyaye tace” toh mummy, Sadik let’s go”
Sadik ya make kafada wai shi da mummy zai kwana, sanda tayi dagaske sanan ya binta, ya na daga ma mummy hannu, suna fita Mummy ta zuba tagumi ta rasa gane kan almari..
Essha na fita sukaci karo dasu Amir, Sadik ya musu murmushi ya Mika musu packet din Laddu sanan yace” good night uncle Amir, good night uncle Walid”
Duk suka shafai Mai kai, Amir yace” sis tare fa zamu kwanta ina Kuma za ki kaishi?
Tace” Mummy ne tace na kaishi guri Daddy k yanason ganishi”
Walid dayacika baki da laddu yace” sis yanaga yanayi ki yan canza lafiya daiko?
Ta gyada Kai ta Kama hannu Sadik sukayi sashe Daddy k, suna zuwa da Sallama suka shiga, Daddy k baiyi bacci ba idoshi biyu ya Kuna NTA news @10 Sadik da gudu yaje ya haye cinyarshi, Daddy k yayi murmushi yace” wash aboki zaka karyani, sai yanzu iyaye naka suka dama mun gaisa ko?
Essha tayi murmushi tace” ai daddy aguri ka ma zai kwana, ni na wuce sai da safeku”
“Toh Likita Allah yatashemu yamiki Albarka”
Ta amsa”Amin daddy”
ta wuce side nasu ta Tara dasu Amir zaune su Kuna Tasha sport suna kallo tace” bros sai da safe ku”
Walid yace” sis wait da Allah?
Ta tsaya tace”yadai ?
Yace” Gobe in Allah yakaimu zamu fita da boy”
Amir ya Mike yace” yes sis mantawa nayi, bagayamiki ba, gobe zamu fita yawo dashi kinsa Sunday free time ne Monday zamu koma school, please grant us that permission mufita da boy kinji?
Tayi dariya tace”Amir Sadik fa Dankune, ai basai ku tambayi izini naba, Allah yakaimu gobe, ina da ina zakuje?
Walid yace” thanks sis, ShopRite kawai zamuje, movie munkeso kallo a cinema din guri da za’a fara 2pm, toh zamuje 9am Boy yasamu fun kafi time din yacika”
Yana Kira ShopRite Essha taji gabanta ya fadi, sai taji batason tafiya, bayanda taiya tace” okay Allah yakaimu sai da safe ku”
Suka amsa da bye sis mungode..
Walid yayi ihu murna yace” ye bro we will rock with your new car”
Amir yayi murmushi yace” bakada matsala yaro in aka wanane”
Essha na koma daki ta kwanta Sam Bata iya runtswa ba sai juye juye kawai take, Bata ki ace gari ya waye ba taji mak mummy zata gayamata, magana aiki da zata fara zuwa gobe ma bai damaita ba cus she knows her work tafi damuwa taji abunda Mummy zata fada mata.
Karshe toilet ta fada ta Dora alwala ta fito ta Soma nafila tana roko Allah ubangiji ta ya kawo mata sauki a alamurata, har Asuba tana idar da sallah subhi ta Kara gyara kwanciya bacci barawo ya saceta.
Tana ciki bacci ne taji ana tashita”mum wake up its nine”
Ta bude Ido a hankali, Sadik tagani a gefeta ya Sha wanka ya hade, jikishi sanye yake da white t-shirt da red jeans trouser,kana yasha gyara, kafarshi sanye yake da wata hadadiyar sneakers red mai, gefe takalmi a zangaya shi da white line, hannushi rike da p-cap red, gaba aljihu rigashi kuwa puzzle game ne.
Essha tayi murmushi tace” you guys are ready ko?
Ya daga mata Kai, ta Mike ta jawoshi gefeta tace” now say Mum’s rules let me hear”
Yayi murmushi yace” rule number 1: Start everything with Bismillah, rule number 2, Don’t talk to strangers, rule number 3, always be obedient, don’t be sturborn”
Tayi murmushi tace”excellent my boy , hi five? Ya Mika mata hannu suka tafa..
Amir yashigo shima ya hade a ciki manya kanya yayi kyau yace” good morning sis?
Ta amsa da kai, yace” mu zamuwuce sai mun dawo, boy common let’s go, sis mummy na kiraki”
Sadik ya sauko ya rike Mai hannu, Essha na kallosu gabanata tsanata faduwa yakeyi tace” Amir da Allah kuladashi kansa Sadik da kirniya”
Yace” sis Kar kidamu he’s safe inshallah”
Itama ta sauko tasa teddy slippers nata ta biyosu, ta cima su khairat na hada table na breakfast, suka gaisheta ta amsa, ta gaida mummy har kasa ta zauna a gefeta, Sadik zasu fita ya dawo da gudu ya Bata peck a goshi yace” bye Granny, bye mum”
Ta daga Mai hannu tana murmushi..
Su Amir suna tada motar suka dauki hanya Abj, Sadik na gefe window sai bin kasamu namu yake da kallo, suyi tafiya awa daya suka isa ShopRite
Suna shiga ciki, Walid ya gyara ma Sadik zama p cap nashi, suka samu table suka zauna, Amir ya musu order su ice creams, drinks da su snacks, suna Sha suna hira hankali kwance..
Gidan Tycoon
Ammi ne zaune, cinyar ta Sofia ne kwance wow su Sofia angirma, sai zuba ma Ammi shagwabe take son ranta, Isa na zaune a kan carpet, Mami na kan dinning ita da Idrees da Rahma suna having breakfast, gefe Rahma Kato teddy ne dayayita hudu Mai kyau.
Ammi sai hararata take cike da matsifa tace” wlh Isa bakaisa ba, Kuma baka kyauta ba, Rahma ne zaka kawo mata tsaraba Teddy, Sofia Kuma hannu rabbana, toh bazai sabu ba, duk yanda zakayi dai ka kakawo mata nata, asamu zama lafiya”